A rana mai kamar yau ne, 6 ga Rabi’ul Auwal shekara ta 11 bayan hijira, kwanaki 5 da bizne gangar jikin fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (S), ‘yarsa, Sayyida Fatima Azzahra (SA) ta fara ziyartarsa a makwancinsa mai albarka.
Manzon Allah (S) ya yi wafati a ranar Litini 28 ga watan Safar ne, Amirulmuminin Imam Ali ‘Dan Abudalib ya yi masa wanka da sutura sannan ya jagoranci janazarsa ya kamala a yammacin Talata, ranar Laraba 1 ga wata da safe ya bizne shi a muhallin da ya cika Allah ya kara masa aminci da tsira.
Sheikh Saduk ya kawo a Amalinsa, shafi 99-101 da Alhamiyuni a cikin Fara’idus Simdain, jildi na 2, shafi 34 da 35, daga Manzon Allah (S) yana wasiya ga Amirulmuminin (AS), yake ce masa: “Ita kuwa ‘Ya ta Fatima, wacce ta kasance itace shugaban matan talikai, a yayin da na ganta sai na tuna da abubuwan da za su faru da ita bayan bana nan. Kamar ina ganinta a yayin da kaskantacce zai kusa cikin dakinta, ya keta alfarmarta, a kwace mata hakkinta, a kuma hanata gadonta, a kassara mata tayin da ke cikinta, a barar da cikinta. A wannan halin za ta kasance tana kira tana cewa; ‘Ya Muhammadaa!’ Amma ba za ta ji amsa ba. Za ta nemi dauki, amma ba za ta samu mai taimako ba. Za ta wanzu a bayana tana cikin bakin ciki da damuwa, kuma mai yawan kuka. Za ta kasance kamar wacce aka kaskantata bayan kuwa a lokacin rayuwar mahaifinta ta kasance mai daukaka.”
Manzon Allah (S) ya ci gaba da cewa: “Za ta kasance farkon wacce za ta sadu da ni a cikin Ahlulbaiti na bayan na tafi. Za ta riske ni a cikin damuwarta kuma tana raunatacciya wacce aka bakantawa rai, wacce akawa kwacen hakkinta, kuma wacce aka kashe ta.”
Sannan sai Manzon Allah (S) yace: “Allah ka la’anci wanda ya zalunceta, kuma ka yiwa wanda ya fusata ta azaba, ka kaskantar da wanda ya kaskantata, kuma ka dauwamar da wanda ya barar da tayin cikinta a wutarKa.” A daidai wannan lokacin sai Mala’iku suka amsa addu’ar Manzon Allah (S) da ‘Ameen’.
Babu wani abu da Manzon Allah (S) ya fada zai faru da wannan diyar tasa mai girma da bai auku ba. Kai sun ma yi gaggawar afkar da shi ne. Kamar suna jira ya cika ne su fara shirin aiwatar da wadannan mugayen nufin nasu. Kamar kuma suna jira ne Imam Ali (AS) ya kammala Janazarsa ya bizne shi a safiyar wannan Larabar, su kuma su dira akan wannan diyar tasa a gidanta a yammacin ranar Larabar!
Wannan diran da suka yi a karkashin wani mutum da ake wa lakabi da ‘Dan Sahhaqu, wanda ya auku a ranar Laraba 1 ga Rabi’ul Auwal, shine dalilin da ya kwantar da Sayyida Zahra (SA) ta fara jinyar raunin da suka mata na bugun kirjinta da karfen bayan kofar dakinta, suka sa ta yi barin dan cikinta, hakan yasa bata iya samun sukunin ta tashi ta tunkari kabarin Mahaifinta ba sai bayan wadannan kwanakin.
Ta je gareshi tana mai zubar da hawaye, tare da rakiyar mijinta Amirulmumin (AS) tana dafe da ‘ya’yanta Hasanain (AS) da Zainabul Kubra (SA), a yayin da baiwarta Fidda ke rike da ita.
Kamar ina jiyo kukan Kakata Sayyida Zahra (SA) a kan kabarin Shugaba (SA) tana rera masa koken irin zaluncin da wadanda ya musu wasiya da su bi ta sukai mata.
Ina tayaku jajen wannan rana ya ku Muminai. Ina hawaye da kuka ga abin da akaiwa Kaka mai girma ga Imamul Asr (AS). Tare da tawassul ga wannan jarabawar tata, akan Allah ya gaggauta hallaka mana Elrufa’I da Buhari da duk mai goyon bayansu ko mai tayasu aikin zaluntarmu a daidai wannan lokacin. Allah ya shudar da su kamar yadda ya shudar da Azzaluman farko!
— Saifullahi M Kabir