December 07, 2016

YAU NE RANAR SHAHADAR LIMAMIN TSIRA NA 11

A rana mai kamar yau, 8 ga watan Rabi'ul Auwal, a shekara ta 260 ne Halifan Manzon Allah (S) na 11, Baban Imam Mahdi, wato Imam Hasan Bin Ali Al'askariy (AS) ya yi Shahada. 


Imam ya yi Shahada ne a kurkukun barikin soji na Banul Abbas, bayan da aka shayar da shi guba Don a ga bayansa a huta, bisa tsoron kar ya haifi Imam Mahdi (AS) wanda hadisai da Dama suka nuna cewa shine mai daukar fansar wadanda aka raunata (Ahlu Muhammad (S), akan azzaluman farko da na karshe. 

Ina mika jaje ga al'umma baki daya, musamman ga Shugaban zamaninmu, Imam Mahdi (AJ) dangane da zagayowar wannan rana ta wafatin Mahaifinsa mai girma. Ta'aziyyar musamman ga Jagora, Sayyid Ibraheem Zakzaky dangane da Wannan rana ta rashin Mahaifin Limamin zamaninmu. 

La'antar Allah akan makasan Iyalan Annabi da Shi'arsu har tashin Alkiyama. 


Saifullahi M Kabir 
8 Rabi'ul Auwal 1438

December 05, 2016

RANAR 6 GA WATAN RABI'UL AUWAL

A rana mai kamar yau ne, 6 ga Rabi’ul Auwal shekara ta 11 bayan hijira, kwanaki 5 da bizne gangar jikin fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (S), ‘yarsa, Sayyida Fatima Azzahra (SA) ta fara ziyartarsa a makwancinsa mai albarka.

Manzon Allah (S) ya yi wafati a ranar Litini 28 ga watan Safar ne, Amirulmuminin Imam Ali ‘Dan Abudalib ya yi masa wanka da sutura sannan ya jagoranci janazarsa ya kamala a yammacin Talata, ranar Laraba 1 ga wata da safe ya bizne shi a muhallin da ya cika Allah ya kara masa aminci da tsira.



Sheikh Saduk ya kawo a Amalinsa, shafi 99-101 da Alhamiyuni a cikin Fara’idus Simdain, jildi na 2, shafi 34 da 35, daga Manzon Allah (S) yana wasiya ga Amirulmuminin (AS), yake ce masa: “Ita kuwa ‘Ya ta Fatima, wacce ta kasance itace shugaban matan talikai, a yayin da na ganta sai na tuna da abubuwan da za su faru da ita bayan bana nan. Kamar ina ganinta a yayin da kaskantacce zai kusa cikin dakinta, ya keta alfarmarta, a kwace mata hakkinta, a kuma hanata gadonta, a kassara mata tayin da ke cikinta, a barar da cikinta. A wannan halin za ta kasance tana kira tana cewa; ‘Ya Muhammadaa!’ Amma ba za ta ji amsa ba. Za ta nemi dauki, amma ba za ta samu mai taimako ba. Za ta wanzu a bayana tana cikin bakin ciki da damuwa, kuma mai yawan kuka. Za ta kasance kamar wacce aka kaskantata bayan kuwa a lokacin rayuwar mahaifinta ta kasance mai daukaka.”

Manzon Allah (S) ya ci gaba da cewa: “Za ta kasance farkon wacce za ta sadu da ni a cikin Ahlulbaiti na bayan na tafi. Za ta riske ni a cikin damuwarta kuma tana raunatacciya wacce aka bakantawa rai, wacce akawa kwacen hakkinta, kuma wacce aka kashe ta.”

Sannan sai Manzon Allah (S) yace: “Allah ka la’anci wanda ya zalunceta, kuma ka yiwa wanda ya fusata ta azaba, ka kaskantar da wanda ya kaskantata, kuma ka dauwamar da wanda ya barar da tayin cikinta a wutarKa.” A daidai wannan lokacin sai Mala’iku suka amsa addu’ar Manzon Allah (S) da ‘Ameen’.

Babu wani abu da Manzon Allah (S) ya fada zai faru da wannan diyar tasa mai girma da bai auku ba. Kai sun ma yi gaggawar afkar da shi ne. Kamar suna jira ya cika ne su fara shirin aiwatar da wadannan mugayen nufin nasu. Kamar kuma suna jira ne Imam Ali (AS) ya kammala Janazarsa ya bizne shi a safiyar wannan Larabar, su kuma su dira akan wannan diyar tasa a gidanta a yammacin ranar Larabar!

Wannan diran da suka yi a karkashin wani mutum da ake wa lakabi da ‘Dan Sahhaqu, wanda ya auku a ranar Laraba 1 ga Rabi’ul Auwal, shine dalilin da ya kwantar da Sayyida Zahra (SA) ta fara jinyar raunin da suka mata na bugun kirjinta da karfen bayan kofar dakinta, suka sa ta yi barin dan cikinta, hakan yasa bata iya samun sukunin ta tashi ta tunkari kabarin Mahaifinta ba sai bayan wadannan kwanakin.

Ta je gareshi tana mai zubar da hawaye, tare da rakiyar mijinta Amirulmumin (AS) tana dafe da ‘ya’yanta Hasanain (AS) da Zainabul Kubra (SA), a yayin da baiwarta Fidda ke rike da ita. 

Kamar ina jiyo kukan Kakata Sayyida Zahra (SA) a kan kabarin Shugaba (SA) tana rera masa koken irin zaluncin da wadanda ya musu wasiya da su bi ta sukai mata.

Ina tayaku jajen wannan rana ya ku Muminai. Ina hawaye da kuka ga abin da akaiwa Kaka mai girma ga Imamul Asr (AS). Tare da tawassul ga wannan jarabawar tata, akan Allah ya gaggauta hallaka mana Elrufa’I da Buhari da duk mai goyon bayansu ko mai tayasu aikin zaluntarmu a daidai wannan lokacin. Allah ya shudar da su kamar yadda ya shudar da Azzaluman farko!

Saifullahi M Kabir 

November 22, 2016

KUKAN KURCIYA; Ya Kai 'Dan Uwan Imani...

 Ya kai dan uwan addini, mai gwagwarmayar Musulunci karkashin Jagora. Tsakaninka da Allah ka yi tunani a karan kanka, cewa tun bayan da aka yi Waki'ar nan, shekara guda kenan kullum dawainiya ake yi da fuskantar abubuwan da ba makawa sai an fuskanta, don Allah, tsakaninka da Allah me ka iya yi na gudummawa wajen ganin an cimma wannan abin? 



Waki'ar nan ta ritsa da mutum sama da 3000, daga wadanda ba a gansu ba, Shahidai da Iyalansu da kuma masu rauni. Kullum kokarin Harka da masu tafi da ita shine ta wace hanya za su ga sun kyautatawa iyalan Shahidai da Mafkudai fiye da dubu da ake da su. Karatunsu, abincinsu da suturarsu. Don Allah kai me ka taba yi a wannan bangaren? Nawa ka taba badawa? 

Marasa lafiya ne daruruwa, har yanzu ana kan yi musu magani, ko yanzu haka akwai kusan sama da mutum 30 da ba makawa rauninsu ta sa sai an fitar da su asibitin waje don musu magani. Shekara guda kenan ba su gane kansu kullum ciwo. Don Allah wane gudummawa ka iya badawa na ganin wadannan yan uwan namu sun samu lafiya kamar yadda kake? Nawa ka bada a wannan kokarin da Harka da Jagorancinta ke yi? 

'Yan uwa ne sama da 200 a Kurkuku a Kaduna tsawon shekara guda kenan. Kullum dawainiyarsu ake yi. Kai me ka iya yi musu? Wane gudummawa ka iya basu? So nawa ka je ka ziyarcesu ka kyautata musu kamar yadda za ka yi burin hakan in a kanka ta fado? 

Shari'o'i ne daban daban aka shigar har guda hudu da Sunan Malam da Malama a Kaduna da Abuja. Ga wanda aka shigar da 'yan uwa na Kurkukun Kaduna, Kullum a kotu ake. Ba kawai Kotun Nijeriya ba har da na Duniya (ICC), Lauyoyi aka dauka ana biyansu miliyoyin Nerori. Don Allah dan uwa da yar uwa, tsakaninku da Allah nawa ka bada na gudummawa akan wannan aikin da aka tsayu da shi? Wane gudummawa ka iya ba wannan bangaren? 

Kullum ana buga Posters da Banners, sai dai ka gansu kala-kala ana rubuta "Free Zakzaky", ka san yadda ake ana wadannan? Sau nawa ka ba da gudummawarka akan wannan yunkurin? Nawa ka taba badawa na yin wannan aikin don Allah? 

Kullum cigaba ake da afkawa 'yan uwa a garuruwa, Harka da Jagorancinta ne kullum ke zama cikin damuwa da lamarin. Ita ke daukar nauyin abin. Kotu aka Kai 'yan uwa, ita ke daukar Lauyoyi su tsaya, a nemi beli in an ba da ta nemo ma'aikata da kudi su cike sharuddan belin a fitar da 'yan uwa. A yayin da suke tsare Harkar ce ke daukar nauyin abincin gidan magidanta har su fito, da abincin wadanda ke dauren. Asibiti ne aka Kai Masu rauni? Harka ke tsayawa, mas'ulanta a Da'irori ke kai kawo wajen hada kudin magani, gado zuwa sallama. Don Allah tsakaninka da Allah ko ke nawa ki taba taimakawa da shi, wane Kokari ki taba yi a wannan bangaren wajen ganin Masu yin wannan dawainiyar ba su wuce ka ba?

Alal misali, a garin Jos, inda na sani, a ranar Ashura an afka mana, aka kama yan uwa kimanin 50 Maza da Mata da yara, bayan an raunata wasu. Sai da aka wayi gari a farko an rasa mutum 5  wadanda za su tsayu da al'amarin 'yan uwan nan kusan 50 da aka kama, har aka Kai su Kotu aka turasu gidan Yari. Sannan aka zo aka samu damar daukar Lauya, aka rika kai komo. Halkoki suka raba kokarin ciyar da gidajen wadanda suke tsare. Wasu tsirarun da'irar suka tsayu da kullum suna Kurkuku suna kotu suna State CID neman beli. Sai da aka shafe kwanaki 23 aka samu belin yara. Sai da aka kwana kusan 38 sannan aka samu belin sauran yan uwan. A yayin da wasu suka tsaya kullum safe da yamma suna girka abincin da zai ishe yan uwan da ke daure suna kai musu. Wannan yasa dole duk Wani shiri da ake da shi na Da'irar ta sha ruwa. Mafi yawan lokaci tsirarun da ke wannan dawainiyar suna yi ne da kudin aljihunsu. Wai fa a hakan ba masu raunin da ke asibiti. 

In ka dubi irin wannan abin, ashe zai zama abin zargi ga wanda ke kokarin tafi da damuwowi idan ya zauna ya yi tunanin abin da ya fi dacewa da yanayi ya ayyana akan komai ma? Kai da baka komai sai ka zama abin zarginsa? 

Me yasa yankin Kano ba a samu damar cigaba da Tafiyar da aka faro ba? Tsakaninka da Allah kai da ka zama mai surutan an ki a yi kaza, an hana kaza a Facebook da whatsApp, daga lokacin Waki'ar Tattakin bana na yankin Kano makon da ya gabata zuwa yanzu wane gudummawa ka ba masu lura da lamarin wadanda Harin ya shafa? Mutum kusan 50 ke tsare. Ka ziyarce su? Me ka kai musu? Wane Kokari kake yi na ganin an ba da gawarwakin yan uwan mu da aka kashe aka rike? So nawa ka je gaban Jami'an tsaron don neman karbo su? Wa kake tunanin za su karbo su? Magidanta nawa ne a cikinsu? Wane gudummawa ka bada na ganin an ci da Iyalansu da daukar dawainiyarsu kamar suna nan? Wa kake tunanin zai yi? Harka ko? Manyan da zaginsu da jefa bakaken maganganu akan su ya zama ibadarka na safiya da maraice? 

Babu shakka abin mu yi Karatun ta-natsu sosai ne akan alakar da ke tsakaninmu da hakkokin da ke kanmu. Wallahi Allah ba zai kyalemu ba idan ya zama aikin wasu shine yiwa Harka Hidima, aikinmu kuma shine zagi da cin mutuncin Masu yin wannan hidimar alhali kwance muke a gado wayarmu na soke a chaji sama da fanka muna danna waya muna wane munafuki, ya hana a yi kaza ya ki ya bari a yi kaza. Anya kuwa Allah zai kyalemu, ba zai kama mu da laifin wannan miyagun dabi'un namu ba? 

Eh, Jagora ne yace: "Wanda bai shirya mutuwa ba ya ja baya." Amma me yasa Jagora ya dage Faretin Harisawa da aka saba yi duk shekara akai kusan shekaru 5 ba a yi ba, sai dai a tarasu a yi Kacici-kacici a yi wa'azi a watse? Haka na nufin tsaron Mutuwa ne? Ashe ba a samu lokacin da aka dawo da taron Mauludin Sayyida Zahra (SA) safe ba maimakon Yamma zuwa dare, saboda halin da aka tsinci kai na dokar Yakowa ba? 

Idan har zai zama komai na dawainiyar Harkar nan da matsalolinta hangoshi kake yi daga nesa, baka zuwa a tattauna da kai a samo mafita ka shige gaba a aiwatar da kai, bai kamata ya zama kullum sai dai ka bayyana a rubutu kana suka cewa an ki a yi kaza, an janye kaza da sauransu ba. Mu ji tsoron Allah. 

Ina rufe rubutuna da tunawa da fadin Imam Sadik (AS) da yake cewa: "Wanda duk ya kasance a muhallin da ake zagin Masoya Allah hakika ya sabawa Allah." wanda ke bamu wajabcin nesantar duk Group din da ya zama wasu sun daukarwa kansu zagi da izgili ga bayin Allah din da basu ma san suna yi ba. 

Giba na nufin fadin wasu maganganu marasa kyau ga Wani da bashi a wajen, kamar yadda marasa kunya da mutunci suka daukarwa kansu aikin yinsa a zaurukan 'yan uwa Musamman na WhatsApp. To Amirulmuminin yace mana, "Mai sauraren giba kamar mai yinta ne." Bayan kuma a Wani wajen yana cewa: "Mafi sharrin mutane shine wanda ya kasance dabi'arsa ta zama yada aibin wasu mutane yana kokarin boye nasa." Imam Musa (AS) yace: "Tsinanne ne duk wanda ke cin naman dan uwansa." 

Mu ji tsoron Allah. Mu kyautata alakamarmu da shi. Mu yi komai don Allah. Da yawa Masu zage zage da maganganun banza akan rashin Tattaki suna yi ne don gudun kar a ce sun ji kunya ko ace sun ja da baya. Wanda haka ke nuna ko da an fito da su sun fito ne don su nuna suna da wata izza ko isa ko don su ba da haushi ko su huce haushin. Kun mance Imam Husaini na cewa: "Ban fito (zuwa Karbala) ba ina mai fariya da jiji da kai, sai don na yi umurni da kyakkyawa da hani ga mummuna, ina mai kokarin jaddada sakon Kakana (S)." Ka yi tunani, tsoro ne yasa Manzon Allah ya ja baya da shiga Makkah lokacin sulhun Hudaibiyya, bayan kuma Sahabbansa sun masa bai'ar mutuwa a karkashin bishiya? 

Yanayi ke ba da damar komai. Allah ya tabbatar da mu. Ya tausaya mana. 


Saifullahi M Kabir 
20 Safar 1437 (20/11/2016)

LABARIN YAKIN SIFFIN

Bayan an gama yakin Jamal, Imam Ali (AS) ya dawo daga Basra zuwa Kufa a Rajab, shekara ta 36 bayan Hijira. Sai ya yanke shawarar kafa cibiyar gwamnatin sa a garin na Kufa saboda a wancan lokacin ita ce a tsakiyar kasashen musulmi, sannan hakan zai taimaka masa wajen hana Mu'awiyya shirin sa na zuwa kasar Iraqi.

Kafin Imam Ali (AS) ya fita yaki da Mu'awiyya, yayi ta kokarin sasanta al'amarin cikin lumana ta hanyar tura Jarir, gwamnan Hamdan; zuwa Syria a matsayin dan sako. Amma kuma sai Jarir ya shagaltu da abun da Mu'awiyya yayi masa, sai ya bata lokacin sa a Syria. Sai bayan wata uku ya dawo da wani sako marar amfani wai ba za'a zauna lafiya ba har sai an hukunta wadanda suka kashe Usman. 

Daga karshe dai Imam Ali (AS) ya gane cewa al'amura ba zasu daidaita ba har sai anyi yaki, ba tare da bata lokaci ba ya shirya yabi ta saharar Kudu maso yammacin Asia zuwa Riqqa a gabar kogin Persia. Sai suka gina gada ta tsallaka dasu gefen Syria, wani gari Sur al-Rum. Akwai wasu 'yan yakuna da aka gwabza da wasu rundunonin kanana, daga karshe dai a watan Zulhajjin shekara ta 36 bayan Hijira; rundunar Imam Ali (AS) ta hadu da babbar rundunar Mu'awiyya wacce tuni ta kafa sansani a Siffin. 

A Siffin, Mu'awiyya ya tura kwamandan sa, Abul A'awar; da sojoji 10,000 suka tsare kogin dake wajen domin hana sojojin Imam Ali (AS) samun ruwa. Sai Imam Ali (AS) ya turawa Mu'awiyya sakon cewa hakan da yayi ba daidai bane, domin ko ba komai wadanda ya hana ruwa din suma musulmi ne. Imam Ali (AS) ya sake tabbatar masa da cewa lallai ya kamata a bar dukkan sojojin suyi amfani da shi. 

Amma kuma, sai Mu'awiyya ya turo da sakon cewa ai lokacin da makasan Usman suka zagaye gidan shima an hana shi ruwa ne, saboda haka yanzu shima Mu'awiyya yana ramawa ne. 

Daga karshe dai Imam Ali (AS) ya fahimci cewa sojojin sa zasu sha wahala idan aka ci gaba da zama a haka, saboda haka ya tayar da wata runduna karkashin Malikal Ashtar. Jarumin Sadaukin daga karshe ya kwato kogin bayan yaki mai tsanani, ya kori Abul A'awar. Bayan wannan nasara, Imam Ali (AS) ya cika alkawarin da yayi ta hanyar barin sojojin Mu'awiyya suyi amfani da ruwan yanda suka ga dama. 

Imam Ali (AS) ya raba rundunar sa mai sojoji 90,000 gida bakwai, kowane kashi karkashin wani jarumi. Shi ma Mu'awiyya ya raba ta shi rundunar mai sojoji 120,000 zuwa gida bakwai. Kowace rana wani bangare na rundunonin zai gwabza da daya (daya daga cikin bakwai na kowane bangare). An yi wannan salon ne na yakin dai-dai domin Imam Ali (AS) na kokarin rage yawan mutuwar musulmi da yakin bai daya zai iya janyowa. Haka aka yi ta yi har watan Zulhijjah ya kare, watan Muharram ya shigo; wanda aka haramta yaki a cikin sa. 

A wannan wata (Muharram), Imam Ali (AS) yayi ta kokarin dakatar da yakin ta hanyar yin sulhu, amma abun yaci tura. Yayi alkawarin cewa lallai zai hukunta makasan Usman idan har Mu'awiyya ya nuna su. 

Amma kuma, Mu'awiyya baya son abun ya kare cikin sauki haka, saboda ta dalilin fansar Usman ne ya iya yaudarar mutane ya tara sojoji masu dimbin yawa haka. 

A watan Safar aka dawo yaki. Tsawon sati daya, ana yaki mai tsanani kullum. 

Kowace rana yaki na kara tsananta fiye da baya. A sati na biyu Imam Ali (AS) ya fito filin daga a karon farko. Bayan jerin fada da daidaikun mutane, a inda yake cin galaba akan duk wanda suka gwabza da shi saboda kwarewar sa, sai ya kasance babu wanda zai iya tarar sa kuma. 

Hakan ya sanya Imam Ali (AS) yake neman wanda zai iya karawa da shi. A irin haka, har aka samu wani Jarumi daga rundunar Mu'awiyya yace zai gwabza da shi. Da sara daya tak na Zulfiqar Imam Ali (AS) ya raba gangar jikin sa gida biyu, sama ya rabu da kasa!

Wadanda ke kallon fadan sun yi tunanin ma bai same shi ba, sai bayan dokin jarumin ya matsa gaba kadan inda suka ga kowane bari na jikin ya fadi gefe guda; sannan suka fahimci abun da ya faru. 

Sai ya kasance kullum yawan mutuwa sai karuwa yake yi, musamman a bangaren Mu'awiyya. Duk da cewa, a bangaren Imam Ali (AS) ma ya rasa wasu manyan sahabban manzon Allah (S). Daga cikin su akwai Hashim bn Utba da kuma Ammar bn Yasir. 

Ammar, wanda a lokacin shekarun sa 93 a duniya, daman Manzon rahama (S) ya sanar da shi cewa za'a kashe shi ne lokacin da yake yakar wasu yan tawaye kuma makiyan musulunci. Wannan kowa ya san haka, kuma saboda haka ne ma bayan an kashe shi sai aka samu rudani a bangaren rundunar Mu'awiyya. Yayi kokarin kwantar musu da hankali ne da cewa, tunda Imam Ali (AS) ne ya janyo Ammar yaki, to lallai shi ya janyo mutuwar sa. Sai yace Imam Ali (AS) ne dan tawayen da Manzon rahama (S) yayi magana akan sa, ba shi (Mu'awiyya) ba. Sai kuwa suka yarda da maganar sa, aka ci gaba da yaki har daren 13. 

A wannan rana, babban kwamandan rundunar Imam Ali (AS), Malikal Ashtar; ya kai wani harin jarumta kan makiya. An ji fadin sa na 'Allahu Akbar' duk lokacin da ya kashe mutum wajen akalla sau dari hudu. 

Yayin da wannan jarumi Malik ya fara cin galaba akan makiya sai Amr Al-aas daga bangaren Mu'awiyya yace, "A kira makiya zuwa ga maganar Ubangiji." 

Cikin sauri Mu'awiyya ya aminta da wannan magana, ya sanya sojojin sa suka daga kwafin alqur'ani guda 500 bisa masu, suna cewa littafin Allah zai yi sulhun wannan rikici. Wannan yaudara tayi galaba a zuciyar wasu daga rundunar Imam Ali (AS), suka yadda makaman su, suka yarda cewa littafin Allah zai warware komai. 

Imam Ali (AS) ya shigo cikin filin daga yana karfafa mutanen sa akan suci gaba da yaki kar su yarda da wannan yaudara ta Mu'awiyya, amma sai suka ki yarda. Sai yakin ya canja salo, inda daga karshe aka ce a wakilta mutum daya daga kowane bangare domin su yanke shawarar karshe. 

Imam Ali (AS) yaso ace Abdullah bn Abbas ko kuma Malikal Ashtar su wakilce shi, amma sai mutanen sa suka dage akan cewa Musa Ash'ari ne zai je. Mu'awiyya kuma ya zabi Amr Al-aas ya wakilce shi. Abu Musa bashi da salo ko dabara, kuma ko kadan ba sa'an Amr bane wajen iya yaudara.

A zaman da aka yi watanni kadan baya, Amr ya yaudari Abu Musa yaudara mai tsanani. 

Ta haka ne Mu'awiyya ya tsira daga shan kashi a yakin Siffin. Amma anyi rashi sosai a yakin. An kashe mutanen Mu'awiyya 45,000 inda Imam Ali (AS) ya rasa mutane 25,000. 

An samo wannan labari ne daga littafin "Gaskiya a tarihi".

Saifullah M Kabir 
15 Safar, 1438 (15/11/2016) 

November 12, 2016

12 Ga Safar: RANAR WAFATIN ANNABI HARUN (AS)

Annabi Haruna (AS) shine dan’uwan Annabi Musa (AS) a jini, kuma abokin isar da da’awarsa (sakon Allah (T) izuwa ga Fir’auna ma’abocin girman kai da ‘Dagawa. Ance Annabi Haruna (AS) ya kasance mai hikima wajen isar da magana. 


Annabi Musa (AS) ya sanya Annabi Haruna (AS) a matsayin halifansa a cikin mutanensa a yayin da zai je saduwa (ganawa) da Allah (T) a kan dutsen da ake kira “Jabalu Duur”. Sai ya zama bayan tafiyar Annabi Musa, wani Shaidani da ake kira Samiriyyu daga cikin mutanen Bani Isra’ila ya yaudari al’ummar Annabi Musa (AS) ta hanyar kawo musu ‘Dan-maraki (Ijil) da bayyana musu shi (Ijil) a matsayin shine Ubangijin hatta ma shi Musa (AS) din. Sai ya zamana al’ummar da Annabi Musa ya bar ma dan’uwansa Haruna (AS) lura da su, suka bijire ma bin Annabi Haruna, suka zabar ma kansu bin Samiriyyu tare da bautan wannan Marakin da Samiri ya kawo musu.


Ance hatta da Annabi Haruna ya matsa musu da wa’azi a kokarinsa na tunatar da su addinin Allah wanda Musa ya tafi ya bar musu, tare da cewa shine Halifan Musa (AS) din, amma sai suka nufi su kashe shi. Har ma suka masa kasheji akan cewa in har ka matsa mana zamu kashe ka.


Iri daya da abin da ya faru da wannan al’ummar ta Manzon Allah Muhammad (S); yayin da ya yi SHAHADA, ya riski Ubangijinsa yana Yardajje abin yarda, alhali ya nasabta ma al’ummarsa Shugaba Ali Dan Abidalib (AS) a matsayin halifansa a bayansa. Amma sai suka bijire a bayan baya nan, suka ki subi Imam Ali (AS) din. Sai ya zama Samiriyyun wannan al’ummar ya kawo Maraqin wannan al’ummar yace shi za’a bi, ya kasantar da shi a matsayin halifan Annabi akan wannan al’ummar. Har ya kasance sun ma Imam Ali (AS) barazanar kisa, ta yadda da ya ja musu a lokacin da sun nufi su kashe shi. 

Na’am, shi Annabi Musa (AS) ya bar Annabi Haruna (AS) ne a matsayin halifansa a cikin mutanensa kafin yaje ya gana da Allah (T) na tsawon kwanaki arba’in kawai ya dawo. Amma suka iya juya ma addininsa baya suka bijire ma halifan da ya bar musu, suka zabi wanda ransu yaso suka bishi. Tare da cewa sun san cewa fa Annabi Musa ba ya mutu bane, sun san zai dawo, amma kunga sun iya bijirema Haruna (AS), har ta kai ma ga suna masa barazanar kisa ma. To, me kake ma mamakin dangane da al’ummar Annabi Muhammad (S) da suka juya ma halifansa baya, suka zabi Maraqi bisa irshadin Samiriyyu, alhali suna da tabbacin Manzon Allah (S) ya riga ya koma ga Allah ba dawowa zai ba?

Shi fa Samiri din sahabin Annabi Musa ne babba, kun ga yadda ya batar da al’ummar Musa, ya hanasu subi Haruna ya kawo musu Ijil yace shi za su ma biyayya, to ya zai zama maka abin mamaki dan Samirin wannan al’ummar ya hana al’ummar subi Wasiyin Annabi ya kawo musu Ijil din wannan al’ummar yace shi zasu bi?

Kar kayi mamaki; domin su al’ummar Annabi Musa (AS) an kawo musu Maraqi ne suka bi a matsayin Ubangiji bayan gashi suna ganinsa fa dabba ne. Su kuwa al’ummar Muhammad (S) mutum ne Samirinsu, kuma ya kawo musu Mutum ne a matsayin Ijil dinsu suka bi a matsayin halifan Manzon Allah (S). Kaga idan ma abin mamaki da al’ajabin yiwuwar hakan ne, to kayi mamakin na wancan al’ummar da aka bar ma Haruna (AS) halifancinta ne, ba na Ali Dan Abidalib (AS) ba.


Ina taya al’ummar Duniya baki daya jajen zagayowar ranar da Annabi Haruna (AS) ya koma ga Allah (T). Dafatan wannan ranar zata kasance abin tunawar al’umma a duk lokacin da ta zagayo don daukaka ambaton wannan Annabi na Allah kuma Khalifan da Sahabban Annabinsa suka zalunce shi, suka ki su bishi, kuma suka nufi kashe shi.


Saifullahi M Kabir 
Muhdsaifu@gmail.com 
12 Safar, 1438 (12/11/2016) 

November 11, 2016

SHAHEED MUHAMMAD TURI A SHEKARU 55 MASU ALBARKA

Ranar 15 ga watan Safar din nan, ta yi daidai da ranar da Jarumi, Mujahidi, Uba, Malami kuma Shahidi mai girma, Shaikh Muhammad Mahmud Turi (RA) ya cika shekaru 55 cur da haihuwa. Madalla da zagayowar ranar haihuwar wannan yaro, matashi, kuma dattijon da ya shafe shekaru 40 cur yana biyayya ga Jagora, Shaikh Zakzaky ba tare da ya kauce ba.

A yayin da Jagoranmu (H) ke godiya ga Allah akan cewa, ya shekara 40 cur yana ibada (bautawa Allah) da yakini kamar yana ganin zahiri. ‘Dan kwarai, Amintaccen almajiri, Shaikh Muhammad Turi ya koma ga Allah ta hanyar Shahada ne bayan ya cika shekaru 40 cur yana biyayya ga jagoran da yake bautar Allah da yakini kamar yana ganin zahiri. 

Shaikh Muhammad Mahmud Turi 

Wane ne Shaikh Muhammad Turi?


Sunansa MUHAMMAD ne. Sunan mahaifinsa kuma MAHMUD, amma ya fi amfani da TURI MUHAMMAD (wato shi Mahaifin Malam din kenan). Don haka sai ya zama cikakken sunan Shaheed shine MUHAMMAD MAHMUD TURI.

An haifi Malam Muhammad Turi ne a ranar 15 ga watan Safar, 1383 Hijiriyya. Wanda ya yi daidai da 7 ga watan Yulin 1963, wanda yake nufin shekarunsa 55 yanzu a kidayar Hijira, a yayin da yake 53 da watanni a kidayar Miladiyyar Annabi Isa (AS).

Malam Muhammad Turi ya taso a gida ne na manyan mutane, masu dattako kuma masu rufin asiri. Muna iya cewa masu dukiya yadda za a fi fahimta. Ko ba komai, mahaifinsa Mahmud Turi, babban dan boko ne tun a wancan lokacin. Ya taba yin Manaja a kamfanin jaridar ‘New Nigeria’. Kuma ya zama Ciyaman a Vitafoam da Liason company of Nigeria. Don haka ya taso ne a gidan masu arziki daidai gwargwado. Amma bisa zabin Allah, sai Shaikh Muhammad Turi ya zabi ya zama mai addini, tare da kawar da kai daga dukiya da mai da fuska ga neman Lahirarsa, a yayin da ya rungumi Harkar Musulunci, ya kuma sallamawa Jagoranta hakikar sallamawa.

An haifi Shaikh Muhammad Turi ne a garin Zariya, kuma shine mutum na biyu a gidansu a haihuwa. Amma ya yi makarantar Firamare dinsa a Kaduna ne. sannan ya yi Sakandire a FGC Sokoto. Bayan kammalawa ya samu damar shiga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (ABU), wanda bai kai ga gama ta ba aka kore ‘yan uwa a ciki saboda Harkar Musukunci da suke yi, ciki har da shi. Don haka sai Shaikh ya koma Jami’ar Maiduguri (Uni-Maid) ya karanci Lissafi ‘Accounting’

Har ila yau, Shaikh Muhammad Turi ya je International University of Africa a Khartoum, inda ya karanci Shari’a. Ko ba komai tun yana Firamare yana yin karatun addini a wajen Malamai daban-daban a Kaduna da ma Sokoto.

A gurguje, Shaikh Muhammad Turi (RA) ya fara haduwa da Jagoranmu Shaikh Ibraheem Zakzaky ne a wajen wani taron IVC, wanda a lokacin Shaikh Turi yana dan shekara 14 a Duniya. Amma tun daga wannan lokacin, ya mika bai’arsa ga Jagora, bai taba ko gezau ko ya yi rawa da hannun ba har zuwa lokacin da sojojin Nijeriya suka Shahadantar da shi a yayin da yake kokarin ba da kariya ga Jagora (H) a shekarar bara. Lokacin yana da shekaru 54 a Duniya. Wanda yake nufin Malam Turi ya shafe shekaru 40 cur yana tare da Malam kuma yana binsa, bai taba ajiye kafarsa ba face a wajen da Malam (H) ya daga tasa.

Shaikh Ibraheem Zakzaky tare da Shaheed Muhammad Turi 

Don haka ne ma Shaikh Muhammad Mahmud Turi, ya kasance wanda ya samu shaidar samun soyayya daga Jagora (H), a yayin da aka ruwaito Malam Zakzaky yake cewa: “… Kuma raina ya zauna da shi (Malam Turi) tun bayan wata magana da ta gudana tsakaninmu muna kurkukun Kaduna tare, kuma na ji kaunarsa ya shiga zuciyata. To naji cewa ba wanda ya kamata lalle ya rike wannan al’amari face Malam Turi, saboda wasu dalilai wanda ba zan bayyana su a nan ba, ba ma zan gaya wa kowa ba.”

Don haka ne ma a cikin maganarsa a yayin da yake ta’aziyya ga ‘yan uwa akan Shahadar Shaikh Turi, Malam Yakubu Yahaya Katsina yake cewa: “Malam Muhammad Turi ba kawai hannun daman Sayyid Zakzaky bane, a’a shi rabin jikinsa ne.” Ya kara da cewa: “Ya kasance mai biyayya da sallamawa.” ‘Yan uwa, wane ne zai maye gurbin Shaikh Turi ga Jagora a cikinmu?

Shaheed Muhammad Turi a sahun Muzaharar Qud's 

Magana akan Shaikh Muhammad Turi, rayuwarsa da dabi’u da kuma halayyarsa abu ne mai fadin gaske da ke bukatar taron dangi daga marubuta kuma masana game da rayuwar tasa da kuma masu bincike. Don haka ma nake shawartarsu akan yana da kyau a bazama ga ruwaito ma Duniya irin halayya da dabi’un wannan Mujahidi mai girma. Madalla da wanda duk lokacin da ka gansa sai ka tuna da umurnin Allah na yin Salati ga Annabi (S) da Iyalan gidansa.

Wannan bawan Allah mai girma, ya yi Shahada yana da matarsa daya, Malama Maimuna Abdullahi. Wanda kuma Allah ya albarkace su da samun zuriya masu albarka. ‘ya’yansa shida duk cikansu mata. Fatima (Amira), Zainab, Maryam, Nusaiba, Hakima da Sukaina. Kuma ya aurar da hudu tun kafin Shahadarsa, saura biyu ne ke kan hanya suma insha Allah. 

Shaheed Turi tare da Jikokinsa.

Sannan kuma Shaikh Muhammad Turi yana da jikoki 8 a yanzu haka; hudu maza hudu mata. ‘Ya’yan Malama Fatima 3, Zainab 3, Maryam da Nusaiba dai-dai. Muna fatan Allah ya raya su, ya kara musu albarka.

Allah ya kara aminci ga Shaheed Muhammad Turi. Ya bamu I tasu. Wassalamu alaikum wa Rahmatullah.


Saifullahi M Kabir 
muhdsaifu@gmail.com 
http://saifmkabir.blogspot.com.ng
11, Safar 1438 (11/11/2016)


November 10, 2016

TAKAITACCEN TARIHIN SHAIKH IBRAHEEM ZAKZAKY (H)


Wannan bawan Allah mai girma, Jagoran Harkar Musulunci a Nigeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky, an haife shi ne a ranar Talata 15 ga Sha’aban shekarar 1372 Hijiriyya, wato yanzu haka ya cika shekaru 65 daidai da haihuwa. A Miladiyyah kuwa haihuwar ta kasance ranar 5 May, 1953. A wannan lissafin zai zama shekarunsa 63 da watanni a yanzu.


Sunansa Ibraheem, ana masa lakabi da AlZakzaky, Kuma Shaikh Usman Danfodiye ya masa lakabi da Sharafuddeen da kuma Ibraheemul Magribiy (Kariyar Allah su kara wanzuwa a gareshi).

Sunan mahaifin Shaikh Ibraheem Zakzaky shine Yaqoub, kakansa kuwa sunansa Ali dan Malam Tajuddeen, shi kuma dan wani babban limami da ake kiransa da Liman Husaini. Dan haka kakan Shaikh Zakzaky na uku ya kasance daga cikin mutanen Shaikh Usman Danfodiye, wadanda ya tura su garuruwa a matsayin wakilansa, sai ya kasance shi Malam Muhammad Tajuddeen Shaikh Danfodiye ya turo shi Lardin Zazzau ne a matsayin mai ba Amir din Zazzau, Malam Musa shawara da taimakonsa wajen tafiyar da harkokin al’umma akan tsarin Musulunci.

Ashe duk wani wanda zai zo da batun asali ya jingina wa kansa a matsayin shi dan Zazzau ne, to yana bayan su Shaikh Zakzaky ne! Domin kuwa kakansu ne suka kafa Mulkin Zariya, duk kuwa da cewa a wancan karon sun kafa Mulkin ne bisa nizamin Musulunci, a yanzu kuma ana tafi da ita bisa nizamin turawan yamma karkashin Kwansitushen.

Ta Mahaifi da Mahaifiya, Shaikh Ibraheem Zakzaky shi Bafullatani ne, kuma asalinsu mutanen kasar Mali ne. Sunan Mahaifiyar Shaikh Ibraheem Zakzaky Hajiya Salaha, ana kiranta da ‘Hari’ (Wanda yake suna ne da ake kiran wanda aka Haifa da damina a Fulatanci). Mahaifinta kuma shine Malam Muhammad Gidado dan Malam Abdulkadir, wanda asalinsa daga Fulanin Mali ne.

Mahaifin Shaikh Zakzaky, Malam Yaqoub ya rasu tun a shekarar 1972, kimanin shekaru 44 da suka wuce, a lokacin Shaikh Ibraheem Zakzaky yana dan shekara 19 a Duniya. Malam Yaqoub ya yi Shahada ne a wani Kududdufi (ruwa) a yayin da ya ga wata akuya ta fada za ta mutu sai ya yi kokarin ceto ranta. Ita kuwa Mahaifiyarsa ta rasu ne a watan Nuwambar 2014. Shaikh Ibraheem Zakzaky shine na biyar a cikin ‘ya’yan da Mahaifinsa ya Haifa su 16.

Abubuwa guda biyu da Shaikh Ibraheem Zakzaky ya tsayu da su tun tasowarsa har zuwa zamansa matashi sune karatu da zuwa gona. Dabi’ar mahaifinsu Shaikh Zakzaky shine baya fara tura dansa gona sai ya sauke Alkur’ani mai girma. Idan kuma ka yi dubi da cewa mahaifin su Shaikh Zakzaky ya yi Shahada ne a yayin Shaikh Zakzaky na da shekaru 19 a duniya, za ka iya fahimtar cewa Shaikh Zakzaky tun yana da kankanin shekaru ya sauke Alkur’ani, saukar gaske ba irin ta yanzu da akan yin a zu-zu ba! 

“Duk wani littafi da ake karantawa a zaure na Mazhabar Malikiyya da na Sunnah da na Lugga, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya karance su a zaurukan Malamai tun yana karami.” Wannan ne shaidar da kanin Shaikh Zakzaky wanda suke uwa daya uba daya, Malam Badamasi Yaqoub ya ba da. Wanda za ka sha mamaki idan ka ji wani makiyin Shaikh Zakzaky yana jingina jahilci ko rashin karatu gareshi.

Cikin malaman Shaikh Ibraheem Zakzaky, baya ga mahaifinsa, wanda sun kasance shi da yayyinsa suna karatu a wajensa tun suna kanana, har ma babban wan su Shaikh Zakzaky, wanda yake shi Dan Izala ne, yake cewa: “Ibraheem ya kasance mai hazaka sosai.”, an tabatar da cewa hatta kannin Shaikh Zakzaky idan suka mance karatunsu shi yake tuna musu, tare da cewa bai kai inda suken ba. Amma dake yana jin sadda ake biya musu kafin a zo kansa, dan haka yakan rike nasa ya rike nashi. 

Shaikh Zakzaky ya yi karatu a wata Shahararriyar makarantar allo da ke gidan Sarkin Ladanai, sannan kuma ya yi karatu a wajen Malamai daban-daban, daga cikinsu akwai Malam Sani Abdulkadir na Kwarbai, wanda Shaikh Zakzaky ya yi karatun Allo a wajensa da kuma karatun littafai musamman ma na koyon Larabci da Nahawunsa. Ya kuma yi karatun littatafai a wajen Malam Isa na madaka, Malam Sani Na’ibi da kuma Malam Ibrahim na kakaki da sauran Malamai daban daban, wanda an tabbatar da cewa babu wani Malami da ke ba da karatu a Zariya wanda Shaikh Zakzaky bai je zaurensa ya kwashi ilimi ba.

Tare da cewa Shaikh Zakzaky ya yi makarantun koyon Larabci, daya a Zariya, wacce a lokacin yana yinta, kuma yana koyarwa a makarantun Islamiyyu daban daban a unguwannin Kwarbai, Kakaki, Lemu da Rimin tsiwa. Sannan makaranta ta biyu da ya yi itace S.A.S (wato School for Arabic Study) a Kano, wanda Shaikh Zakzaky ya je dan ya karanta Arabiyya ne, amma sai suka masa tambaya da Turanci suka ji yana ta amsa musu da Turancin (Tare da cewa bai yi ko Firamari ba!) sai kawai suka bashi Grade-Two, bayan shekara 5 Shaikh ya ci jarabawar gama wannan makarantar, wacce hakan ta ba shi damar shiga Jami’ar Amadu Bello kai tsaye.

Kuma a lokacin da Shaikh Zakzaky ke yin wannan makarantar ta SAS a Kano, a tsawon wannan shekarun, ya rika amfani da damammakin da ya samu wajen zuwa zaurukan Malamai daban daban a garin Kano yana yin karatun littatafai. Misali, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya yi karatun littatafai gaba da gaba a wajen Shaikh Nasiru Kabara na tsawon shekaru. Ya kuma yi a wajen Shaikh Isa Waziri Kano, da wajen Malam Ibrahim Babarbare da Malam Nuhu Limamin masallacin Yola da ke cikin birnin Kano. Ya yi karatu a wajen Malam Datti Ahmad, Malam Abdulra’uf Usman (wani mutumin Misra) da sauran manyan Malamai masu yawan gaske.

Rayuwar Shaikh Zakzaky gaba daya ta kare ne a karatu da karantarwa, sai kuma gwagwarmayar yunkurin dawo da koyarwar addinin Musulunci da Shaihin ya sakama gaba, wanda hakan ya auku ne sakamakon yadda Shaikh Zakzaky ya ga lalacewar kasar nan ta kai makura tun yana jami’a ta yadda kwata-kwata, tare da cewa kasar nan Musulunci ya taba iko da ita a lokacin Shaikh Usman Dan Fodiye, amma sai aka wayi gari yanzu ba addini ke iko ba, face wani tsarin mulkin turawan yamma wanda suka yi hannun riga da Musulunci. Sai Shaikh Zakzaky ya daurawa kansa nauyin kira zuwa ga komawa tsarin Musulunci da yunkurin tabbatar da shari’ar Allah a doron kasa, tare da tarbiyantar da al’umma akan irin koyarwar Manzon Allah Muhammad (S).

Wannan ne yasa tun da Shaikh Ibraheem Zakzaky ya fara wannan kiran, a lokacin yana Jami’ar Amadu Bello Zariya (ABU) ya fara fuskantar barazanar kamu a kulle shi daga mahukuntan kasar Nigeriya, masu kare muradun turawan yamma. Ya zamana I zuwa yau da a yanzu haka Shaikh Zakzaky yana tsare, an kama shi ya fi sau goma, kuma ya shiga gidan kurkuku daban daban a fadin kasar nan. Na karshe kafin wannan shine na lokacin Sani Abacha wanda aka zargi Shaikh Zakzaky a kotu da cewa yace Babu Hukuma Sai Ta Allah!

Janibobin rayuwar Shaikh Zakzaky (H) suna da fadin gaske. Misali akwai labarai daban daban na gwagwarmayarsa a makaranta da alakarsa da sauran mutane. Akwai kuma labarin fara da’awarsa zuwa yau. Abubuwan da ya fuskanta na jarabawa musamman daga azzaluman mahukunta da kuma janibobi daban daban na rayuwarsa kamar aurensa, ‘ya’yansa da zamantakewarsa da sauransu. Wanda muna sa ran marubuta za su tattabo mana wasunsu a wannan daren.


- Saifullahi M Kabir 
13 Sha’aban 1437 (20/50/2016)

November 09, 2016

RANAR SHAHADAR AMMAR BIN YASIR (AS)

A rana mai kamar yau, 9 ga watan Safar a shekara ta 37 da hijira, rundunar makiya Allah (T) masu ketare iyaka, kuma batattu, a karkashin jagorancin jagorancin sarkin Sham, Mu’awiya ‘Dan Abi Sufyan (L) suka shahadantar da Sahabin Manzon Allah (S) mai suna Ammar Bin Yasir (RA).


Sahabi Ammar Bin Yasir, ya kasance ma’abocin falala da fifiko mabayyani, ta yadda ya kasance mahaifiyarsa Shahida Sumayyah (RA) itace farkon wanda ta fara yin Shahada a duk fadin tarihin wannan addini na Musulunci. Tayi shahada ne ta hanyar soka mata gasasshen mashi wanda wuta ya dafashi ya yi jawur a cikin al’auranta Tsarkakakkiya. Ta hakan ta zama farkon Shahidi a wannan addinin.

Mahaifinsa Yasir (RA) ya kasance amintacce kuma Mujahidin a kwarai, ya taiamaki Manzon Allah (S) iyakan iyawarsa. Kuma shima bai sadu da Allah (T) ba face yana matsayin Shahidi. Wannan matsayi ne babba ga Sahabi Ammar bin Yasir a matsayinsa na wanda mahaifansa biyu suka kasance Shahidai a wannan addini na Musulunci.

To kuma shi Ammar bin Yasir ya kasance daga cikin amintattun sahabban Amirul Muminin (AS). Tun bayan wafatin Manzon Allah yake tare da Amirulmuminin Ali (AS) haka kuma bai koma ga Allah ba face yana matsayin mai kare Addinin Muhammad (S) ta hanyar Amirulmuminin (AS) a yakin Seffin.

Manzon Allah (S) ya yi bushara da cewa; “Runduna masu ketare iyaka ne zasu kashe Ammar”. Yalai ko sai ya zama Rundunar Mu’awiyya dan Abi Fusyan ne suka kashe Shahabi Ammar a yayin da yake cikin rundunar Imam Ali (AS) a yakin Siffin. Ya yi shahada yana dan Shekaru 93 a Duniya.

A irin wannan rana, ina taya daukacin al’ummar Musulmi jajen shahadar wannan Sahabi mai girma, tare da addu’ar Allah ya kara la’anta ga rundunar azzalumai, masu ketare iyaka kuma batattu. Allah ka la’anci shugabanta Mu’awiya da duk wadanda sukai musharaka wajen yakar Imam Ali (AS) madamar sun koma ga Allah (T) basu tuba ba.


— Saifullahi M Kabir
9, Safar 1438H

YAU CE RANAR DA AKA FARA YAKIN NAHRAWAN

Yau Ce Ranar Da Aka Fara Yakin Nahrawan 

Daga Saifullahi M Kabir


November 07, 2016

IMAM HASAN ALMUJTABA (AS)

Ya kasance mafi ibada a cikin gaba dayan mutanen zamaninsa. Babu wani wanda ya kai shi falala, daraja da matsayi tare da sallamawa cikakkiya ga Allah da ManzonSa (S) a lokacin rayuwarsa. 

Imam Hasan (AS), wannan da shine babban jikan Manzon Allah Muhammad (S), kuma sanyin idaniyarsa, an ruwaito cewa duk lokacin da aka ambaci mutuwa ko kabari ko tashi bayan mutuwa ko tsayuwar Lahira akan ga hankalinsa ya tashi har ta kai ga yana zubar da hawayensa masu albarka.

Shine mai kaskantar da kai na hakika a duk lokacin da ya tsaya gaban Allah (T) da nufin yin Sallah. Kafin nan ma, an ruwaito cewa, duk lokacin da ya nufi yin Sallah akan ga fuskarsa ta sauya, jikinsa ya yi sanyi. An tambaye shi akan hakan, sai yace; Ya b azan fita hayyacina ba alhali zan tsaya gaba da Mahalicina?

Duk sanda aka ambaci Aljanna da Wuta, za ka ji Imam Hasan (AS) ya yi addu’ar cewa: “Allah ka azurtani da Aljannarka da falalarKa, ka kiyaye ni daga wutarka da afuwarKa.” Bai taba tsammani ko zaton cewa ya aikatawa Allah abin da ya kai ya bashi Aljanna ba idan bad a falala da afuwar Allah (T) ba.

Shine wannan da duk lokacin da zai je Hajji yana tafiya ne akan kafafunsa (Tattaki) ba tare da ya hau abin hawa ba. Imam Hasan (AS) ya yi hajji sau 25 da kafafunsa masu albarka. Ya fadi cewa; “Ni ina jin kunyar na sadu da Ubangijina ba tare da na taka da kafafuna na ziyarci dakinSa ba.”

Duk lokacin da yaji an karanta, ko kuma shi ya karanto fadin Allah (T); “Ya Ayyuhallazina Amanu” (Wato ‘Ya ku wadanda kuka yi imani), Imam Hasan (AS) yana tsayawa, yace; “Labbaikallahumma Labbaik!” Wato, ya kasance mai amsa kiran Allah a duk lokacin da ya ambata kiran nan nasa ga muminai.

Idan Imam Hasan (AS) ya doshi Masallaci da nufin Sallah, yakan tsaya a kofar Masallacin ya daga kansa sama, sannan yace; “Daifuka bi babika Ya Allah. Ya Muhsinu, kad atakal masi’u, fatajawaza an kabihi ma indi bi jamili ma indaka Ya Kareem.” Yana mai kirari ga Allah da neman ya canza masa munanansa zuwa ga KyawawanSa Madaukaki Mai Kyautatawa.

Ya kasance baya taba yin Magana da kowa idan ya gama Sallar Asubah, har fitowar rana, ba zai gushe ba yana Ta’akibat din bayan Sallar Subahi. Bai gushe ba a kullum, Imam Hasan (AS) baya bacci sai ya karanta Suratul Kahfi. 



Wannan bawan Allah mai girma shine ya yi Shahada a ranar 7 ga watan Safar shekara ta 49 da Hijira, sakamakon guba da Mu’awiya dan Abusufyan ya ba matarsa ta shayar da shi, wanda ya tsittsinka hanjinsa, ya canza launin fatar jikinsa, ya kuma yi sanadiyyar Shahadarsa bayan ya yi jinyar kwanaki 40 cur a jere.

Amincin Allah ya kara tabbata a gareka Ya Imam Hasan Dan Ali Dan Abudalib (AS).

— Saifullahi M Kabir 
7 Safar, 1438.