March 02, 2019

Shekaru 3 Da Kisan-kiyashin Zariya (10)


Daga Saifullahi M. Kabir

KAWO WA SHAIKH ZAKZAKY SAMMACIN KOTU

Bayan hakan da ’yan kwanaki, a ranar 2/5/18 sai ga wani ‘Registerer’ din kotu daga Kaduna ya zo inda ake tsare da Shaikh Zakzaky, wai ya kawo sammacin kotu.

Kamar yadda wannan din ma Shaikh Zakzaky ya sanar da Sayyid Muhammad ta waya labarin abin da ya faru, Shaikh din ya bayyana cewa bai karbi takardar ba, kuma bai sanya hannu ba, har ma ya ce a mayar da ita, a ce ba zai karba ba, kuma ba zai sa hannu ba, kuma ba zai je kotun ba, sai dai in za a kai shi da bakin bindiga!

Shaikh Zakzaky ya fada wa Sayyid Muhammad cewa; “To, a nan sai na fa]a wa (mai kawo sammacin) cewa, ka gane wannan al’amari fa, mu aka kawo wa hari, aka bude mana wuta, aka harbe mu da bindiga, aka kashe mutane sama da 1,000, ciki har da ’ya’yanmu. Ni da matata an harbe mu, ni an ja ni a kan gawar ’ya’yana ne. Sannan kuma aka kawo mu nan aka kulle duk cikar mu da harsasai a jikinmu. Yanzu haka muna fama da ciwo duk jikinmu da harsasai.”

Ya ci gaba da cewa; “To, sannan mu muka kai kara kotu, muka ce don me ake tsare da mu? Suka tura Lauyan gwamnati, ya ce suna tsare da mu ne domin su kare mu. Kotu bayan ta gama jin kowane bangare ta fitar da hukunci, cewa, lallai ba wata doka a Nijeriya ko wacce Nijeriya ta saka ma hannu (ta kasar waje), wadda ta ba da dama gwamnati ta tsare wani mutum da sunan tana kare shi. Saboda haka (kotu) ta hukunta cewa a sake mu ba tare da gindaya shara]i ba. Yau an kwashe kusan shekara da watanni shiru, ba su bi umurnin wannan kotun ba. Sannan kuma yanzu ka zo ka ce wai ka kawo za a kai ni kara? Wannan bai da ma’ana ai.”

A nan sai shi mai kawo sammacin ya nemi ya yi jayayya da Shaikh Zakzaky a kan sai fa Shaikh din ya saka hannu a wannan takardar, don haka Shaikh ya yi masa magana mai zafi. Cikin abin da Shaikh Zakzaky ya fada masa; “To in kai ma bangaren ‘problem’ din ne (zaluncin da ake mana), don ka sani, kun yi kadan! Tunda da bindiga kuka harbe mu kuka zo da mu nan, to yanzu ku zo da bindigar ma ku sake harbin, ko ku yi abin da kuka so.”

Shaikh Zakzaky ya ce; “Sai ya nemi ya fita ya bar takardun. Sai muka ce masa, ba ka isa ba sai ka dauki abinka. Daya daga cikin ma’aikatansu na DSS sai ya Dauka, sai muka ce a’a, sai an ba shi. Lallai sai an ba shi takardun. Sannan dole ya karbi takardun. Kuma muka raka shi ya tsaya a waje, duk sai suka taru (su ’yan security) suka hadu, shi kadai ne fa (dan sakon), muka tsaya a kofar wajen muka ce lallai sai an fita da shi. To, a nan ne ma nake ce wa shi wanda ya zo da shi, fita da wannan ]an iskan daga nan, na ga shi ‘is part of’ abin. Ka fita da shi da wuri. Ya kwashe takardunsa aka sa shi ya shiga mota aka yi waje da shi. Sai da muka tabbatar motar ta tafi, ta bace da gani, sannan muka dawo.”

Shaikh ya ci gaba da cewa; “To, ni abin da ban gane ba shi ne, shi wannan mutumin ya ba ni mamaki. Shi ya zo a matsayin Dan sako ne, amma wai sai an sa hannu. To, kuma ka ga kamar yadda nake ce maka, ka ga su mutanen nan, su suna nan a kan bin umurnin abin da aka ba su ne. Dama tuntuni su Saudi-Arabiyya da suka biya su suna ta ba su umurnin cewa, lallai a kashe ni. Lallai a kashe ni kawai. Kuma tuntuni suke masu wannan. To, kuma ga dukkan alamu tunda abin da suke nufi shi ne tunda su sukan kai mutum kotu ne a Saudi-Arabiyya, su yanke masa hukunci su ce sun kashe shi, to shi ma abin da suka ba su umurnin yanzu su yi ke nan.”

Ya kara da cewa; “To, lokacin da suka bude mana wuta ai ba kotu suka kai mu suka yanke mana hukunci ba, sun zo sun bude wuta ne. Yanzu ma mene nasu na zuwa su kai kotu sannan su yanke mana hukuncin kisa? Yanzu su zo da bindigar mana su harbe, me ya rage kuma?”

Ya ce; “Kuma alhali ba yadda za a yi bayan kotu ta ce, tsare mun da ake yi ba bisa ka’ida ba ne, a sake mu, sannan wani ya zo don rashin kunya ya ce wai kuma yana karar mu a kotu. Wace kotu kuma bayan ta yanke hukunci? Ana wani hukuncin ne a kan wani hukuncin? Hukuncin da ba ku bi ba, an riga an ba ku umurni ba ku bi ba, sannan kuma ku ce ku kuna wata kara? In dai ba bindigar nan za ku sa (ba)! Sai dai in bindiga za su saka kamar yadda suka saka mana da farko. Amma Wallahi sun yi ladan, su ce wai mu mu tashi wai mu je, wai akwai wata tsiya wai ita kotu, wai tana mana hukunci, Wallahi sun yi kadan. In dai bindiga ce tana nan a hannunsu, kuma mu ma jininmu yana nan a tare da mu, saboda haka ku zo ku gama shekarwa. Zance ya kare.”


KAI SHAIKH ZAKZAKY KOTU A KADUNA DAGA ABUJA

To, bayan wannan kawo sammacin da ya faru a ranar 2/5/2018, kwatsam da subahin ranar Talata, 15/5/2018, sai kuwa jami’an tsaro suka zo don tafiya da Shaikh Zakzaky kotu da bakin bindiga.

A wannan ranar gamayyar jami’an tsaro sun zo inda ake tsare da Shaikh Zakzaky da misalin karfi 5:00 da mintoci, na safe, a daidai lokacin Shaikh ya sallame Sallar Asubah yana addu’o’in bayan Sallar (Ta’akibat), sai kawai suka ji ana buge-bugen kofofi, tare da kabbarori. Ashe suna yunkurin balla kofar dakin da yaran Shaikh Zakzaky suke ne, a yayin da yaran suke kabbara.

Majiya mai tushe ta tabbatar mana cewa, bayan sun haura inda Shaikh Zakzaky yake, sun bugi kofar dakin da yake ne suka balle, suka shiga suka rika haukataku, har wasunsu na cewa yana jiran mene? A yayin da Shaikh Zakzaky ke kokarin saka rawani, suna rirrike shi suna kokarin fita da shi da karfi. Da kyar Shaikh ya samu ya saka takalminsa a yayin da suke jan sa, ba su bari ya saka abayarsa ba sai bayan da suka fito da shi.

Haka suka fito da Shaikh Zakzaky suna rirrike da shi, ba su dubi tsufansa a matsayinsa na Dattijo mai shekara 67 ba, ba su yi la’akari da raunukan da ke jikinsa na harbin da sojoji suka masa a kafa, hannu da ido ba, suka rika musguna masa, har suka sanya shi a tsakiyar mota a baya, gefe da gefensa a cikin motar akwai jami’an tsaro kowanne rike da bindiga har da bindigar da suke saka wa mutum ta yi masa shokin.

A yayin da ita ma Malama Zeenah, suka shiga suka fito da ita suka saka ta a wata mota ta daban. Haka ma sauran ’yan’uwan da suke tare da su, su uku, suka saka wa biyu ankwa a hannayensu, dayar kuwa bayan ankwar hannu har da mari a kafa. Suka shigar da kowaccensu mota aka tafi da su Kaduna.

A haka suka kai Shaikh Zakzaky kotu da karfin tsiya, da bakin bindiga a wannan ranar Talata din. Ranar ta dace da karshen watan Sha’aban din shekarar 1439 ne, inda daga nan aka fara yi wa su Shaikh Zakzaky haramtacciyar Shari’a.


HARAMTACCIYAR SHARI’A A KADUNA

A wannan ranar da aka dauko su Shaikh daga Abuja, kai tsaye an taho da su wata babbar kotu ne a Kaduna, a yayin da shi kansa Shaikh Zakzaky din sai da aka isa aka bude motar ya sauka sai ya gane ashe duk wannan haukar da ake masu za a kawo su kotu ne.

Bayan shiga kotu aka fara Shari’a, a yayin da ya kasance tunda ana da labarin yiwuwar kawo Shaikh sin kotu a wannan ranar, tuni wasu daga Lauyoyin Shaikh Zakzaky da suka hada da Barista Maxwell sun hallara a kotun. Haka su ma Lauyoyin gwamnatin Kaduna, karkashin Barista Bayaro Dari sun kasance a kotun.

A nan Alkali ya nemi ganin ragowar mutum biyu da ake karar da su, sai Lauyan Gwamnati, Bayero ya nemi Alkalin ya ba shi dama kafin zama na gaba don ya isar da takardar sammaci ga ragowar mutum biyun a Kano da Katsina.

Lauyoyin Shaikh Zakzaky sun nemi kotun ta ba da belinsa da matarsa a wannan ranar, amma sai Alkalin ya ce sai dai su rubuto takardar neman belin su kawo wa kotu a rubuce. Sannan Jojin ya yi tambayar a ina ake tsare da su Shaikh Zakzaky da matarsa a yanzu? Aka sanar da shi cewa suna hannun DSS ne. Sai ya yi umurni a ci gaba da tsare su a hannun DSS din, maimakon mai da su gidan yari.

Daga nan ne kotun ta fara tattauna batun daga Shari’ar da sanya sabuwar ranar da za a dawo kotu don ci gaba da Shari’ar. Alkalin ya saka cewa za a dawo bayan mako biyu ne, amma sai Shaikh Zakzaky ya kira Lauyansa ya tambaye shi, bayan mako biyu din za mu zo kotu? Ya ce masa eh za ku zo. Sai Shaikh ya ce masa a bari sai bayan Ramadan! Sai aka ce yaushe ne Ramadan din? Shaikh Zakzaky ya ce tana iya yiwuwa ya zama jibi 17/5/18 ne, kuma za a kwana kamar 30 ana Ramadan, bayan Sallah sai a dawo. Nan Alkalin ya ce ya yi yawa. Lauyan ya ce masa haka wanda muke karewa yake bukata. Don haka sai Alkalin ya ce za a daga zuwa 21/6/2018. Aka ce ya yi.

Ranar Laraba 20/6/18 ana gobe komawa kotu, ’yan’uwa suka fita gagarumar Muzahara a Kaduna, wadda ’yan sanda suka bude wuta, har suka raunata mutane uku. Haka ma washegari Alhamis, 21/6/18, ’yan’uwa sun sake fitowa Muzaharar, nan ma ’yan sanda suka sake bude wuta har suka shahadantar da mutane uku, kamar yadda muka yi bayani a babin waki’o’i.

A wannan ranar Alhamis din, sai ba a kawo su Shaikh Zakaky kotun ba, aka ce wai me Keke-Napep ya kade Alkalin, don haka yana jinya ba zai samu damar zuwa kotun ranar ba. Nan take ba a saka ranar da za a dawo ba, sai daga baya babban Lauyan Shaikh Zakzaky Femi Falana SAN ya je kotun aka saka sabuwar ranar da za a koma.

Ranar Alhamis, 2/8/2019 ne aka koma kotu don ci gaba da haramtacciyar Shari’ar da ake wa su Shaikh Zakzaky. A wannan ranar Mai Shari’ar Gidiom Kurada ya halarci kotun. Sai dai har a sannan ba a iya zuwa da sauran mutum biyu da ake karar tare da su Shaikh Zakzaky ba, don haka sai ya ba da umurnin a kamo su kafin a ci gaba da zaman, inda ya sake daga zaman zuwa ranar 4/10/2018. Sai dai a wannan ranar ne ya karanto wa Shaikh Zakzaky laifuffukan da ake tuhumarsa da aikatawa, inda Shaikh Zakzaky ya musanta su baki daya, ya kuma bayyana su a matsayin raini da zagi ga ‘shaksiyyarsa’.

Alhamis 4/10/18 aka sake komawa kotun don duba yiwuwar ta ba da belinsu kamar yadda Lauyoyinsa suka nema a zaman farko aka ce sai sun rubuto. Sai dai kuma a wannan ranar ba a kawo Shaikh Zakzaky da maidakinsa kotun ba, bisa hujjar da Lauyan gwamnati ya bayyana a cikin kotu na cewa a wannan ranar Shugaban kasa zai zo Kaduna, kuma babu isassun jami’an tsaron da za su ba shi tsaro a lokaci guda su bai wa Shaikh Zakzaky.

Wannan ta sa ba a yi Shari’ar ba, balle a yi batun ba da beli. Aka kuma dage ci gaba da sauraron karar zuwa 7/11/2018. Sai dai bayan da Lauyan gwamnati ya fito daga kotun, ’yan jarida sun tambaye shi dalilin dagewan, sai ya ce masu mataimakin Shugaban kasa ne zai zo Kaduna a ranar, ba Shugabankasar da kansa ba.

Ranar 7/11/2018 aka koma kotu da su Shaikh Zakzaky don yin batu a kan yiwuwar ba da beli. Sai dai a ranar Alkalin ya hana belin, bisa hujjar cewa bai gamsu da cewa su Shaikh Zakzaky ba su da lafiya ba, saboda ba a kawo gamsasshiyyar takarda daga Asibitin gwamnati ko wacce Hukumar lafiya ta amincewa a kan rashin lafiyar su Shaikh Zakzaky din ba.

Ya kuma amince da abin da Lauyan gwamnati ya gabatar, na cewa in har aka ba da belin Shaikh Zakzaky ba lallai ne in yana waje ya kawo kansa kotun ba. Don haka sai Mai Shari’a Kurada ya kori batun belin. Ko da aka zo batun ranar da za a dawo kotu, sai Shaikh Zakzaky ya ce masu in sun so su kai ta watan Maris, 2019, wato bayan an gama zaben Shugaban kasa da na Gwamnoni.

Sai dai Alkalin ya sanya 22/1/2019 a matsayin ranar da za a dawo kotu. A wannan ranar ne kuma Falana SAN da kansa ya samu halartar kotun, inda ya yi ma kotu cikakken bayani a kan rashin lafiyar da Shaikh Zakzaky ke fama da shi, ya kuma tabbatarwa da kotun cewa gwamnati ba ta da niyyar bai wa Shaikh Zakzaky kulawa, ya kuma nemi kotun ta ba da izini a fitar da Shaikh Zakzaky kasar waje don ya nemi lafiyarsa da kansa.

A nan sai Lauyan gwamnatin Kaduna, Bayero Dari ya musanta ikirarin Falana SAN, inda ya ce tuntuni har kasar waje gwamnati ta fitar da su Shaikh Zakzaky don nema masu lafiya, don haka ya nemi kotu ta yi watsi da maganar Falana.

A nan Shaikh Zakzaky ya lauyan na gwamnati wa’azi da cewa ya ji tsoron Allah ya guji yin karya, musamman ma a gaban kotu. Tabbas ba inda aka fitar da Shaikh Zakzaky tun da aka kama shi.

Sannan sai Alkalin ya bukaci Shaikh Zakzaky ya zo da Likitocinsa don su duba shi, kuma a yayin zuwan su su ma DSS su zo da nasu, kuma su jami’an tsaron DSS su kyale Likitocin na Shaikh Zakzaky wanda za su zo daga kasar waje ko daga nan gida Nijeriya su duba shi. Ya kuma dage ci gaba da Shari’ar zuwa ranar 25/3/2019.


Shekaru 3 Da Kisan-kiyashin Zariya (9)


Daga Saifullahi M. Kabir

KAFIN DAWO DA SHAIKH ZAKZAKY KADUNA

Tun bayan da kotu ta yi umurnin a saki Shaikh Zakzaky a ranar 2 ga Disambar 2016, inda kotun ta ba da umurnin a saki Shaikh din da mai]akinsa, a cikin kasa da kwanaki 45, kuma a biya su diyyar Naira miliyan 50, tare da gina masu gida a duk Jihar da suka zaba a cikin Jihohin Arewacin Nijeriya, mako guda bayan wannan hukuncin na Kotu, a ranar Juma’a 9/12/2016, kwatsam sai DSS suka je gidan da suke tsare da Shaikh Zakzaky a cikin garin Abuja suna kokarin canza masa wajen da za su ci gaba da tsare shi.

A yayin wayarsa da wasu daga iyalansa a lokacin, Shaikh Zakzaky ya ba da labarin yadda wasu jami’an tsaron suka zo suna kokarin sai sun tashe su a gidan, kan cewa za su komar da su wani gida daban. Sai dai a yayin da suka zo, sam ba su nuna cewa za su canza wajen tsarewa ba ne, sun ce ne ana so ai ma wannan gidan kwaskwarima.

Shaikh Zakzaky ya ce masu; “Ku da kotu ta ce ku sake mu, me zai sa ku zo ku ce za ku canza mana wajen tsarewa? Kuma in ma da gaske za a yi gyara ne, ko fenti a nan gidan, ai ana iya yi muna cikin gidan, illa iyaka ai ma wani bangare, in ya bushe sai mu koma can a sake wa wani bangaren.” Amma dai sai suka dage a kan lallai suna so sai an kwashe kayan su Shaikh din, tare da su an mai da su wani waje saboda nan za a yi gyara.

A ranar Juma’a kwashe kaya da dauke Shaikh Zakzaky bai yiwu ba, sai a ranar Asabar suka kuma dawowa da Yamma a kan cewa lallai DSS DG Lawal Daura ne ya ce, a kwashe kayan a komar da su Malam Zakzaky wani wajen daban, don ci gaba da tsarewa.

Bayan Isha, a wannan daren Asabar 10/12/16 din kuwa, sai suka sake dawowa dauke da bindigogi suka kewaye gidan, sun zo da katuwar mota don kwashe kaya, suka rika hauka, har suka kwashi wasu karikitai suka yi gaba da su.

Dama a wannan lokacin akan ba Shaikh Zakzaky waya duk ranar Asabar da Talata da daddare don su yi waya da danginsu. Amma a wannan ranar, sai suka hana su waya din, sai daga baya aka ba da, inda su Malam suka labarta wa iyalansu, kuma ta sanadin hakan ne ma ’yan’uwa suka san halin da ake ciki, wanda aka rika Muzaharori tun a wannan daren, ba kawai a Nijeriya ba, har a birnin London.

Ranar Lahadi 11/12/16, sai DSS suka aminta Jagora ya tura ’ya’yansa da suke tare da shi su gyara wajen da za a mai da su din. Don haka suka je suka ga wajen suka tsaftace shi, sannan a ranar 12/12/16, shekara daya cif da waki’ar Zariya aka dauke su Shaikh Zakzaky daga inda ake tsare da su a cikin garin Abuja, aka komar da su unguwar jami’an tsaro don ci gaba da tsarewa.

Shaikh Zakzaky da mai]akinsa, Malama Zeenat sun ci gaba da zama a wannan sabon wajen tsarewar har tsawon watanni 17, wato tun daga 12/12/2016 har zuwa ranar 15/5/2018, inda aka dauke su daga Abuja, aka kai su kotu a Kaduna da bakin bindiga.



SHIRYE-SHIRYEN MAIDO DA SHAIKH ZAKZAKY KADUNA

Wani abu tabbatacce shi ne, duk lokacin da ’yan’uwa almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky suka yi wani gagarumin motsi (Muzahara), musamman a birnin Tarayya Abuja na kiran a saki Shaikh din daga haramtacciyar tsarewar da ake masa, jami’an tsaro sun auka musu, ko ba su auka ba, za ka ga wata natija ya biyo bayan hakan.

Wannan a fili yake, mun gani a can baya, yadda suka fito suka nuna Shaikh Zakzaky a TV, yana magana da ’yan jarida, bayan da ’yan’uwa suka kwashe mako guda suna Muzaharori, ana bu]e masu wuta, amma ba su takaita ba a farkon shekarar 2018.

Wasu muhimman abubuwa sun auku a watan Afrilun 2018, wanda ya fara da gagarumar Muzahara da ta gudana a ranar Laraba 11/4/16, inda aka yini a gaban kofar Majalisar Tarayyar Nijeriya, washegari Alhamis kuma aka gudanar da taron tunawa da Shahidan Gwagwarmayar Musulunci, wanda shi ne mafi girman taro da ya gudana a Abuja a lokacin, bayan kammala shi aka yi Muzahara wacce aka rufe ta a gaban ofishin Shari’a na Nijeriya.

Tun daga wannan ranar ne jami’an tsaro, da suka ha]a da ’yan sanda da kuma sojojin da ke tsaron fadar Shugaban kasa (Guards Brigade), suka mamaye filin ‘Unity Fountain’ dauke da muggan makamai, suka dakatar da zaman dirshan din da aka faro tsawon kusan watanni uku, tare da hana duk wani taro a wannan muhallin.

Makon da ya biyo baya, ranar Litinin 16/4/2018, ’yan’uwa suka sake cincirindo suka gudanar da Muzaharar kira a saki Shaikh Zakzaky, inda suka je ofishin Hukumar kare hakkin dan’adam da ke Abuja, sai dai a gaban Hukumar ’yan sanda suka bude wa ’yan’uwa wuta, suka raunata da dama, suka kama fiye da mutum 100, har aka samu Shahidi guda daya; Ahmad Rufa’i Bauchi.

Mutane da kungiyoyi sun ta Allah-wadai da wannan abin, don haka ga alama ita gwamnatin ba ta ji dadin hujumin da duniya ta yi mata na tofin-Allah-tsinen ba, sai kawai kwana biyu bayan nan, a ranar Laraba 18/4/18 gwamnatin Kaduna ta gaggauta shigar da kara a wata babbar kotu a Kaduna, inda take zargin Shaikh Zakzaky, Malama Zeenah da wasu mutum biyu; Malam Yakubu Yahya da Malam Sunusi Abdulkadir da laifuka guda takwas.

Sai dai kuma gwamnatin ba ta bayyana shigar da karar ba a wannan lokacin sai daga baya. A ranar 27/4/2018, Shaikh Zakzaky ya yi waya da babban dansa; Sayyid Muhammad, inda ya ba da labarin yadda Shugaban DSS na lokacin, Lawal Daura ya gana da shi, da kuma abubuwan da suka tattauna.

TATTAUNAWAR SHAIKH ZAKZAKY DA LAWAL DAURA

Shaikh Zakzaky ya labarta cewa a ranar Laraba 25/4/2018 an sanar da shi cewa washegari za su gana da Lawal Daura, don haka ranar Alhamis 26/4/18 tun da sassafe aka dauke su aka kai su muhallin da za su yi ganawar, amma shiru, har zuwa Magriban wannan yinin Lawal Daura bai zo ba. Sai bayan hakan ya zo, ya rika nuna masu isa. Daga karshe ya ce ba zai yiwu a yi ganin a wannan ranar ba, sai dai gobe a komo. Aka mai da su Shaikh inda suke tsare.

Washegari Juma’a aka dawo da su Malam, nan ma Lawal Daura ya kara bata lokaci, sai can da yamma ya zo. A nan ma ya so ya kara dage zaman, amma sai su Malam (H) suka ce ba za su sake zuwa wajen ba in har bai yi maganar da zai yi a lokacin ba. Don haka sai ya yi maganganunsa masu cike da izgili, nuna isa da rainin wayo.

Idan mai karatu ya nemi ‘audio’ din wayar da Shaikh Zakzaky ya yi da Sayyid Muhammad a lokacin, ko kuma ya nemi littafin da Cibiyar wallafa da yada ayyukan Shaikh Zakzaky ta wallafa mai suna ‘Yunkurin kashe Shaikh Zakzaky a tsawon shekaru 10’, zai ga cikakken labarin abin da ya gudana tsakanin Lawal Daura da Shaikh Zakzaky.

Dama kwana biyu kafin zuwan Lawal Daura, Yariman Saudiyya, MBS, ya yi magana, inda ya yi ikirarin da hannunsu a yi wa Shaikh Zakzaky abin da aka masa na yunkurin kawo karshensa da da’awarsa. Don haka a lokacin Shaikh Zakzaky ya fada wa Lawal Daura cewa: “Ka je ka gaya wa wanda ya ba ka ajiyarmu, ya kammala ladansa, in ya dauka kashe mu lada ne, tunda ya kashe mutum sama da dubu, to ya ha]a da mu. Ka ce masa ni da matata a shirye muke, mun shirya mutuwa, saboda haka Bismillah!”

Lawal Daura ya tambayi Shaikh Zakzaky, yanzu idan aka sake shi me zai yi? Ya ce wa Shaikh din. “Saboda akwai wasu masu wani ‘interest’ daban, in ya so sai a fasa wannan.” Sai dai bai fa]i mene ne wannan din da za a fasa din ba, kuma Shaikh Zakzaky bai tambaye shi ko mene ne ba.

Shaikh Zakzaky ya ce masa, zai ci gaba da abin da yake yi ne. “Da can me nake yi? Makamaina tun a da sune ilimi, da hankali da hikima. Kuna so na fita na sa jahilci ne da wauta da hauka? Me kake so na yi? Da can me nake yi wanda yanzu in na fita zan canza? Sai dai in kuna so in na fita zan yi hauka ke nan. Ko kuma ya zama ba ilimi zan sa ba, ko zan dauki makami. Na ce makami na shi ne ilimi da hankali. To sai dai in zan dauki kuma wani makamin ne daban,” in ji Malam Zakzaky.

A nan ne Lawal Daura ya ce wa Shaikh Zakzaky; “Malam na fa san ka tun kana yaro!” Malam ya ce masa; “Tun ina yaro? Ko tun muna yara? Ina ce a 1953 aka haife ka?” Lawal Daura ya ce; “Eh, a watan Agustan 1953.” Sai Malam Zakzaky ya ce masa; “Ni kuma an haife ni a watan Mayun 1953.” Nan Lawal Daura ya ce wa Shaikh Zakzaky; “Eh ka girme ni da watanni uku. To, shi ke nan tun muna yara.”

Nan Shaikh Zakzaky ya ce masa; “To, abin da ka san ni tuntuni dai ina yi, shi nake kai har yanzu. Shekarana 40 ina yi, shi ne kuma nake yi, a kansa kuma nake. Don haka in na fita abin da nake yi tun shekaru 40, shi zan ci gaba da yi.”

A nan Lawal Daura ya samu amsar daga alama ba ita ya so samu daga Shaikh Zakzaky ba. Ya ga cewa tunda Shaikh Zakzaky ya tabbatar masa da cewa zai ci gaba da abin da ya saba ne, bai da alamar fasawa, don haka yanzu ba za a fasa wannan din da yace in ya so sai a fasa shi ba. Wannan din kuwa shi ne kai Shaikh Zakzaky kotu, wanda suka riga suka shigar da kara tun kafin zuwan nasu.

Za mu cigaba.