January 07, 2017

DARAJOJIN IMAM ALI (AS) DAGA BAKIN UMAR DAN KHADDABI (R)


An ruwaito a cikin littafin Riyadun-Nadarat, jildi 2, shafi 226 daga Umar ‘Dan Khaddabi yana cewa: Na shaida cewa naji Manzon Allah (S) yana cewa: “Da ace sammai bakwai da kassai bakwai zasu kasance a gefe daya, shi kuma Imanin Ali ‘Dan Abidalib a aje shi a gefe daya, da Imanin Ali ya rinjaye sammai bakwai da kassai bakwai da abin da ke cikinsu”.

An kuma samu a littafin Yunabi’ul-Muwadda, shafi 249 Daga Umar dan Khaddabi, ya daukaka shi daga Manzon Allah (S) yace: “Da ace dukkan tekuna tawadda ne, kuma itace alkaluma ne, mutane kuma marubuta ne, aljanu masu tattarawa ne, ba zasu iya kiyaye dukkan darajojinka ba ya kai Baban Hasan (Ali)”. 

Muhibbud-Dabariy as-Shafi’iy ya kawo a littafinsa ‘Zaka’iru-Ukba’ shafi na 89 daga Umar ‘Dan Khaddabi yace, Naji Manzon Allah (S) yana cewa Ali (AS); “Ya kai Ali, hannunka da nawa zamu shiga (Aljanna) tare ta inda na shiga a ranar Alkiyama”.

A cikin littafin ‘Kaukabud-Durriy’ shafi na 125, daga Umar ‘Dan Kaddabi yace, Manzon Allah (S) yace: “Duk wanda ya ke sonka ya Ali, ya kasance tare da Annabawa a darajarsu a ranar Alkiyama, kuma duk wanda ya mutu da kinka, ya so ya mace a Bayahude ko Banasare!”.

A wani hadisi mai kama da wannan da Muattakal-Hindiy ya kawo a littafinsa ‘Kanzul-ummal’ jildi 6, shafi 154, yace ya nakalto daga littafin ‘Majma’ul Kabir’ na Dabari, da ‘Tarikhul Kabir’ na Ibn Asakir, da isnadinsu daga Manzon Allah (S) yace: “Na yi ma duk wanda ya yi Imani da ni kuma ya gasgata ni wasiyya da riko da Wilayar Ali ‘Dan Abidalib. Duk wanda ya bi shi ni yabi, duk wanda ya bi ne ya bi Allah. Duk wanda yake son shi ni yake so, duk wanda yake so na ya so Allah. Wanda kuwa ya fusata shi ni ya fusata, kuma wanda ya fusata ni ya fusata Allah Mai Girma da Daukaka”.

A cikin littafin ‘Sawa’iku Muhri’ka’ shafi 109, daga Umar dan Khaddabi yana cewa: “…Ku sani, daukaka bata cika face da wilayar Ali (AS)”.

Sayyid Muhammad Salih at-Tirmizi (Bahanafe) ya kawo littafinsa ‘Kaukabud-Durriy’ shafi na 134, daga Umar ‘Dan Khaddabi yace; Yayin da Manzon Allah (S) ya kulla alaka tsakanin Sahabbansa, sai ya dubi Ali (AS) yace: “Wannan (Ali) ‘dan’uwa na ne a Duniya da Lahira, kuma Halifa na ne a cikin iyalaina, kuma wasiyi na ne a cikin al’ummata, kuma shi ne magajin ilimi na, kuma shine magabaci a addini na (Musulunci), duk abin da yake gare shi daga ni yake, amfaninsa amfanina ne, cutuwarsa cutuwata ne, duk wanda yake son sa hakika yana so na, kuma wanda ya fusata shi hakika ni ya fusata”. 

A ‘Riyadun Nadarat’ jildi na 2, shafi na 163, an ruwaito daga Umar dan Khaddabi, cewa, wata rana Umar ya ji wani mutum yana zagin Imam Ali (AS). Sai Umar yace masa; Amma ni ban yi zaton cewa kai kana daga cikin Munafukai ba! Domin naji Manzon Allah (S) ya ce ma Ali (AS): “Kai Matsayinka a wajana kamatr matsayin Haruna ne a wajen Annabi Musa, sai dai ni babu Annabi a bayana.”

Saifullahi M Kabir 

Wacce Nake Son Aura

Kyakkyawa ce kyau mara misaltuwa, wajen hali, sakamakon irin tarbiyar da ta samu a gidansu daga mahaifanta guda biyu. Ko ba komai, mahaifinta wani mutum ne ma’abocin addini, mai riko da koyarwar tsarkakan bayi, daidai gwargwado ya karantu, dan haka ya kasance mai aiki da abin da ya karanta. Kai in takaice muku, shi mahaifin nata irin mutanen nan ne da matansu suke musu kirari ta hanyar ce musu ‘Mazajen goyo da majanyi!’

Ka san kuwa idan har mata, wadanda aka sansu da yi wa maza kirari da cewa “Namiji ba dan goyo bane” sai ka ji wata tana cire nata mijin ta hanyar cewa shi ‘Namijin goyo da majanyi’ ne ma, kun san lallai namijin nan irin mazan nan ne da suka debi soyayyar tsakani ga Allah tun ana yarinta, har gashi ‘yarsu ta tasa ta isa aure, har ma ta sameni a matsayin saurayi, amma wancan soyayyar tasu (iyayen) na nan a matsayin budurwa, duk kuwa da tsufan da suka yi bayan tasawar kyakkyawar yarinyarsu.

A zahiri, na iya shaida cewa mahaifin wannan wacce nake so din, irin mazan nan ne da Annabi (S) yace: “Mafiya alkairin mutane daga cikin al’ummata sune wadanda ba su tsawwalawa iyalansu, kuma ba su zaluntarsu.” Saboda a iya bincikena ban taba jin ko a labarum tsegumi irin na matan gidan biki, ko kuma na mazan dandali, cewa sun taba samun sabani da matar tasa wacce yake matsanancin sonta kamar yadda take sonsa ba.

Ita ma mahaifiyar matar da nake son aura, irin wannan matan ne da Manzon Allah (S) yake cewa: “yana daga cikin dacen mutum ya samu mace managarciya.” Haka ma Amirulmuminin Ali ‘Dan Abudalib (AS) yana cewa; “Mace tagari ta fi alkairi akan mutum dubu da ba nagargaru ba.” To da gasken-gaske bincikena ya nuna min cewa ita wannan mahaifiyar tana cikin wadannan mata na gargarun da Allah ya ma sirikina baiwa da ita. 

Kai, sarkuwar tawa fa a iyakan sanina, bata yarda ta kasance daga matan nan da za su rasa maceci a ranar Lahira ba, kamar yadda aka ruwaito daga Imam Muhammad al-Bakir (AS) yana cewa: “Babu wani maceci ga mace wanda zai tseratar da ita daga Ubangijinta face yardar mijinta (a gareta).” To sarkuwar tawa ta kasance tana iyakar yinta wajen ganin ta samu yardar Allah da ta hanyar samun yardar mijinta. 

Lokaci bayan lokaci za ku ji Sarkuwata ta tara ‘yan matanta da take shirin ta aurar da su, wadanda babba a cikinsu itace wacce nake son a bani na aura, tana basu labarin cewa; “Yayin da Sayyida Fatima ta yi Shahada, mijinta, Amirulmuminin (AS) ya tsaya a kanta, yana mai cewa; ‘Ya Allah! Ni mai yarda ne da ‘yar Annabinka. Ya Ubangiji, hakika ta sauke min hakkina da ke kanta.” Sai take fadawa ‘ya’yan nata cewa wannan shaidar nake so daga mahaifinku nima, ku dage idan kun yi aure ku kasance masu neman wannan shaidar daga mazajenku.

Hakika na samu ‘yar manyan mutane, ‘yar mutunci da arziki. Ba fa arzikin kudi ba, domin kuwa Mahaifin nata ba shi da wani tarin abin Duniya, face dai Allah ya masa rufin asiri. Wannan ne ma yasa take yawan cemin, ta amince na aureta da rufin asiri na, in Allah ya nufi mu yi dukiya Shi ya so. Idan bai nufa ba kuwa arzikin da ya mana abin godewa ne. 



Ina tsananin kaunar wannan budurwar tawa saboda na taba tambayarta a wani lokaci muna ‘chat’, nace mata mene ne labari? Sai ta bani labarin wata mata da tazo tana tambayar Annabi (S) akan hakkokin miji da ke kan matarsa, sai yake ce mata: “Ta biya masa bukatarsa ko da tana cikin uzuri (lokacin da ya neman), kuma kar ta gabatar da wani abu face da izininsa, idan ta aikata ba tare da amincewarsa ba tana da dakon aikin, shi kuma yana da ladansa (aikin da ta yin mai kyau), kuma kar ta yi bacci da daddare matukar yana mai fushi da ita.” A lokacin sai take cemin, “Ina son ka zama miji na, Allah ya bani ikon sauke dukkan hakkokinka da ke kaina ko na samu kyakkyawar sakamako a wajen Allah, Ya kai Uban ‘ya’yana.”

Na sha fada mata wani Hadisin Annabi (S) da yake cewa: “Duk wanda ya ke da wata mace wacce ta ke cutar da shi, Allah ba zai karbi sallarta ba, ba kuma zai karbi duk wani kyakkyawa daga ayyukanta ba ko da ta kare zamani tana azumi, har sai ta samu yardar mijinta.” Nake cewa, bani fatan ki kasance a sahun irin wadannan matan Ya ke matar aurena.

Ya ke abar kaunata, na roke ki da ki kasance min mafi alkairin jin dadi a rayuwata. Domin na ji a hadisi Manzon Allah (S) yana cewa: “Mafi alkairin jin dadin duniya shine samun mace tagari.” Na yi miki alkawarin sauke duk hakkokinki da ke kaina bayan aurenmu gwargwadon iyawata, na daga kosar da dukkan nau’in yunwarki, tufatar da ke, ilmantarwa da kuma biyan bukatunki. Ko ba komai naga wani hadisi a cikin ‘Mizanul Hikma’ daga Manzon Allah (S) yana cewa: “Hakkin mace ne akan mijinta ya kosar mata da yunwarta, ya suturce mata al’auranta.”

Zan kuma yi kokarin zama a gareki kamar yadda Annabi (S) yake cewa: “Mafiya alkairin mutane daga cikin al’ummata sune wadanda ba su tsawwalawa iyalansu, kuma ba su zaluntarsu.” Zan yi matukar burin na tsinci kaina daga cikin wadanda Annabi (S) yake cewa: “Babu wani bawa da zai fita ya nemo abinci, sannan ya zo ya ciyar da iyalansa, face Allah ya ribanya masa a kan dukkan dirhami daya da ya ciyar da su zuwa dirhami dari bakwai.”

Ya ke abar kaunata, ina mai alfahari da zamarki Budurwata. Zan ji dadi fiye da na yanzu bayan an daura aurenmu. Fatanmu shine Allah ya bamu zuriya masu albarka, tsayayyu a tafarkin Allah, masu sallamawa ga Jagora, wakilai na gari ga addinin Allah da sakonSa.

Tunatarwa ce kawai... 

 - Saifullahi M. Kabir
 10/10/2016 

MUNA TIR DA TAKE-TAKEN GWAMNATIN TARAYYAR NA KIN BIN UMURNIN KOTU KAN SAKIN SHAIKH ZAKZAKY

TAKARDAR MANEMA LABARAI

Muna tir da take-taken gwamnatin Tarayyar na kin bin umurnin kotu kan sakin Shaikh Zakzaky

Yayin da yake mai da martani ga hirar Shugaban Dandalin yada labaranmu da sashen Hausa na BBC, Kakakin fadar Shugaban kasa a kan harkar yada labarai, Garba Shehu a ran Litinin 02/01/17 ya yi wasu kalamai masu nuna take-taken Gwamnatin Tarayya na kin bin umurnin hukuncin da babbar kotun Abuja ta 6 ta yanke na a saki Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky a cikin kwanaki Arbain da biyar daga ranar da aka yanke hukuncin. Ya bayyana cewa wadansu mutane sun daukaka kara a kan hukuncin da babbar Kotun Abujar ta yanke ba tare kuma da ya ambata ko su wane ne su ba. Ya kuma ambata cewa wasu dalilai na tsaron kasa da bai bayyana takamaimai ko wadanne nen ba su ke sa ake ci gaba da tsare Shehin Malamin ba bisa kaida ba. Haka nan kuma ya nisanta Shugaban kasa a kan hannun da yake da shi cikin lamarin, a inda ya bayyana cewa lamari ne wanda ya shafi gwamnatin Jihar Kaduna.

Wannan ba shi ne karon farko ba wanda mai taimaka wa Shugaban kasa a kan harkar yada labarai ya yi kokarin nisanta hannun Shugaban kasa a kan lamarin Kisan Kiyashin da aka kaddamar a garin Zariya. Amma alal hakika babu wata hujja da za ta iya wanke Shugaban daga hannun da yake da shi a kan tsararrun hare-hare na taaddanci da ake kai wa yan uwa Musulmi na Harkar Musulunci a Najeriya a cikin daukacin kasar ta tarayyar Najeriya. Tsakanin rundunar Sojojin Nijeriya da suka fara kaddamar da kisan kiyashi a garin Zariya da kuma Hukumar Jamian tsaro na farin kaya (DSS) wadda ke tsare da Shaikh Zakzaky ba bisa kaida ba, ba  wacce take Hukumar gwamnatin Jihar Kaduna. Shugaban Kasa dai shi ne babban Kwamandan askarawan Sojojin Najeriya kuma babban Jamiin tsaro na kasa baki daya. Sai ga shi ya kasa daukar mataki a kan wadanda suka yi fatali da dokokin kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya gabansu gadi, ta hanyar kashe yan kasa fararen hula wadanda ba su dauke da makami tare kuma da yi wa gawawwakinsu kabari na bai daya, kamar yadda rahoton hukumar binciken kisan kiyashin Zariya (JCI) ya tabbatar. Kasantuwar Shugaban Kasa ya kasa ko da yi wa dangin wadanda aka kashe taaziyyar jajen rashin yan uwansu da suka yi, ko kuma nuna tausaya wa ga wadanda aka jikkata a yayin harin, ko da kuwa a bayan da hukumar bincike ta (JCI) ta fitar da rahoton da ya tabbatar da kisan daruruwan yan kasa fararen hula da jamian tsaro Sojoji suka yi, alhali kuma shi ne babban kwamandan askarawa, ba zai iya tsame hannunsa a cikin wannan taannuti ba.

Dadin dadawa kuma, Mai taimaka wa Shugaban kasa sai ya nuna jahilcin cewa Antoni-janar na tarayyar Najeriya, wanda yana cikin wadanda ake kara kan tabbatar da hakkin Shaikh Zakzaky, Ministan Tarayya ne da ke wakiltar Shugaban kasa a cikin wannan kara. Haka nan kuma, irin girma da fadin hare-haren taaddancin da ake kaddamarwa a kan yan uwa Musulmi na Harkar Musulunci a Najeriya (IMN), ai bai tsaya a iya cikin Jihar Kaduna ba, amma wani tsararren shiri ne da wasu jihohi suke taimakawa a sarari wajen aiwatarwa. Salon harin taaddancin da aka yi amfani da shi a Kano, Jos, Sakkwato, Funtuwa da kuma Kaduna ai ba lamari ba ne wanda ya shafi jihar Kaduna ita kadai ba, kamar yadda Garba Shehu ya yi ikirari. Don haka a sani lallai ba za a yaudare mu da shirun da gwamnatin tarayya ta yi ba a kan wannan lamari na tsawon sama da shekara guda.



Mai taimaka wa Shugaban kasar ya yi kuma kokarin danganta tsare Shaikh Zakzaky da batun da ya shafi wasu zarge-zarge marasa tushe na tsaro. Wanda kuma dama wannan dalilin shi ne wanda mahukunta suke bayyanawa a duk lokacin da ruwa ya karewa dan kada. Ta yaya ne bin umurnin kotu na sakin wanda aka tsare a boye na tsawon sama da shekara guda zai iya zama barazana ga shaanin tsaro? Mun yi amannar cewa babu wani batu na shaanin barazana ta tsaro da zai sanya a ci gaba da tauye wa Shaikh Zakzaky yancinsa. Hukumomi sun kasa aza wani laifi a kan Shaikh Zakzaky da iyalinsa a tsawon shekara guda da ya yi a tsare.

Da yake bayyana dalilin da ya sanya ba su bi ba, kuma ta yiwu ba za su bi umurnin kotun ba, ya ce wasu mutane sun daukaka kara a kan hukuncin, amma kuma ya kasa bayyana su waye su kuma bisa wane dalili. Abin sani dai a nan shi ne, mujarradin daukaka kara kawai ba zai iya dakatar da zartar da umurnin waccan kotun ba, sai dai kawai idan wata babbar kotu ce ta bayar da umarni a kan haka. Haka nan kuma bai iya bayyana wani umurni da aka fitar ba wanda ya ci karo da wannan hukunci na sakin Shaikh Zakzaky da Kotu ta bayar ba, duk kuwa da cewa waadin sakinsa na kara kusantowa. A sarari yake cewa gwamnatin dai tana so ta yi wasa da hankalin jamaa ne kawai.

Mun yi amannar cewa maimakon hakan, fadar Shugaban Kasa tana bukatar ta bi umurnin kotu na a gaggauta sakin Jagoranmu, Shaikh Ibraheem Zakzaky a matakin farko, maimakon musanta hannun da tabbas tana da shi a cikin lamarin kisan kiyashin da aka kaddamar a garin Zariya, ko fitar da wasu damuwa na ba gaira ba sabat kan shaanin tsaro. A dai yi mu gani, domin kuwa al'umman duniya suna ji kuma suna gani.

SA HANNU:
IBRAHIM MUSA
SHUGABAN DANDALIN YADA LABARAI NA HARKAR MUSULUNCI A NAJERIYA
07/01/2017
Skype: Ibrahim Musa42
Fassara daga Zaharaddeen Sani Malumfashi

January 06, 2017

Ranar 8 Ga Rabi'ul Akhir;

Ranar 8 ga watan Rabi'ul Akhir, a shekara ta 232 aka haifi Mahaifin Limaman Zamaninmu, Tsarkakakke Imam Hasanul Askari (AS). 

A irin wannan ranar ta 8 ga Rabi'ul Akhir, ina taya Maulana Sahibul Asr Waz Zaman, Imam Mahdi (AJ) murnar zagayowar wannan ranar ta farin ciki. Haka ma ina taya dukkan Ahlulbaiti da jikokinsu Shurafa tare da daukacin masoya masu karimci murnar wannan rana mai albarka. 

Dafatan za a gudanar da ayyukan alkairi Don tuna wannan rana ta haihuwar daya daga cikin Imamai Ma'asumai Tsarkaka. 


Saifullah M Kabir