Annabi Haruna (AS) shine dan’uwan Annabi Musa (AS) a jini, kuma abokin isar da da’awarsa (sakon Allah (T) izuwa ga Fir’auna ma’abocin girman kai da ‘Dagawa. Ance Annabi Haruna (AS) ya kasance mai hikima wajen isar da magana.
Annabi Musa (AS) ya sanya Annabi Haruna (AS) a matsayin halifansa a cikin mutanensa a yayin da zai je saduwa (ganawa) da Allah (T) a kan dutsen da ake kira “Jabalu Duur”. Sai ya zama bayan tafiyar Annabi Musa, wani Shaidani da ake kira Samiriyyu daga cikin mutanen Bani Isra’ila ya yaudari al’ummar Annabi Musa (AS) ta hanyar kawo musu ‘Dan-maraki (Ijil) da bayyana musu shi (Ijil) a matsayin shine Ubangijin hatta ma shi Musa (AS) din. Sai ya zamana al’ummar da Annabi Musa ya bar ma dan’uwansa Haruna (AS) lura da su, suka bijire ma bin Annabi Haruna, suka zabar ma kansu bin Samiriyyu tare da bautan wannan Marakin da Samiri ya kawo musu.
Ance hatta da Annabi Haruna ya matsa musu da wa’azi a kokarinsa na tunatar da su addinin Allah wanda Musa ya tafi ya bar musu, tare da cewa shine Halifan Musa (AS) din, amma sai suka nufi su kashe shi. Har ma suka masa kasheji akan cewa in har ka matsa mana zamu kashe ka.
Iri daya da abin da ya faru da wannan al’ummar ta Manzon Allah Muhammad (S); yayin da ya yi SHAHADA, ya riski Ubangijinsa yana Yardajje abin yarda, alhali ya nasabta ma al’ummarsa Shugaba Ali Dan Abidalib (AS) a matsayin halifansa a bayansa. Amma sai suka bijire a bayan baya nan, suka ki subi Imam Ali (AS) din. Sai ya zama Samiriyyun wannan al’ummar ya kawo Maraqin wannan al’ummar yace shi za’a bi, ya kasantar da shi a matsayin halifan Annabi akan wannan al’ummar. Har ya kasance sun ma Imam Ali (AS) barazanar kisa, ta yadda da ya ja musu a lokacin da sun nufi su kashe shi.
Na’am, shi Annabi Musa (AS) ya bar Annabi Haruna (AS) ne a matsayin halifansa a cikin mutanensa kafin yaje ya gana da Allah (T) na tsawon kwanaki arba’in kawai ya dawo. Amma suka iya juya ma addininsa baya suka bijire ma halifan da ya bar musu, suka zabi wanda ransu yaso suka bishi. Tare da cewa sun san cewa fa Annabi Musa ba ya mutu bane, sun san zai dawo, amma kunga sun iya bijirema Haruna (AS), har ta kai ma ga suna masa barazanar kisa ma. To, me kake ma mamakin dangane da al’ummar Annabi Muhammad (S) da suka juya ma halifansa baya, suka zabi Maraqi bisa irshadin Samiriyyu, alhali suna da tabbacin Manzon Allah (S) ya riga ya koma ga Allah ba dawowa zai ba?
Shi fa Samiri din sahabin Annabi Musa ne babba, kun ga yadda ya batar da al’ummar Musa, ya hanasu subi Haruna ya kawo musu Ijil yace shi za su ma biyayya, to ya zai zama maka abin mamaki dan Samirin wannan al’ummar ya hana al’ummar subi Wasiyin Annabi ya kawo musu Ijil din wannan al’ummar yace shi zasu bi?
Kar kayi mamaki; domin su al’ummar Annabi Musa (AS) an kawo musu Maraqi ne suka bi a matsayin Ubangiji bayan gashi suna ganinsa fa dabba ne. Su kuwa al’ummar Muhammad (S) mutum ne Samirinsu, kuma ya kawo musu Mutum ne a matsayin Ijil dinsu suka bi a matsayin halifan Manzon Allah (S). Kaga idan ma abin mamaki da al’ajabin yiwuwar hakan ne, to kayi mamakin na wancan al’ummar da aka bar ma Haruna (AS) halifancinta ne, ba na Ali Dan Abidalib (AS) ba.
Ina taya al’ummar Duniya baki daya jajen zagayowar ranar da Annabi Haruna (AS) ya koma ga Allah (T). Dafatan wannan ranar zata kasance abin tunawar al’umma a duk lokacin da ta zagayo don daukaka ambaton wannan Annabi na Allah kuma Khalifan da Sahabban Annabinsa suka zalunce shi, suka ki su bishi, kuma suka nufi kashe shi.
— Saifullahi M Kabir
Muhdsaifu@gmail.com
12 Safar, 1438 (12/11/2016)
No comments:
Post a Comment