Wannan bawan Allah mai girma, Jagoran Harkar Musulunci a Nigeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky, an haife shi ne a ranar Talata 15 ga Sha’aban shekarar 1372 Hijiriyya, wato yanzu haka ya cika shekaru 65 daidai da haihuwa. A Miladiyyah kuwa haihuwar ta kasance ranar 5 May, 1953. A wannan lissafin zai zama shekarunsa 63 da watanni a yanzu.
Sunansa Ibraheem, ana masa lakabi da AlZakzaky, Kuma Shaikh Usman Danfodiye ya masa lakabi da Sharafuddeen da kuma Ibraheemul Magribiy (Kariyar Allah su kara wanzuwa a gareshi).
Sunan mahaifin Shaikh Ibraheem Zakzaky shine Yaqoub, kakansa kuwa sunansa Ali dan Malam Tajuddeen, shi kuma dan wani babban limami da ake kiransa da Liman Husaini. Dan haka kakan Shaikh Zakzaky na uku ya kasance daga cikin mutanen Shaikh Usman Danfodiye, wadanda ya tura su garuruwa a matsayin wakilansa, sai ya kasance shi Malam Muhammad Tajuddeen Shaikh Danfodiye ya turo shi Lardin Zazzau ne a matsayin mai ba Amir din Zazzau, Malam Musa shawara da taimakonsa wajen tafiyar da harkokin al’umma akan tsarin Musulunci.
Ashe duk wani wanda zai zo da batun asali ya jingina wa kansa a matsayin shi dan Zazzau ne, to yana bayan su Shaikh Zakzaky ne! Domin kuwa kakansu ne suka kafa Mulkin Zariya, duk kuwa da cewa a wancan karon sun kafa Mulkin ne bisa nizamin Musulunci, a yanzu kuma ana tafi da ita bisa nizamin turawan yamma karkashin Kwansitushen.
Ta Mahaifi da Mahaifiya, Shaikh Ibraheem Zakzaky shi Bafullatani ne, kuma asalinsu mutanen kasar Mali ne. Sunan Mahaifiyar Shaikh Ibraheem Zakzaky Hajiya Salaha, ana kiranta da ‘Hari’ (Wanda yake suna ne da ake kiran wanda aka Haifa da damina a Fulatanci). Mahaifinta kuma shine Malam Muhammad Gidado dan Malam Abdulkadir, wanda asalinsa daga Fulanin Mali ne.
Mahaifin Shaikh Zakzaky, Malam Yaqoub ya rasu tun a shekarar 1972, kimanin shekaru 44 da suka wuce, a lokacin Shaikh Ibraheem Zakzaky yana dan shekara 19 a Duniya. Malam Yaqoub ya yi Shahada ne a wani Kududdufi (ruwa) a yayin da ya ga wata akuya ta fada za ta mutu sai ya yi kokarin ceto ranta. Ita kuwa Mahaifiyarsa ta rasu ne a watan Nuwambar 2014. Shaikh Ibraheem Zakzaky shine na biyar a cikin ‘ya’yan da Mahaifinsa ya Haifa su 16.
Abubuwa guda biyu da Shaikh Ibraheem Zakzaky ya tsayu da su tun tasowarsa har zuwa zamansa matashi sune karatu da zuwa gona. Dabi’ar mahaifinsu Shaikh Zakzaky shine baya fara tura dansa gona sai ya sauke Alkur’ani mai girma. Idan kuma ka yi dubi da cewa mahaifin su Shaikh Zakzaky ya yi Shahada ne a yayin Shaikh Zakzaky na da shekaru 19 a duniya, za ka iya fahimtar cewa Shaikh Zakzaky tun yana da kankanin shekaru ya sauke Alkur’ani, saukar gaske ba irin ta yanzu da akan yin a zu-zu ba!
“Duk wani littafi da ake karantawa a zaure na Mazhabar Malikiyya da na Sunnah da na Lugga, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya karance su a zaurukan Malamai tun yana karami.” Wannan ne shaidar da kanin Shaikh Zakzaky wanda suke uwa daya uba daya, Malam Badamasi Yaqoub ya ba da. Wanda za ka sha mamaki idan ka ji wani makiyin Shaikh Zakzaky yana jingina jahilci ko rashin karatu gareshi.
Cikin malaman Shaikh Ibraheem Zakzaky, baya ga mahaifinsa, wanda sun kasance shi da yayyinsa suna karatu a wajensa tun suna kanana, har ma babban wan su Shaikh Zakzaky, wanda yake shi Dan Izala ne, yake cewa: “Ibraheem ya kasance mai hazaka sosai.”, an tabatar da cewa hatta kannin Shaikh Zakzaky idan suka mance karatunsu shi yake tuna musu, tare da cewa bai kai inda suken ba. Amma dake yana jin sadda ake biya musu kafin a zo kansa, dan haka yakan rike nasa ya rike nashi.
Shaikh Zakzaky ya yi karatu a wata Shahararriyar makarantar allo da ke gidan Sarkin Ladanai, sannan kuma ya yi karatu a wajen Malamai daban-daban, daga cikinsu akwai Malam Sani Abdulkadir na Kwarbai, wanda Shaikh Zakzaky ya yi karatun Allo a wajensa da kuma karatun littafai musamman ma na koyon Larabci da Nahawunsa. Ya kuma yi karatun littatafai a wajen Malam Isa na madaka, Malam Sani Na’ibi da kuma Malam Ibrahim na kakaki da sauran Malamai daban daban, wanda an tabbatar da cewa babu wani Malami da ke ba da karatu a Zariya wanda Shaikh Zakzaky bai je zaurensa ya kwashi ilimi ba.
Tare da cewa Shaikh Zakzaky ya yi makarantun koyon Larabci, daya a Zariya, wacce a lokacin yana yinta, kuma yana koyarwa a makarantun Islamiyyu daban daban a unguwannin Kwarbai, Kakaki, Lemu da Rimin tsiwa. Sannan makaranta ta biyu da ya yi itace S.A.S (wato School for Arabic Study) a Kano, wanda Shaikh Zakzaky ya je dan ya karanta Arabiyya ne, amma sai suka masa tambaya da Turanci suka ji yana ta amsa musu da Turancin (Tare da cewa bai yi ko Firamari ba!) sai kawai suka bashi Grade-Two, bayan shekara 5 Shaikh ya ci jarabawar gama wannan makarantar, wacce hakan ta ba shi damar shiga Jami’ar Amadu Bello kai tsaye.
Kuma a lokacin da Shaikh Zakzaky ke yin wannan makarantar ta SAS a Kano, a tsawon wannan shekarun, ya rika amfani da damammakin da ya samu wajen zuwa zaurukan Malamai daban daban a garin Kano yana yin karatun littatafai. Misali, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya yi karatun littatafai gaba da gaba a wajen Shaikh Nasiru Kabara na tsawon shekaru. Ya kuma yi a wajen Shaikh Isa Waziri Kano, da wajen Malam Ibrahim Babarbare da Malam Nuhu Limamin masallacin Yola da ke cikin birnin Kano. Ya yi karatu a wajen Malam Datti Ahmad, Malam Abdulra’uf Usman (wani mutumin Misra) da sauran manyan Malamai masu yawan gaske.
Rayuwar Shaikh Zakzaky gaba daya ta kare ne a karatu da karantarwa, sai kuma gwagwarmayar yunkurin dawo da koyarwar addinin Musulunci da Shaihin ya sakama gaba, wanda hakan ya auku ne sakamakon yadda Shaikh Zakzaky ya ga lalacewar kasar nan ta kai makura tun yana jami’a ta yadda kwata-kwata, tare da cewa kasar nan Musulunci ya taba iko da ita a lokacin Shaikh Usman Dan Fodiye, amma sai aka wayi gari yanzu ba addini ke iko ba, face wani tsarin mulkin turawan yamma wanda suka yi hannun riga da Musulunci. Sai Shaikh Zakzaky ya daurawa kansa nauyin kira zuwa ga komawa tsarin Musulunci da yunkurin tabbatar da shari’ar Allah a doron kasa, tare da tarbiyantar da al’umma akan irin koyarwar Manzon Allah Muhammad (S).
Wannan ne yasa tun da Shaikh Ibraheem Zakzaky ya fara wannan kiran, a lokacin yana Jami’ar Amadu Bello Zariya (ABU) ya fara fuskantar barazanar kamu a kulle shi daga mahukuntan kasar Nigeriya, masu kare muradun turawan yamma. Ya zamana I zuwa yau da a yanzu haka Shaikh Zakzaky yana tsare, an kama shi ya fi sau goma, kuma ya shiga gidan kurkuku daban daban a fadin kasar nan. Na karshe kafin wannan shine na lokacin Sani Abacha wanda aka zargi Shaikh Zakzaky a kotu da cewa yace Babu Hukuma Sai Ta Allah!
Janibobin rayuwar Shaikh Zakzaky (H) suna da fadin gaske. Misali akwai labarai daban daban na gwagwarmayarsa a makaranta da alakarsa da sauran mutane. Akwai kuma labarin fara da’awarsa zuwa yau. Abubuwan da ya fuskanta na jarabawa musamman daga azzaluman mahukunta da kuma janibobi daban daban na rayuwarsa kamar aurensa, ‘ya’yansa da zamantakewarsa da sauransu. Wanda muna sa ran marubuta za su tattabo mana wasunsu a wannan daren.
- Saifullahi M Kabir
13 Sha’aban 1437 (20/50/2016)

No comments:
Post a Comment