Ya kasance mafi ibada a cikin gaba dayan mutanen zamaninsa. Babu wani wanda ya kai shi falala, daraja da matsayi tare da sallamawa cikakkiya ga Allah da ManzonSa (S) a lokacin rayuwarsa.
Imam Hasan (AS), wannan da shine babban jikan Manzon Allah Muhammad (S), kuma sanyin idaniyarsa, an ruwaito cewa duk lokacin da aka ambaci mutuwa ko kabari ko tashi bayan mutuwa ko tsayuwar Lahira akan ga hankalinsa ya tashi har ta kai ga yana zubar da hawayensa masu albarka.
Shine mai kaskantar da kai na hakika a duk lokacin da ya tsaya gaban Allah (T) da nufin yin Sallah. Kafin nan ma, an ruwaito cewa, duk lokacin da ya nufi yin Sallah akan ga fuskarsa ta sauya, jikinsa ya yi sanyi. An tambaye shi akan hakan, sai yace; Ya b azan fita hayyacina ba alhali zan tsaya gaba da Mahalicina?
Duk sanda aka ambaci Aljanna da Wuta, za ka ji Imam Hasan (AS) ya yi addu’ar cewa: “Allah ka azurtani da Aljannarka da falalarKa, ka kiyaye ni daga wutarka da afuwarKa.” Bai taba tsammani ko zaton cewa ya aikatawa Allah abin da ya kai ya bashi Aljanna ba idan bad a falala da afuwar Allah (T) ba.
Shine wannan da duk lokacin da zai je Hajji yana tafiya ne akan kafafunsa (Tattaki) ba tare da ya hau abin hawa ba. Imam Hasan (AS) ya yi hajji sau 25 da kafafunsa masu albarka. Ya fadi cewa; “Ni ina jin kunyar na sadu da Ubangijina ba tare da na taka da kafafuna na ziyarci dakinSa ba.”
Duk lokacin da yaji an karanta, ko kuma shi ya karanto fadin Allah (T); “Ya Ayyuhallazina Amanu” (Wato ‘Ya ku wadanda kuka yi imani), Imam Hasan (AS) yana tsayawa, yace; “Labbaikallahumma Labbaik!” Wato, ya kasance mai amsa kiran Allah a duk lokacin da ya ambata kiran nan nasa ga muminai.
Idan Imam Hasan (AS) ya doshi Masallaci da nufin Sallah, yakan tsaya a kofar Masallacin ya daga kansa sama, sannan yace; “Daifuka bi babika Ya Allah. Ya Muhsinu, kad atakal masi’u, fatajawaza an kabihi ma indi bi jamili ma indaka Ya Kareem.” Yana mai kirari ga Allah da neman ya canza masa munanansa zuwa ga KyawawanSa Madaukaki Mai Kyautatawa.
Ya kasance baya taba yin Magana da kowa idan ya gama Sallar Asubah, har fitowar rana, ba zai gushe ba yana Ta’akibat din bayan Sallar Subahi. Bai gushe ba a kullum, Imam Hasan (AS) baya bacci sai ya karanta Suratul Kahfi.
Wannan bawan Allah mai girma shine ya yi Shahada a ranar 7 ga watan Safar shekara ta 49 da Hijira, sakamakon guba da Mu’awiya dan Abusufyan ya ba matarsa ta shayar da shi, wanda ya tsittsinka hanjinsa, ya canza launin fatar jikinsa, ya kuma yi sanadiyyar Shahadarsa bayan ya yi jinyar kwanaki 40 cur a jere.
Amincin Allah ya kara tabbata a gareka Ya Imam Hasan Dan Ali Dan Abudalib (AS).
— Saifullahi M Kabir
7 Safar, 1438.

No comments:
Post a Comment