Ya kai dan uwan addini, mai gwagwarmayar Musulunci karkashin Jagora. Tsakaninka da Allah ka yi tunani a karan kanka, cewa tun bayan da aka yi Waki'ar nan, shekara guda kenan kullum dawainiya ake yi da fuskantar abubuwan da ba makawa sai an fuskanta, don Allah, tsakaninka da Allah me ka iya yi na gudummawa wajen ganin an cimma wannan abin?
Waki'ar nan ta ritsa da mutum sama da 3000, daga wadanda ba a gansu ba, Shahidai da Iyalansu da kuma masu rauni. Kullum kokarin Harka da masu tafi da ita shine ta wace hanya za su ga sun kyautatawa iyalan Shahidai da Mafkudai fiye da dubu da ake da su. Karatunsu, abincinsu da suturarsu. Don Allah kai me ka taba yi a wannan bangaren? Nawa ka taba badawa?
Marasa lafiya ne daruruwa, har yanzu ana kan yi musu magani, ko yanzu haka akwai kusan sama da mutum 30 da ba makawa rauninsu ta sa sai an fitar da su asibitin waje don musu magani. Shekara guda kenan ba su gane kansu kullum ciwo. Don Allah wane gudummawa ka iya badawa na ganin wadannan yan uwan namu sun samu lafiya kamar yadda kake? Nawa ka bada a wannan kokarin da Harka da Jagorancinta ke yi?
'Yan uwa ne sama da 200 a Kurkuku a Kaduna tsawon shekara guda kenan. Kullum dawainiyarsu ake yi. Kai me ka iya yi musu? Wane gudummawa ka iya basu? So nawa ka je ka ziyarcesu ka kyautata musu kamar yadda za ka yi burin hakan in a kanka ta fado?
Shari'o'i ne daban daban aka shigar har guda hudu da Sunan Malam da Malama a Kaduna da Abuja. Ga wanda aka shigar da 'yan uwa na Kurkukun Kaduna, Kullum a kotu ake. Ba kawai Kotun Nijeriya ba har da na Duniya (ICC), Lauyoyi aka dauka ana biyansu miliyoyin Nerori. Don Allah dan uwa da yar uwa, tsakaninku da Allah nawa ka bada na gudummawa akan wannan aikin da aka tsayu da shi? Wane gudummawa ka iya ba wannan bangaren?
Kullum ana buga Posters da Banners, sai dai ka gansu kala-kala ana rubuta "Free Zakzaky", ka san yadda ake ana wadannan? Sau nawa ka ba da gudummawarka akan wannan yunkurin? Nawa ka taba badawa na yin wannan aikin don Allah?
Kullum cigaba ake da afkawa 'yan uwa a garuruwa, Harka da Jagorancinta ne kullum ke zama cikin damuwa da lamarin. Ita ke daukar nauyin abin. Kotu aka Kai 'yan uwa, ita ke daukar Lauyoyi su tsaya, a nemi beli in an ba da ta nemo ma'aikata da kudi su cike sharuddan belin a fitar da 'yan uwa. A yayin da suke tsare Harkar ce ke daukar nauyin abincin gidan magidanta har su fito, da abincin wadanda ke dauren. Asibiti ne aka Kai Masu rauni? Harka ke tsayawa, mas'ulanta a Da'irori ke kai kawo wajen hada kudin magani, gado zuwa sallama. Don Allah tsakaninka da Allah ko ke nawa ki taba taimakawa da shi, wane Kokari ki taba yi a wannan bangaren wajen ganin Masu yin wannan dawainiyar ba su wuce ka ba?
Alal misali, a garin Jos, inda na sani, a ranar Ashura an afka mana, aka kama yan uwa kimanin 50 Maza da Mata da yara, bayan an raunata wasu. Sai da aka wayi gari a farko an rasa mutum 5 wadanda za su tsayu da al'amarin 'yan uwan nan kusan 50 da aka kama, har aka Kai su Kotu aka turasu gidan Yari. Sannan aka zo aka samu damar daukar Lauya, aka rika kai komo. Halkoki suka raba kokarin ciyar da gidajen wadanda suke tsare. Wasu tsirarun da'irar suka tsayu da kullum suna Kurkuku suna kotu suna State CID neman beli. Sai da aka shafe kwanaki 23 aka samu belin yara. Sai da aka kwana kusan 38 sannan aka samu belin sauran yan uwan. A yayin da wasu suka tsaya kullum safe da yamma suna girka abincin da zai ishe yan uwan da ke daure suna kai musu. Wannan yasa dole duk Wani shiri da ake da shi na Da'irar ta sha ruwa. Mafi yawan lokaci tsirarun da ke wannan dawainiyar suna yi ne da kudin aljihunsu. Wai fa a hakan ba masu raunin da ke asibiti.
In ka dubi irin wannan abin, ashe zai zama abin zargi ga wanda ke kokarin tafi da damuwowi idan ya zauna ya yi tunanin abin da ya fi dacewa da yanayi ya ayyana akan komai ma? Kai da baka komai sai ka zama abin zarginsa?
Me yasa yankin Kano ba a samu damar cigaba da Tafiyar da aka faro ba? Tsakaninka da Allah kai da ka zama mai surutan an ki a yi kaza, an hana kaza a Facebook da whatsApp, daga lokacin Waki'ar Tattakin bana na yankin Kano makon da ya gabata zuwa yanzu wane gudummawa ka ba masu lura da lamarin wadanda Harin ya shafa? Mutum kusan 50 ke tsare. Ka ziyarce su? Me ka kai musu? Wane Kokari kake yi na ganin an ba da gawarwakin yan uwan mu da aka kashe aka rike? So nawa ka je gaban Jami'an tsaron don neman karbo su? Wa kake tunanin za su karbo su? Magidanta nawa ne a cikinsu? Wane gudummawa ka bada na ganin an ci da Iyalansu da daukar dawainiyarsu kamar suna nan? Wa kake tunanin zai yi? Harka ko? Manyan da zaginsu da jefa bakaken maganganu akan su ya zama ibadarka na safiya da maraice?
Babu shakka abin mu yi Karatun ta-natsu sosai ne akan alakar da ke tsakaninmu da hakkokin da ke kanmu. Wallahi Allah ba zai kyalemu ba idan ya zama aikin wasu shine yiwa Harka Hidima, aikinmu kuma shine zagi da cin mutuncin Masu yin wannan hidimar alhali kwance muke a gado wayarmu na soke a chaji sama da fanka muna danna waya muna wane munafuki, ya hana a yi kaza ya ki ya bari a yi kaza. Anya kuwa Allah zai kyalemu, ba zai kama mu da laifin wannan miyagun dabi'un namu ba?
Eh, Jagora ne yace: "Wanda bai shirya mutuwa ba ya ja baya." Amma me yasa Jagora ya dage Faretin Harisawa da aka saba yi duk shekara akai kusan shekaru 5 ba a yi ba, sai dai a tarasu a yi Kacici-kacici a yi wa'azi a watse? Haka na nufin tsaron Mutuwa ne? Ashe ba a samu lokacin da aka dawo da taron Mauludin Sayyida Zahra (SA) safe ba maimakon Yamma zuwa dare, saboda halin da aka tsinci kai na dokar Yakowa ba?
Idan har zai zama komai na dawainiyar Harkar nan da matsalolinta hangoshi kake yi daga nesa, baka zuwa a tattauna da kai a samo mafita ka shige gaba a aiwatar da kai, bai kamata ya zama kullum sai dai ka bayyana a rubutu kana suka cewa an ki a yi kaza, an janye kaza da sauransu ba. Mu ji tsoron Allah.
Ina rufe rubutuna da tunawa da fadin Imam Sadik (AS) da yake cewa: "Wanda duk ya kasance a muhallin da ake zagin Masoya Allah hakika ya sabawa Allah." wanda ke bamu wajabcin nesantar duk Group din da ya zama wasu sun daukarwa kansu zagi da izgili ga bayin Allah din da basu ma san suna yi ba.
Giba na nufin fadin wasu maganganu marasa kyau ga Wani da bashi a wajen, kamar yadda marasa kunya da mutunci suka daukarwa kansu aikin yinsa a zaurukan 'yan uwa Musamman na WhatsApp. To Amirulmuminin yace mana, "Mai sauraren giba kamar mai yinta ne." Bayan kuma a Wani wajen yana cewa: "Mafi sharrin mutane shine wanda ya kasance dabi'arsa ta zama yada aibin wasu mutane yana kokarin boye nasa." Imam Musa (AS) yace: "Tsinanne ne duk wanda ke cin naman dan uwansa."
Mu ji tsoron Allah. Mu kyautata alakamarmu da shi. Mu yi komai don Allah. Da yawa Masu zage zage da maganganun banza akan rashin Tattaki suna yi ne don gudun kar a ce sun ji kunya ko ace sun ja da baya. Wanda haka ke nuna ko da an fito da su sun fito ne don su nuna suna da wata izza ko isa ko don su ba da haushi ko su huce haushin. Kun mance Imam Husaini na cewa: "Ban fito (zuwa Karbala) ba ina mai fariya da jiji da kai, sai don na yi umurni da kyakkyawa da hani ga mummuna, ina mai kokarin jaddada sakon Kakana (S)." Ka yi tunani, tsoro ne yasa Manzon Allah ya ja baya da shiga Makkah lokacin sulhun Hudaibiyya, bayan kuma Sahabbansa sun masa bai'ar mutuwa a karkashin bishiya?
Yanayi ke ba da damar komai. Allah ya tabbatar da mu. Ya tausaya mana.
— Saifullahi M Kabir
20 Safar 1437 (20/11/2016)

No comments:
Post a Comment