November 09, 2016

YAU CE RANAR DA AKA FARA YAKIN NAHRAWAN

Yau Ce Ranar Da Aka Fara Yakin Nahrawan 

Daga Saifullahi M Kabir




A irin wannan rana ta 9 ga watan Safar a shekara ta 38 da hijira, aka fara yakin Nahrawan, tsakanin Amirulmuminin (AS) da kuma mutanen da ake kira Khawarij. 

Khawarijawa wasu mutane ne da suka fita daga da’ar Amirulmumin (AS), alhali a da suna bayansa. Sai suka koma suna ikirarin cewa Imam Ali (AS) ya kafirta, saboda sulhun da su ne suka tilasta aka yi a lokacin yaudarar da ta auku daga bangaren Mu’awiya a yakin Siffin. Sai suka yi matsayar Imam Ali (AS) ma ya kafirta don haka wajibi ya tuba ko su kashe shi.

Ba ina nufin na baku labarin akan ko su waye Khawarij bane. Ba kuma ina nufin baku labarin abin da ya faru a yakin bane. Amma dai a takaice muna iya cewa Yakin Khawarij wani yaki ne da zamu iya murna sosai da nasarar da Allah ya ba Amirulmuminin a cikinsa.

A wannan yakin ne Imam Ali (AS) ya yake mutane dubu hudu, ya kashe dukkansu in banda mutum kasa da goma da suka arce. A yayin da ba’a kashe mutanen da suka kai mutum goma daga cikin mayakansa ba. Muna gode ma Allah da wannan nasara da ya ba Muminai ta hannun Shugabansu Mai Giraman Daraja.

No comments:

Post a Comment