Ranar 15 ga watan Safar din nan, ta yi daidai da ranar da Jarumi, Mujahidi, Uba, Malami kuma Shahidi mai girma, Shaikh Muhammad Mahmud Turi (RA) ya cika shekaru 55 cur da haihuwa. Madalla da zagayowar ranar haihuwar wannan yaro, matashi, kuma dattijon da ya shafe shekaru 40 cur yana biyayya ga Jagora, Shaikh Zakzaky ba tare da ya kauce ba.
A yayin da Jagoranmu (H) ke godiya ga Allah akan cewa, ya shekara 40 cur yana ibada (bautawa Allah) da yakini kamar yana ganin zahiri. ‘Dan kwarai, Amintaccen almajiri, Shaikh Muhammad Turi ya koma ga Allah ta hanyar Shahada ne bayan ya cika shekaru 40 cur yana biyayya ga jagoran da yake bautar Allah da yakini kamar yana ganin zahiri.
Shaikh Muhammad Mahmud Turi
Wane ne Shaikh Muhammad Turi?
Sunansa MUHAMMAD ne. Sunan mahaifinsa kuma MAHMUD, amma ya fi amfani da TURI MUHAMMAD (wato shi Mahaifin Malam din kenan). Don haka sai ya zama cikakken sunan Shaheed shine MUHAMMAD MAHMUD TURI.
An haifi Malam Muhammad Turi ne a ranar 15 ga watan Safar, 1383 Hijiriyya. Wanda ya yi daidai da 7 ga watan Yulin 1963, wanda yake nufin shekarunsa 55 yanzu a kidayar Hijira, a yayin da yake 53 da watanni a kidayar Miladiyyar Annabi Isa (AS).
Malam Muhammad Turi ya taso a gida ne na manyan mutane, masu dattako kuma masu rufin asiri. Muna iya cewa masu dukiya yadda za a fi fahimta. Ko ba komai, mahaifinsa Mahmud Turi, babban dan boko ne tun a wancan lokacin. Ya taba yin Manaja a kamfanin jaridar ‘New Nigeria’. Kuma ya zama Ciyaman a Vitafoam da Liason company of Nigeria. Don haka ya taso ne a gidan masu arziki daidai gwargwado. Amma bisa zabin Allah, sai Shaikh Muhammad Turi ya zabi ya zama mai addini, tare da kawar da kai daga dukiya da mai da fuska ga neman Lahirarsa, a yayin da ya rungumi Harkar Musulunci, ya kuma sallamawa Jagoranta hakikar sallamawa.
An haifi Shaikh Muhammad Turi ne a garin Zariya, kuma shine mutum na biyu a gidansu a haihuwa. Amma ya yi makarantar Firamare dinsa a Kaduna ne. sannan ya yi Sakandire a FGC Sokoto. Bayan kammalawa ya samu damar shiga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (ABU), wanda bai kai ga gama ta ba aka kore ‘yan uwa a ciki saboda Harkar Musukunci da suke yi, ciki har da shi. Don haka sai Shaikh ya koma Jami’ar Maiduguri (Uni-Maid) ya karanci Lissafi ‘Accounting’
Har ila yau, Shaikh Muhammad Turi ya je International University of Africa a Khartoum, inda ya karanci Shari’a. Ko ba komai tun yana Firamare yana yin karatun addini a wajen Malamai daban-daban a Kaduna da ma Sokoto.
A gurguje, Shaikh Muhammad Turi (RA) ya fara haduwa da Jagoranmu Shaikh Ibraheem Zakzaky ne a wajen wani taron IVC, wanda a lokacin Shaikh Turi yana dan shekara 14 a Duniya. Amma tun daga wannan lokacin, ya mika bai’arsa ga Jagora, bai taba ko gezau ko ya yi rawa da hannun ba har zuwa lokacin da sojojin Nijeriya suka Shahadantar da shi a yayin da yake kokarin ba da kariya ga Jagora (H) a shekarar bara. Lokacin yana da shekaru 54 a Duniya. Wanda yake nufin Malam Turi ya shafe shekaru 40 cur yana tare da Malam kuma yana binsa, bai taba ajiye kafarsa ba face a wajen da Malam (H) ya daga tasa.
Shaikh Ibraheem Zakzaky tare da Shaheed Muhammad Turi
Don haka ne ma Shaikh Muhammad Mahmud Turi, ya kasance wanda ya samu shaidar samun soyayya daga Jagora (H), a yayin da aka ruwaito Malam Zakzaky yake cewa: “… Kuma raina ya zauna da shi (Malam Turi) tun bayan wata magana da ta gudana tsakaninmu muna kurkukun Kaduna tare, kuma na ji kaunarsa ya shiga zuciyata. To naji cewa ba wanda ya kamata lalle ya rike wannan al’amari face Malam Turi, saboda wasu dalilai wanda ba zan bayyana su a nan ba, ba ma zan gaya wa kowa ba.”
Don haka ne ma a cikin maganarsa a yayin da yake ta’aziyya ga ‘yan uwa akan Shahadar Shaikh Turi, Malam Yakubu Yahaya Katsina yake cewa: “Malam Muhammad Turi ba kawai hannun daman Sayyid Zakzaky bane, a’a shi rabin jikinsa ne.” Ya kara da cewa: “Ya kasance mai biyayya da sallamawa.” ‘Yan uwa, wane ne zai maye gurbin Shaikh Turi ga Jagora a cikinmu?
Shaheed Muhammad Turi a sahun Muzaharar Qud's
Magana akan Shaikh Muhammad Turi, rayuwarsa da dabi’u da kuma halayyarsa abu ne mai fadin gaske da ke bukatar taron dangi daga marubuta kuma masana game da rayuwar tasa da kuma masu bincike. Don haka ma nake shawartarsu akan yana da kyau a bazama ga ruwaito ma Duniya irin halayya da dabi’un wannan Mujahidi mai girma. Madalla da wanda duk lokacin da ka gansa sai ka tuna da umurnin Allah na yin Salati ga Annabi (S) da Iyalan gidansa.
Wannan bawan Allah mai girma, ya yi Shahada yana da matarsa daya, Malama Maimuna Abdullahi. Wanda kuma Allah ya albarkace su da samun zuriya masu albarka. ‘ya’yansa shida duk cikansu mata. Fatima (Amira), Zainab, Maryam, Nusaiba, Hakima da Sukaina. Kuma ya aurar da hudu tun kafin Shahadarsa, saura biyu ne ke kan hanya suma insha Allah.
Shaheed Turi tare da Jikokinsa.
Sannan kuma Shaikh Muhammad Turi yana da jikoki 8 a yanzu haka; hudu maza hudu mata. ‘Ya’yan Malama Fatima 3, Zainab 3, Maryam da Nusaiba dai-dai. Muna fatan Allah ya raya su, ya kara musu albarka.
Allah ya kara aminci ga Shaheed Muhammad Turi. Ya bamu I tasu. Wassalamu alaikum wa Rahmatullah.
— Saifullahi M Kabir
muhdsaifu@gmail.com
http://saifmkabir.blogspot.com.ng
11, Safar 1438 (11/11/2016)




🌹😍😍😍
ReplyDelete