November 08, 2016

RANAR WAFATIN SAHABI SALMANUL MUHAMMADIY (RA)

Ranar Wafatin Sahabi Salmanul Muhammadiy (RA)

Daga Saifullahi M. Kabir



 A rana mai kamar yau, 8 ga watan Safar, a shekara ta 36 bayan hijirane Sahabin Manzon Allah (SAWA) mai suna Salman al-Farisiy ko Salman al-Muhammadiy (RA) ya yi wafati. 

 Salman al-Farisiy ya kasance daga cikin ‘Khiyar’ (zababbun) Sahabban Manzon Allah (S). Wanda saboda tsananin biyayyarsa da sallamawarsa ga Manzon Allah (S) ne ma yasa Annabi (S) yace; “Salmanu daga gare mu yake, mu Ahlulbait!”. Wannan ne ya sa ake kiran Salmanul Farisi da Salmanul Muhammadiy. Wato Salmanun Manzon Allah (S).

 Haka ma bayan wafatin Manzon Allah (S), Sahabi Salman ya kasance daga cikin kebabbun sahabban Amirulmumin (AS). Yana daga cikin wadanda basu yarda sun yi ma wani bai’a ba idan ba Imam Ali (AS) ba a bayan Manzon Allah (S). Ya kasance daga cikin Shi’a mafiya kurkusa na Amirulmuminin Ali (AS) da Ahlulbait (AS). Bai ha’inci Manzon Allah (S) ba.

 Ko daga ji, kasan Salman mutum ne daga mutanen Farisa (Iran a yanzu), amma saboda tsananin sallamawarsa cikakkiya ga Annabi da Ahlulbait, wannan ya bashi damar samun ijaza ‘mudlika’ ta kasancewa Sharifi kamar sauran Sharifan da tsatsonsu yakai zuwa ga Manzon Allah Muhammad (S). Madalla da kai ya Salman.
Wafatin Sahabi Salman (RA) ta kasance ne a wani gari da ake ce ma MADA’IN, wanda ya zabi zaman can akan ya zauna a Madina ko makwafciyarta alhali al’ummar Muhammad sun juya ma umurninsa baya. Na’am. Salman ba ya koma zaman Mada’in akan son ransa bane, an kai shi can ne da karfi. Idan ban da haka ba garin da Salman yaso ya rayu a cikinsa kamar Madina inda masoyinsa Muhammad (S) ke ciki.
Kabarin Salmanul Muhammady (RA) 

 Muna sallama a gareka ya kai amintaccen Manzon Allah da Tsarkakan Iyalan gidansa. Muna masu maimaita tsinuwa da la’anta akan wadanda suka cutar da rayuwarka alhali ka kasance daga Ahlulbait (AS) su kuma sun kasance daga wasu kabilun da a cikinsa ma su ‘ya’yan ‘Tabanni’ ne. Allah ya kara maka rahama da jin kai. Ya mika cetonmu a hannun masoyanka ta hanyarka dan matsayinka a wajen Allah (T).

No comments:

Post a Comment