Bayan an gama yakin Jamal, Imam Ali (AS) ya dawo daga Basra zuwa Kufa a Rajab, shekara ta 36 bayan Hijira. Sai ya yanke shawarar kafa cibiyar gwamnatin sa a garin na Kufa saboda a wancan lokacin ita ce a tsakiyar kasashen musulmi, sannan hakan zai taimaka masa wajen hana Mu'awiyya shirin sa na zuwa kasar Iraqi.
Kafin Imam Ali (AS) ya fita yaki da Mu'awiyya, yayi ta kokarin sasanta al'amarin cikin lumana ta hanyar tura Jarir, gwamnan Hamdan; zuwa Syria a matsayin dan sako. Amma kuma sai Jarir ya shagaltu da abun da Mu'awiyya yayi masa, sai ya bata lokacin sa a Syria. Sai bayan wata uku ya dawo da wani sako marar amfani wai ba za'a zauna lafiya ba har sai an hukunta wadanda suka kashe Usman.
Daga karshe dai Imam Ali (AS) ya gane cewa al'amura ba zasu daidaita ba har sai anyi yaki, ba tare da bata lokaci ba ya shirya yabi ta saharar Kudu maso yammacin Asia zuwa Riqqa a gabar kogin Persia. Sai suka gina gada ta tsallaka dasu gefen Syria, wani gari Sur al-Rum. Akwai wasu 'yan yakuna da aka gwabza da wasu rundunonin kanana, daga karshe dai a watan Zulhajjin shekara ta 36 bayan Hijira; rundunar Imam Ali (AS) ta hadu da babbar rundunar Mu'awiyya wacce tuni ta kafa sansani a Siffin.
A Siffin, Mu'awiyya ya tura kwamandan sa, Abul A'awar; da sojoji 10,000 suka tsare kogin dake wajen domin hana sojojin Imam Ali (AS) samun ruwa. Sai Imam Ali (AS) ya turawa Mu'awiyya sakon cewa hakan da yayi ba daidai bane, domin ko ba komai wadanda ya hana ruwa din suma musulmi ne. Imam Ali (AS) ya sake tabbatar masa da cewa lallai ya kamata a bar dukkan sojojin suyi amfani da shi.
Amma kuma, sai Mu'awiyya ya turo da sakon cewa ai lokacin da makasan Usman suka zagaye gidan shima an hana shi ruwa ne, saboda haka yanzu shima Mu'awiyya yana ramawa ne.
Daga karshe dai Imam Ali (AS) ya fahimci cewa sojojin sa zasu sha wahala idan aka ci gaba da zama a haka, saboda haka ya tayar da wata runduna karkashin Malikal Ashtar. Jarumin Sadaukin daga karshe ya kwato kogin bayan yaki mai tsanani, ya kori Abul A'awar. Bayan wannan nasara, Imam Ali (AS) ya cika alkawarin da yayi ta hanyar barin sojojin Mu'awiyya suyi amfani da ruwan yanda suka ga dama.
Imam Ali (AS) ya raba rundunar sa mai sojoji 90,000 gida bakwai, kowane kashi karkashin wani jarumi. Shi ma Mu'awiyya ya raba ta shi rundunar mai sojoji 120,000 zuwa gida bakwai. Kowace rana wani bangare na rundunonin zai gwabza da daya (daya daga cikin bakwai na kowane bangare). An yi wannan salon ne na yakin dai-dai domin Imam Ali (AS) na kokarin rage yawan mutuwar musulmi da yakin bai daya zai iya janyowa. Haka aka yi ta yi har watan Zulhijjah ya kare, watan Muharram ya shigo; wanda aka haramta yaki a cikin sa.
A wannan wata (Muharram), Imam Ali (AS) yayi ta kokarin dakatar da yakin ta hanyar yin sulhu, amma abun yaci tura. Yayi alkawarin cewa lallai zai hukunta makasan Usman idan har Mu'awiyya ya nuna su.
Amma kuma, Mu'awiyya baya son abun ya kare cikin sauki haka, saboda ta dalilin fansar Usman ne ya iya yaudarar mutane ya tara sojoji masu dimbin yawa haka.
A watan Safar aka dawo yaki. Tsawon sati daya, ana yaki mai tsanani kullum.
Kowace rana yaki na kara tsananta fiye da baya. A sati na biyu Imam Ali (AS) ya fito filin daga a karon farko. Bayan jerin fada da daidaikun mutane, a inda yake cin galaba akan duk wanda suka gwabza da shi saboda kwarewar sa, sai ya kasance babu wanda zai iya tarar sa kuma.
Hakan ya sanya Imam Ali (AS) yake neman wanda zai iya karawa da shi. A irin haka, har aka samu wani Jarumi daga rundunar Mu'awiyya yace zai gwabza da shi. Da sara daya tak na Zulfiqar Imam Ali (AS) ya raba gangar jikin sa gida biyu, sama ya rabu da kasa!
Wadanda ke kallon fadan sun yi tunanin ma bai same shi ba, sai bayan dokin jarumin ya matsa gaba kadan inda suka ga kowane bari na jikin ya fadi gefe guda; sannan suka fahimci abun da ya faru.
Sai ya kasance kullum yawan mutuwa sai karuwa yake yi, musamman a bangaren Mu'awiyya. Duk da cewa, a bangaren Imam Ali (AS) ma ya rasa wasu manyan sahabban manzon Allah (S). Daga cikin su akwai Hashim bn Utba da kuma Ammar bn Yasir.
Ammar, wanda a lokacin shekarun sa 93 a duniya, daman Manzon rahama (S) ya sanar da shi cewa za'a kashe shi ne lokacin da yake yakar wasu yan tawaye kuma makiyan musulunci. Wannan kowa ya san haka, kuma saboda haka ne ma bayan an kashe shi sai aka samu rudani a bangaren rundunar Mu'awiyya. Yayi kokarin kwantar musu da hankali ne da cewa, tunda Imam Ali (AS) ne ya janyo Ammar yaki, to lallai shi ya janyo mutuwar sa. Sai yace Imam Ali (AS) ne dan tawayen da Manzon rahama (S) yayi magana akan sa, ba shi (Mu'awiyya) ba. Sai kuwa suka yarda da maganar sa, aka ci gaba da yaki har daren 13.
A wannan rana, babban kwamandan rundunar Imam Ali (AS), Malikal Ashtar; ya kai wani harin jarumta kan makiya. An ji fadin sa na 'Allahu Akbar' duk lokacin da ya kashe mutum wajen akalla sau dari hudu.
Yayin da wannan jarumi Malik ya fara cin galaba akan makiya sai Amr Al-aas daga bangaren Mu'awiyya yace, "A kira makiya zuwa ga maganar Ubangiji."
Cikin sauri Mu'awiyya ya aminta da wannan magana, ya sanya sojojin sa suka daga kwafin alqur'ani guda 500 bisa masu, suna cewa littafin Allah zai yi sulhun wannan rikici. Wannan yaudara tayi galaba a zuciyar wasu daga rundunar Imam Ali (AS), suka yadda makaman su, suka yarda cewa littafin Allah zai warware komai.
Imam Ali (AS) ya shigo cikin filin daga yana karfafa mutanen sa akan suci gaba da yaki kar su yarda da wannan yaudara ta Mu'awiyya, amma sai suka ki yarda. Sai yakin ya canja salo, inda daga karshe aka ce a wakilta mutum daya daga kowane bangare domin su yanke shawarar karshe.
Imam Ali (AS) yaso ace Abdullah bn Abbas ko kuma Malikal Ashtar su wakilce shi, amma sai mutanen sa suka dage akan cewa Musa Ash'ari ne zai je. Mu'awiyya kuma ya zabi Amr Al-aas ya wakilce shi. Abu Musa bashi da salo ko dabara, kuma ko kadan ba sa'an Amr bane wajen iya yaudara.
A zaman da aka yi watanni kadan baya, Amr ya yaudari Abu Musa yaudara mai tsanani.
Ta haka ne Mu'awiyya ya tsira daga shan kashi a yakin Siffin. Amma anyi rashi sosai a yakin. An kashe mutanen Mu'awiyya 45,000 inda Imam Ali (AS) ya rasa mutane 25,000.
An samo wannan labari ne daga littafin "Gaskiya a tarihi".
— Saifullah M Kabir
15 Safar, 1438 (15/11/2016)
— Saifullah M Kabir
15 Safar, 1438 (15/11/2016)
No comments:
Post a Comment