January 07, 2017

DARAJOJIN IMAM ALI (AS) DAGA BAKIN UMAR DAN KHADDABI (R)


An ruwaito a cikin littafin Riyadun-Nadarat, jildi 2, shafi 226 daga Umar ‘Dan Khaddabi yana cewa: Na shaida cewa naji Manzon Allah (S) yana cewa: “Da ace sammai bakwai da kassai bakwai zasu kasance a gefe daya, shi kuma Imanin Ali ‘Dan Abidalib a aje shi a gefe daya, da Imanin Ali ya rinjaye sammai bakwai da kassai bakwai da abin da ke cikinsu”.

An kuma samu a littafin Yunabi’ul-Muwadda, shafi 249 Daga Umar dan Khaddabi, ya daukaka shi daga Manzon Allah (S) yace: “Da ace dukkan tekuna tawadda ne, kuma itace alkaluma ne, mutane kuma marubuta ne, aljanu masu tattarawa ne, ba zasu iya kiyaye dukkan darajojinka ba ya kai Baban Hasan (Ali)”. 

Muhibbud-Dabariy as-Shafi’iy ya kawo a littafinsa ‘Zaka’iru-Ukba’ shafi na 89 daga Umar ‘Dan Khaddabi yace, Naji Manzon Allah (S) yana cewa Ali (AS); “Ya kai Ali, hannunka da nawa zamu shiga (Aljanna) tare ta inda na shiga a ranar Alkiyama”.

A cikin littafin ‘Kaukabud-Durriy’ shafi na 125, daga Umar ‘Dan Kaddabi yace, Manzon Allah (S) yace: “Duk wanda ya ke sonka ya Ali, ya kasance tare da Annabawa a darajarsu a ranar Alkiyama, kuma duk wanda ya mutu da kinka, ya so ya mace a Bayahude ko Banasare!”.

A wani hadisi mai kama da wannan da Muattakal-Hindiy ya kawo a littafinsa ‘Kanzul-ummal’ jildi 6, shafi 154, yace ya nakalto daga littafin ‘Majma’ul Kabir’ na Dabari, da ‘Tarikhul Kabir’ na Ibn Asakir, da isnadinsu daga Manzon Allah (S) yace: “Na yi ma duk wanda ya yi Imani da ni kuma ya gasgata ni wasiyya da riko da Wilayar Ali ‘Dan Abidalib. Duk wanda ya bi shi ni yabi, duk wanda ya bi ne ya bi Allah. Duk wanda yake son shi ni yake so, duk wanda yake so na ya so Allah. Wanda kuwa ya fusata shi ni ya fusata, kuma wanda ya fusata ni ya fusata Allah Mai Girma da Daukaka”.

A cikin littafin ‘Sawa’iku Muhri’ka’ shafi 109, daga Umar dan Khaddabi yana cewa: “…Ku sani, daukaka bata cika face da wilayar Ali (AS)”.

Sayyid Muhammad Salih at-Tirmizi (Bahanafe) ya kawo littafinsa ‘Kaukabud-Durriy’ shafi na 134, daga Umar ‘Dan Khaddabi yace; Yayin da Manzon Allah (S) ya kulla alaka tsakanin Sahabbansa, sai ya dubi Ali (AS) yace: “Wannan (Ali) ‘dan’uwa na ne a Duniya da Lahira, kuma Halifa na ne a cikin iyalaina, kuma wasiyi na ne a cikin al’ummata, kuma shi ne magajin ilimi na, kuma shine magabaci a addini na (Musulunci), duk abin da yake gare shi daga ni yake, amfaninsa amfanina ne, cutuwarsa cutuwata ne, duk wanda yake son sa hakika yana so na, kuma wanda ya fusata shi hakika ni ya fusata”. 

A ‘Riyadun Nadarat’ jildi na 2, shafi na 163, an ruwaito daga Umar dan Khaddabi, cewa, wata rana Umar ya ji wani mutum yana zagin Imam Ali (AS). Sai Umar yace masa; Amma ni ban yi zaton cewa kai kana daga cikin Munafukai ba! Domin naji Manzon Allah (S) ya ce ma Ali (AS): “Kai Matsayinka a wajana kamatr matsayin Haruna ne a wajen Annabi Musa, sai dai ni babu Annabi a bayana.”

Saifullahi M Kabir 

No comments:

Post a Comment