February 11, 2018
Tsage Gaskiya (1)
Daga Saifullahi M Kabir
Ina fara wannan rubutu da sunan Ubangijin da ya yi ma AnnabinSa (S) shaida a cikin littafinSa mai tsarki da cewa: “Kuma baya furuci bisa son ransa, face (duk abin da ya fada) wahayi ne aka yi a gare shi.” Allah (T) da yake wasiyya ga Muminai a cikin Alkur’ani da cewa: “Abin da Manzo (S) ya zo muku da shi ku rike shi, kuma abin da ya haneku a kansa ku hanu.”
SalatinKa Allah da na Mala’ikunKa da na Muminai baki-daya, su kara ninkuwa ga wannan Annabin naKa, zababbe, wanda Ka saukar dangane da shi a cikin Alkur’aninKa mai tsarki kana yabonsa da cewa: “Kuma lallai Kai (Annabi) kana bisa dabi'u masu girma.” Ka kuma yi masa garkuwa daga masu jingina masa gushewar hankali, a yayin da Kake cewa: “Kuma sahibinku (Annabi (S) ba mahaukaci bane!”
Muhimmi kuma mafi girman jaje da Ta’aziyya gare ku baki-daya, dangane da zagayowar lokacin Shahadar Manzon Allah Muhammad (S), wanda ya zo a cikin ingantattun ruwayoyi cewa ta kasance ne a ranar 28 ga watan Safar din shekara ta 11 bayan Hijira.
Yau muna 24 ne ga watan Safar, 1439bh. Wanda rana ce da tarihi ba zai taba mancewa da ita, ko ya kyaleta ta rika zuwa tana wucewa ba tare da raya musiba da ambaton bala’in da ta kunsa ba. Domin kuwa a irin wannan ranar ne na 24 ga Safar, 11bh aka shiga tsakanin Annabi (S) da wanzarwa al’ummarsa dauwamammiyar shiriya. A rana mai kamar yau 24 ga Safar ne aka tabbatarwa da Manzon Allah (S) cewa ba za a taba bari shiriyar da ya zo da ita ta wanzu a kan gaba dayan al’ummarsa ba sai ga ‘yan kadan daga cikinsu, wanda muna fatan Allah ya sa muna cikin kadan masu riko da shiriyar nan.
Ranar 24 ga watan Safar, wanda a wancan shekarar ta 11 bayan hijira, ta kasance ranar Alhamis ne, ta kasance ranar da kamar yadda Ibn Abbas (RA) ke siffata ta, da ranar da mafi bakin cikin abin bakin-ciki ya auku.
A yayin da muke magana da al’umma, mu kan yi iyakan kokarinmu wajen ganin mun yi magana da su ne bisa hujja daga littatafan da suka aminta da su, don idan abin mu ce a cikin littafin Allama Majlisi ya kawo cewa, kaza da kaza ne. Ahlussunnah zai ce, ina ruwanmu da tatsuniyar Shi’a!? Amma idan kace ma Ahlussunah Imaminsa Bukhari ya fada a cikin Sahihinsa. Yanzun nan zai ce, Na’am! Me yace? To a nan, duk girma da nauyin maganar, zai yarda da ita, sai dai kawai idan ta saba da son zuciyarsa ta kau da kai daga shiriyar da kake kokarin haska masa a ciki.
Wana yasa na yi kokarin ya zama na yi wannan rubutun ne bisa rinjayar da dogarona ga Hadisan da Imamin Ahlussunah, Bukhari ya kawo su a cikin ingantaccen littafinsa da aka fi sani da Sahihul Bukhari. A yayin da madogarar da ke biye da shi dan’uwansa ne Muslim a cikin Sahihinsa shima. Ina fatan mai karatu zai bude zuciyarsa ne ya yi ta bina tare da karbar gaskiyar da ke cikin wannan rubutun, har i zuwa kashin karshe da ban san ina ne birki na ba.
Ina magana a kan ranar Alhamis, 24 ga Safar, shekara ta 11 bayan hijirar Annabi (S) me ya faru a wannan ranar?
Dauko littafin Sahihul Bukhari, imma wand aka saya da kudinka, ko wand aka gada, ko kuma ma ka aro daga wani a unguwarku, ka bude ka lalubo Hadisi na 4431 da na 4432, bayan duk isnadin da aka jero a karkashin wadannan Hadisai guda biyu wanda ya tuke zuwa ga Abdullahi Ibn Abbas (RA), za ka ga yana cewa:
“Ranar Alhamis! Ko ka san abin da ya faru a ranar Alhamis din? Yace: Itace ranar da rashin lafiyar Annabi (S) ta tsananta. Sai Annabi (S) yace: “Ku kawo min abin rubutu na rubuta muku rubutun da ba za ku taba bata a bayansa ba har abada.”
Na katse hadisin na muku tambaya? Wannan me Manzon Allah (S) ya yi? Kila ku ce min umurni ko? Su wa ya umurta? Kila kace min Sahabban da a gabansu Allah (T) ya saukar da cewa: ‘Abin da Manzo ya zo muku da shi ku rike shi’ ko? Yanzu Annabi (S) ya zo musu da umurnin cewa su bashi abin rubutu. Me ya hau kan duk wadanda suke cikin wajen su yi? Su bi umurnin nan su bashi ko? To sun bashi? Mu cigaba da Hadisin mu ji.
Ibn Abbas yace; Sai suka yi jayayya, kuma bai cancanta su yi jayayya a gaban Annabi (S) ba! Sai suka ce; “Me ya dameku da shi? Ya fita hayyacinsa!” Inna lillahi wa inna ilaihi Raji’un!
To, su waye suka yi jayayyar? A kan me suka yi jayayya? Kuma da wa suka yi jayayya din? Ibn Abbas ya bamu amsar a Hadisi na 5669, a cikin Sahihul Bukhari.
Hadisi na 5669, Hadisin Ibrahim bin Musa da Isinadinsa na mutane 7 wanda ya tuke izuwa ga Abdullahi Dan Abbas (RA), yace: “Yayin da ajali ya fuskato Manzon Allah (S), a dakin akwai mazaje (Sahabbai), daga cikinsu akwai Umar dan Khaddabi, sai Manzon Allah (S) yace; ‘Ku kusantoni (da abin rubutu) na rubuta muku rubutu wanda ba za ku bace ba a bayansa.’ Sai Umar yace: ‘Lallai rashin lafiya ya galabaitar da Annabi, kuma a wajenku akwai Alkur’ani, Littafin Allah ya wadatar da mu!’
Na kara tsayar da mu a nan na nemi karin bayani; Shin Manzon Allah (S) bai san cewa akai Alkur’ani bane yace a bashi abin rubutun ya rubuta wasiyya? Ba a cikin Alkur’ani din ne Allah ya yi ma Muminai umurni da barin wasiyya ba? Ina fadin Allah (T), cewa Manzon Allah (S) baya furuci bisa son ransa, face duk abin da ya fada wahayi ne aka masa? Ashe umurnin Annabi (S) ba abin bi bane a kowane hali? To me yasa Umar ya hana, ya kuma bai yi shiru ba ma har sai da yake fadawa mutane a gaban Annabi cewa Alkur’ani ya ishe su? Basu bukatar shiriyar da Annabi zai rubuta musu kenan?
A cigaban Hadisin, Ibn Abbas yace: (Da Umar ya fadi hakan), Sai mutanen da ke cikin dakin suka samu sabani, (suka rabu gida biyu), suna masu husuma da junansu. Daga cikinsu akwai masu cewa; ‘Ku kawo wa Manzon Allah (S) ya rubuta muku abin da ba za ku bace ba a bayansa.’ Daga cikinsu kuma akwai masu cewa abin da Umar yace. (Wato kar a bayar, zafin ciwo ne ke damun Manzon Allah (S)).
Tambaya; Ashe Allah (T) bai ce; “Baku da zabi (Ku Muminai) idan Allah da ManzonSa suka yi hukunci akan wani al’amari” ba? Yanzu har Manzon Allah (S) yace a bashi, wani yace ba za a bada ba! Ba a da bukata! Littafin Allah ya isa! Kuma Mumini, ace mumininma Sahabi a gaban Annabi ya goyi bayan mai sabawa Annabi din nan, har ya zama akwai bangaren Manzon Allah da bangaren Umar? Wane ne Umar da za ku bi ra’ayinsa ku bar umurnin Manzon Allah, in dai kun yi Imani da Allah da ManzonSa!?
Dan Abbas ya cigaba da cewa: Yayin da wargi da sabaninsu ya yawaita a gaban Manzon Allah (S), sai Annabi (S) yace dasu; ‘Ku tashi daga gareni (ku fice min)!”
A Hadisin aka karkare da cewa, Ubaidullahi yace; Ibn Abbas (RA) ya kasance yana cewa “Mafi girman dukkan abin bakin ciki shine abin da ya katange tsakanin Manzon Allah (S) da ya rubuta musu wannan rubutun, saboda sabaninsu da kuma warginsu.”
Akwai shigen hadisin da ya gabata, hadisi na 7366. Haka ma a Hadisi na 114 a cikin Bukhari din, makamancin wanda ya gabata, Manzon Allah (S) yace musu ne; “Ku fice daga gare ni, domin bai cancanta ku yi jayayya a gabana ba!” Sai Ibn Abbas ya fito, yana cewa: “Mafi bakin cikin abin bakin ciki, shine abin da ya shiga tsakanin Manzon Allah (S) da rubutunsa.”
A hadisi na 3053 a Sahihul Bukhari, Ibn Abbas yace, bayan da suka yi jayayyan, wasu daga cikinsu sai suka ce: ‘Hankalin Manzon Allah (S) ya gushe!’ Manzon Allah (S) sai yace musu; “Ku kyale ni, abin da nake a kansa ya fi abin da kuke jingina min” (Wato ni ba hauka nake yi ba, na san abin da nake fadi muku).
Ya kai Musulmi mai Imani! Har yanzu duniyar Musulmi suna rabe ne gida biyu, gado daga Sahabban da ke cikin wannan dakin. Har yau din nan da masu goyon bayan Manzon Allah (S) ne da kuma masu goyon bayan abin da Umar yace ga Annabi (S); cewa zafin ciwo ya rinjaye shi; cewa hankalinsa ya gushe; cewa ba mu da bukatar abin da zai rubuta mana; cewa a tare da ku akwai Alkur’ani, ya ishemu daga abin da Manzon Allah (S) zai rubuta mana! Tir!!! Kai a wanne bangare kake?
Wannan ba zagin Sahabbai bane, in ka fahimce shi a zagin Sahabbai ko raina su, sai nace ka fara komar da laifi ga Imaminka Bukhari da ya ruwaito abin da sahabban suka aikata daga bakin sahabi Ibn Abbas. Amma wallahi muna fada ne don mutum ya farka. Ya fahimci cewa addinin nan fa na Musulunci, Allah ne ya aiko Annabi Muhammadu (S) da shi, kuma ya wajabta a bi shi a kowace lahazar rayuwarsa da bayan ransa, kuma ya sanya sabawa Annabin nan a matsayin saba masa a yayin da yace: “Wanda ya bi Manzo hakika ya bi Allah.”
Idan har ta bayyana wasu gungun Sahabban Annabi (S) sun saba masa, ba kawai saba masa masa ba, sun ji ma jayayya da shi, ba kawai jayayya ba har fito-na-fito sun yi da shi, yace kaza su ce kaza ne, kamar yadda za mu ci a can gaba a cikin wannan nazarin, don me za su zama maka abin bi? Ashe Allah (T) bai ce; “Babu biyayya ga halitta a kan sabawa Allah ba?”
Hana abin rubutu da Umar tare da wasu gungun sahabbai suka yi, har ta kai ga Annabi (S) ya yi fushi da su yace su tashi daga kansa su fice su bashi waje, ba sabawa Allah bane? Don me suka zama maka abin bi a yanzu!?
Me yasa suka yi abin da suka yi a wannan lokacin? Shin sun yi makamancinsa kafin rannan? Me suka aikata bayan hanawan? Meye ra’ayi da isharar Manzon Allah (S) akan su a bayansa?
Insha Allah a cigaban rubutunmu za mu ji su.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment