February 11, 2018

Tsage Gaskiya (10)

Daga Saifullahi M Kabir 

A yayin da Amirulmuminin (AS) yake ta sabgogin kokarin ganin ya yi wa Manzon Allah (S) sutura ya bizne shi, sai ya zama na su kuma Muhajirun da Ansar sun watsar da wannan sha’anin na jana’izar Annabi, suka dankara ma kansu hada-hadar kokarin sun fitar ma da kansu Khalifan da ya dace da son ransu.

Nan suka nufi wani waje da ake cema ‘Sakifar Bani Sa’ada, inda kowace Kabila daga Kabilun Madina kowannensu yake raya cewa lazim su ne za su samu matsayin su halifci Annabi (S). Abin mamaki sosai, ta yadda za mu ga cewa kwata-kwata, bai wuce wata 2 ba Manzon Allah (S) ya tara su a Ghadeer Khum ya halifantar da Imam Ali (AS) a matsayin halifansa a cikinsu a bayansa. Amma kuma yau ga Manzon nan ya koma ga Allah (T), ko bizne shi ba a yi ba, amma har sun juya ma umurninsa baya.

Dama a cikin Alkur’ani, Allah (T) yace: “Muhammadu ba kowa bane face Manzo, kuma Manzonni sun gabace shi. Shin idan ya mutu, ko kuma aka kashe shi, za ku (yi ridda) ne ku koma ga abin da diga-diginku ke kai (Jahiliyya)?” Sai kuwa mutanen nan suka ba Allah amsa a aikace da cewa Eh! Mun zabi mu watsar da abin da ya zo da shi, mu yi son ranmu. Wanda hakan shine Jahiliyya din.

Ba za ku yi mamakin juya bayansu da kin karban wasiccin Manzon Allah (S) ba a yayin da ya yi wafati, tunda a halin da yake da ransa ma, ya musu umurni da abubuwa da dama sun ki yi, kamar yadda muka kawo misalsalai a baya.

Daga misali, maganar kawo abin rubutu, wanda suka maid a abin hayaniya da hargowa, har ya kare yace duk su fita su bashi waje. Da kuma batun tura su yaki da ya yi a karkashin Usamatu Dan Zaidu, da suka ki su je, suka dawo suka tsaya a kansa, ya daga kai ya gansu yace Allah ya la’anci duk wanda bai kama hanya ya tafi ba. Kuma basu je din ba. Yana raye kenan. Ina kuma ga ace ga shi sun ga baya numfashi? Bai da halin yi musu magana? Sai su bi umurninsa a wannan lokacin? Eh, haka ya kamata, amma ba su yi hakan ba!

Toh, a Sakifa sai Muhajirun (Wato mutanen Makkah) suka yi ikirarin cewa lallai su ne suka fi dacewa da a samu halifan Annabi a cikinsu, saboda sun fi Ansar (mutanen Madina) dadewa da zama Musulmi, sun kasance tare da Annabin kafin Ansar. Gori ko fariya kala-kala, ciki harda cewa su ne suka iya baro gidajensu a Makkah da dukiyoyinsu da kuma kayayyakinsu suka biyo Manzon Allah zuwa Hijirar da ya yi.

Ansar kuma suka ce su ne ya kamata su zama Halifan Annabi saboda sun ba Annabi mafaka a Madina a yayin da aka kore shi daga Makkah. Kuma suka ba shi kariya a yayin da karfafan makiya suka taso shi a gaba da yaki. Suma cikin nasu gorin, har da cewa, ai shekara 13 Annabi ya yi a Makkah yana da’awa, amma sai ‘yan kadan suka karba masa. Amma tunda ya zo garesu, suka karba hannu bibiyu. Dan haka sune ya fi dacewa su halifance shi tunda sune suka taimaki Musuluncin da yazo da shi ya karfafa.

Wani abu da ya kamata ku sani shine, a daidai lokacin da suke can suna wannan hargowar, shi Imam Ali (AS) tare da Abbas (AS) da wasu tsiraru suna wajen jana’izar Annabi. To a nan ne Abbas yace ma Imam Ali (AS); “Ya Aliy, miko hannunka na yi maka mubayi’a.” Sai ya zama Ammin Manzon Allah (Abbas) ya yi ma ‘Dan Ammin Manzon Allah (Ali) mubayi’a kenan. Abbas yace: “Su ma mutanen da suke cikin gidan nan duk su yi maka bai’ar. Domin idan akai hakan to ba zai kwantu ba (cikin sauki ba).”

Sai Imam Ali (AS) yace masa: “Ah! Wane ne kake tunanin zai ce wannan al’amarin nashi ne ba namu ba?” (Amirulmuminin na masa tambayar a sigar yanke uzuri ba wai don bai san za a kwace masa din ba).

An ce Abbas ya je wajen Abubakar da Ummar ya tambaye su daya bayan daya, shin Manzon Allah ya muku wasicci da wani abu? Suka ce masa, a’a. Amma duk da hakan ya nemi Ali ya kawo hannunsa dai ya masa bai’a shi da mutanen gidan. Amma Imam Ali (AS) yace masa: “Mu shagaltu da al’amarin Jana’izar nan tukunna. Shine aula akan komai.”

Wannan kamar yadda mai littafin Imama Was-siyasa ya kawo kenan. Wanda idan abin muce, Ah! to ina ce Annabi ya sanar da Imam Ali abin da za a yin? Sai muce eh mana. Amma kana tsammanin Imam zai bar abin daya dace ne ya je ga rudin duniya saboda kar ta kubuce masa?

To mu komo ga Sakifar. A yayin da Abubakar ya ji labarin abin da ke wakana a Sakifa, sai ya yi maza ya sanar da Umar, sai sukai maza suka tafi suma, a hanya suka hadu da Abu Ubaida binil Jarra, sai suka rankaya. Yayin da suka isa, suka iske Ansar sun tsayar da Sa’ad bin Ubadah a matsayin wanda zai jagoranci Musulmi. Sai Umar yace ina, hakan ba zai yiwu ba fa. Lazim ne a samu halifan nan daga Muhajirun ne.

A nan sai Abubakar ya tashi ya musu huduba. Ya yabi Ansar a cikinta sosai ya musu godiya da duk abin da suka ma Musulunci, don ya kwantar musu da hankali, sannan yace musu, shi yana ganin wannan al’amarin ko dai ya kasance a hannun Abu Ubaidata ko ga Umar. Kowanne a cikinsu ya san kan wannan al’amarin.

Sai Umar da Abu Ubaida suka ce, bai cancanta ga wani a cikin mutane ya gabaceka ba Ya Ababakar. Suka ce miko hannu mun maka bai’a. To a nan sai Ansar wadanda suke da manyan kabiloli guda biyu, suka samu sabani a tsakaninsu (Aus da Khazraj). Dama sun kasance masu fada da juna kafin Manzon Allah ya zo ya hada kansu, aiko rannan suka sake ballewa. Bashir dan Sa’ad, wanda yake daga kabilar Aws ne, sai ya mike shima ya ma Abubakar bai’a, saboda ya kawar da yunkurin Ansar na yin bai’a ga Sa’ad bin Ubada, wanda yake shine shugaban kabilar Khazraj dama. Sai nan da nan dai ya zama rinjayen kuri’ar tana kan Muhajirin ne.

Labarin Sakifa na da tsawo, ba shi kawai muke son yi ba. A takaice, su Banu Hashin sun taru ga Imam Ali (AS) akan lallai shi za su ma bai’a, domin kuwa tunda tabbas Manzon Allah (S) ya bar Amirulmumin (AS) ne a matsayin halifansa a bayansa, to ba su ga dalilin da zai sa su yi mubayi’a ga wanin Ali ba alhali yana raye.

A cikin Imama Was-Siyasa, ya kawo cewa, Imam Ali da Abbas (AS) da wadanda suke tare da su na daga Banu Hashim, sun kasance a tare a gidan Sayyida Fatima, tare da su akwai Zubair binil Auwam (wanda yake shi mahaifiyarsa Bahashimiya ce, dan haka yake jingina kansa da Hashimawa).

Sai Umar ya debi tawaga suka nufi gidan, tare da shi akwai Usair Bin Hudair da Salamatu bin Salama, suka je kofar gidan suka ce, Ku fito ku ma Abubakar bai’a. Amma Imam (AS) suka ki. Sai suka ji Umar yana cewa ku saka ma gidan wuta! A nan sai Imam (AS) suka fito tare da Abbas da Zubair. Zubair ya daga takobi, sai Umar yace ma Salamat maza ka rike shi. Sai suka taru a kan su Imam (AS) suka tafi da su.

Suna ji a wannan lokacin Sayyida Zahara (SA) tana kai kara wajen Annabi, tana cewa: “Ya Babana, kaga daga wafatinka abin da yake samunmu daga dan Abu Quhafa. Dubi yadda cikin lokaci suka watsar da kalmomin da ka ambata a Ghadeer cewa; “Ali a wajenka kamar Harun ne a wajen Musa.” Sai ya zama wasu daga cikinsu har sun yanke cewa lallai ba da su a wannan aika-aikar ba. Tunda suka ji Tsokar jikin Annabi na kai kara gareshi. Wasu daga nan suka bar wajen. Amma su Umar da wadanda ke tare da shi da ba su da nufin yin nadama, sai suka daure Imam (AS) da igiya, wai don kar ya gudu, suka ja shi zuwa Masallaci akan ya yi bai’a.

Dubi abin ban mamaki, Alin da yake zakin Allah, gwarzon Badar, Uhudu, Khandaq, Kyaibar da Hunain, amma shi yau wannan mutumin da bai tana jurewa ya tsaya a fagen daga ba yake ja da igiya. Hakan na nuna girman hakuri da juriyan Imam ne da kuma sallamawa da bin umurninsa na Annabi (S) kamar yadda muka kawo a baya. Tare da kiyaye maslahar Musulunci a lokacin.

Da aka kai Imam Ali gaban Halifan nasu, Sai Umar yace idan har Imam bai yi mubayi’a ga Abubakar ba zai kashe shi. Sai Imam Ali yace masa: “Yanzu za ka kashe Bawan Allah, kuma dan’uwan Manzon Allah?” Imam Ali yace musu: “Ni bawan Allah ne kuma dan’uwan Manzon Allah. Ni ne naked a hakki akan wannan al’amarin (halifanci) akanku, ba zan muku mubayi’a ba alhali ku ne kuke da hakki akan ku min bai’a.” Yace musu: “Kun karbe wannan al’amarin (Halifanci) daga hannun Ansar, kun kafa musu hujja da kusancinku da  Annabi, amma kuma sai ku kwace shi daga garemu mu iyalan gidan Annabin? Ashe ba ku ne kuka ce ma Ansar kun karbi wannan mulkin vane daga gare su saboda Annabi ya kasance ne daga cikinku? Suka sallama muku al’amarin.”

Imam ya cigaba da cewa: “Ni ina kafa muku hujja da irin abin da kuka kafawa Ansar hujja da shi; Mu muka fi cancanta da halifcin Annabi yana raye ko ba shi. Ku kyalemu idan kun kasance masu imani, idan kuwa ba haka ba, to za a yi muku bai’a bisa zalunci alhali kuna sane!”

Da Umar ya ga Abubakar ya yi shiru bai ce uffan ba a lokacin. Sai yace masa, ba za ka nemi da ya maka bai’a ba ko? Sai Abubakar yace masa, matukar Fatima tana raye, to ba zan tilasta mijinta ya min bai’a ba. Wannan yasa suka sake Imam Ali a lokacin. A nan sai Imam (AS) ya nufi kabarin Manzon Allah yana kai masa kukan yadda mutane suka canza daga barinsa wannan duniyar.


To, ta iya yiwuwa jin maganar Abubakar na cewa ba zai iya tilasta Imam ya yi bai’a ba matukar Sayyida Zahara tana raye. Wannan ne ya ba dan Sahhaqu karfin hali na ganin yadda zai bullo ma al’amarin. Nan ya ga to a kashe Fatima din mana, indai hakan zai sa Ali ya yi bai’a a huta! Wannan kuma shi ya kai ga komawa sake kai hari gidan Sayyida Zahra (S), wanda ya yi sanadiyyar karya kashin awazanta da kashe tayinta, kona gidanta da ma shahadarta. Kamar yadda insha Allah za mu zo da bayanin yadda abubuwan suka faru.

No comments:

Post a Comment