January 03, 2019

WATAN DISAMBAR 2015 A KUNDIN ADANA NA

WATAN DISAMBAR 2015 A KUNDIN ADANA BAYANAI NA

Daga Saifullahi M. Kabir

Bayan na na kammala fitar da muhimman abubuwa guda 40 da suka faru a shekarar 2018 da suka shafi Harkar Musulunci da motsin fafutukar ganin an saki Jagora, Sayyid Zakzaky (H). Wasu ‘yan uwa sun bukaci a yi bitan sauran shekarun da suka gabata, musamman daga Disambar 2015, da shekarar 2016 da kuma 2017 ma a bisa jerin raneku.



1- Ranar 2 ga watan Disambar 2015 aka kammala Tattakin Arba’in din Imam Husaini (AS), wanda a cikinsa aka samu Shahidai 23 daga masu tasowa ta bangaren Kano zuwa Zariya, sakamakon Bom da jami’an tsaron gwamnatin Buhari suka dasa a jikin wasu yara guda biyu. Na farko ya tashi, na biyun aka kwance shi kafin ya tashi.

2- Ranar 12-14/12/2015 aka yi Waki’ar Zariya, wanda sojoji suka dira a kan ‘yan uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), suka kashe fiye da mutum 1000 a cikin kwanaki 2, suka kona tare da rushe gidan Shaikh Zakzaky da wasu gine-gine akalla guda bakwai da suke da alaka da Shaikh din. Suka kashe ‘ya’yansa uku da ‘yan uwansa da yayarsa mace, suka harbe shi da matarsa suka kama su suka tafi da su cikin jinni, har yau shekaru uku kenan suna tsare da su bisa zalunci.

3- Ranar Litini 14/12/2015 Manjo-Janar Adeniyi Oyebade, shugaban rundunar soja ta 1 da ke Kaduna, wanda shi ya jagoranci duk ‘operations’ din da aka yi na kisan kiyashin Zariya, ya gana da manema labarai, inda ya bayyana musu cewa shi ya ba da umurnin a mamaye gidan Malam, Husainiyyah da kuma Darur Rahma a kawo masa Shaikh Zakzaky. Ya kuma ce Shaikh Zakzaky da matarsa Zeenah suna nan a raye, a ‘Protective Custody’.

4- Ranar Talata 15/12/2015 ‘yan uwa suka gudanar da gagarumar Muzaharar kira a saki Shaikh Zakzaky tare da yin Allah-wadai da kisan kiyashin Zariya a garin Kaduna. ‘yan sanda sun budewa ‘yan uwa wuta, inda suka kashe mutum 13. Mutum 7 daga cikin Shahidan an kashe su ne nan take, a yayin da mutum 6 ‘yan sanda sun tafi da su da ransu ne suka kashe su, sai bayan Waki’ar da kwana shida suka ba da gawarwakinsu akai musu Jana’iza.

5- Ranar Laraba 16/12/2015 kafar watsa labarai ta FARS NEWS AGENCY ta ruwaito cewa Sarkin Saudiyyah, Salman Bin Abdul’azeez ya kira Shugaban kasar Nijeriya, Muhammadu Buhari ya taya shi murna tare da bayyana kisan kiyashin Zariya a matsayin Yaqi da Ta’addanci.
 A wannan ranar ne sojoji suka kwashe duk gawarwakin da suka kashe daga asibitin Shika, da kuma wadanda suka aje su a Depo dinsu a Zariya, suka kai su wani kauye da ake kira Mando a bayan garin Kaduna suka bizne su cikin dare. Kamar yadda sakataren gwamnatin jihar Kaduna ya tabbatar a gaban kwamitin JCI.

6- Ranar Alhamis 17/12/2015 ne Gwamnan jihar Kaduna, Nasiru Elrufa’I ya fito a gidan Rediyon jihar Kaduna yana magana a kan matsayar gwamnatinsa a kan kisan kiyashin da sojoji suka yi a Zariya. Ya yi ikirarin cewa Harkar Musulunci tana mamaye gidajen mutane tai musu barazanar kwace su, kuma tana gina waje ba bisa izini ba, sannan ‘yan Harkar Musuluncin suna hawa su yi tafiya a kan Titin Gwamnati har su yi amfani da makarantun gwamnati (a yayin da suke Tattakin juyayin Shahadar jikan Manzon Allah (S), Imam Husaini (AS). Bayan ya jera zarge-zarge da kazafofinsa, sai yace zai kafa kwamitin bincike kana bin da ya faru a Zariya.
 A irin wannan ranar ne kuma shugaban sojojin Nijeriya, Tukur Yusuf Buratai ya bayyana cewa sun mika Shaikh Zakzaky ga inda ya dace don a hukunta shi.

7- Ranar Juma’a 18/12/2018 aka gudanar da Muzaharorin Allah-wadai da kisan kiyashin Zariya da sojojin Nijeriya suka aiwatar a kusan kowane bangare na kasashen Duniya. A Pakistan kawai an yi Muzahara a garuruwa kusan 50. Haka ma a Indiya da Iran, Iraq, NewYork, Istambul, Canada, da sauransu, bare kuma a Nijeriya, kauye da birni ‘yan uwa sun fita suna Allah-wadai, tare da kira a saki Jagora, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H).
 A wannan ranar wasu daidaikun mutane sun rika Allah-wadai da ta’addancin sojojin gwamnatin Nijeriya, kamar tsohon ministan harkokin jiragen sama na Nijeriya, Femi Fani Kayode, a wani rubutu da ya sake a kafar sadarwa, ya bayyana abin da ya faru a matsayin shiryayye kuma tsararren abu, inda ya kuma nuna takaicinsa kan yadda sojoji suka kona gidaje bayan sun kashe ‘yan kasa wadanda basu dauke da makami. Ya kuma jaddadawa Buhari da Buratai cewa kotun ICC tana jiransu. Shima Ministan Matasa da wasanni na kasa, Solomon Dalung ya yi Allah wadai da abin da ya faru, kamar yadda wata kafa ta thewistleng.com ta ruwaito.
 A wannan ranar Fadar Shugaban kasa ta sanar da cewa rikicin ba abu ne da ya shafe ta ba, ya shafi sojoji ne kawai, don haka ba za su ce uffan ba.

8- Ranar 19/12/2015, Gwamnonin Arewacin Nijeriya a karkashin shugabancin Kasim Shettima suka yi zama a Kaduna a kan yadda za su bullowa Harkar Musulunci da ‘yan Harkar a jihohinsu, musamman ma ta fuskacin hana su fita Muzaharori. A

9- A ranar Lahadi zuwa Talata 20-22/12/2015 ne gwamnatin jihar Kaduna ta tura hukumar KASUPDA tare da jami’an tsaro suka je suka karisa rusa Husainiyyah Bakiyyatullah, da ginin NTC da shagunan tsallaken Husainiyyah, da Darur Rahma da masallacin da ke cikinsa, suka je unguwar Jushi a cikin garin Zariya suka rushe gidan da aka bizne mahaifiyar Shaikh Zakzaky, suka kuma rushe Fudiyyah Islamic Center da ke unguwar Dan-Magaji a Zariya.

10- Ranar 21/12/2015 ne wani ‘audio’ ya bayyana na Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, inda yake yabawa da kisan kiyashin da aka yi ma ‘yan Shi’a a cewarsa. Ya bayyana ‘yan Shi’a a matsayin wadanda suke zagin Sahabbai, kuma yace Arewacin Nijeriya Ahlussunnah ne ya kafa shi, don haka ba za su cigaba da zura ido ‘Yan Shi’a suna zagin Sahabbai ba. Ya jingina duk kisan da su Janar Oyebade suka yi a matsayin sakamakon zagin sahabbai ne.

11- Ranar 22/12/2015 Kungiyar Biafara suka fitar da takardar Allah wadai da kisan da aka ma ‘yan kasa marasa dauke da makami a Zariya, ta hannun wani jigo a kungiyar mai suna Ndubuisi Anukwuem.
 Shima wani babban Lauya mai rajin kare hakkin dan Adam, Mista Femi Falana SAN ya yi tir da harin na Zariya a wani shiri ‘Breakfast show’ a gidan TV din Channels TV. Falana ya jaddada cewa dole ne gwamnatin Nijeriya ta biya diyyar wannan barnar da ta yi, ta kuma hukunta duk ofisoshin da suke da hannu wajen kisan-kiyashin na Zariya. Sannan kuma ya ba da shawarar a saka darussan da suka shafi ‘Yancin Dan Adam a makarantun hoton sojoji.

12- Ranar 24/12/2015 Kungiyar Iyamurai ta Igbo-Mandate Congress (IMC) ta yi Allah-wadai, tare da yin kira ga Buhari a kan ya ba Shaikh Zakzaky hakuri a kana bin da sojoji sukai masa. Sun yi kiran ne ta bakin babban daraktansu, Rev. Obinna Akukwe.
 Wata Kungiya mai suna ‘Social Party of Nigeria’ ta hannun kakakinta, Segun Sango, ita ma ta yi kira ga shugaban sojoji, Buratai ya sauka daga mukaminsa saboda abin kunyar da sojoji suka yi na kashe yan kasa marasa dauke da makami har daruruwa a cikin kwanaki biyu. Sun kuma yi Allah-wadai da hana Muzahara da afkawa masu yinsa da gwamnatin jihar Kaduna ke yi, inda suka ce ‘Hana mutane zanga-zangar lumana a kan hakkinsu goyawa zalunci baya ne.’
 Haka ma kungiyar ‘Non-Profit Making Organisation’ ta hannun Daraktanta, Josept Otteh, ta yi kira ga Buratai ya sauka daga mukaminsa don a bincike shi. Suka kuma bayyana harin a matsayin haramtacce wanda ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa.

13- Ranar 28/12/2015 ne kungiyar Malamai da Limamai (na Wahabiyawa) na jihar Kaduna suka ziyarci gwamnan Kaduna, Elrufa’I a kan kudirinsu na mara masa baya a kan cigaba da fada da Shi’a (sunan da suka fi kiran Harkar Musulunci da shi).

Wadannan a takaice sune abubuwan da Kundi na ya iya taskacewa sun auku a jere a watan Disambar 2015 da suka shafi Harkar Musulunci ko Waki’ar Zariya. Saura na shekarar 2016 da 2017, in Allah ya bani iko insha Allah.

No comments:

Post a Comment