January 06, 2019

Shekaru 3 Da Kisan Kiyashin Zariya (1)

Daga Saifullahi M. Kabir

WAIWAYE

Kimanin shekaru tara da suka gabata, gwamnatin Nijeriya bisa umurnin tsohon Shugaban kasa, Marigayi Umaru Musa ’Yara’aduwa, ta yi shiri na musamman don murkushe Harkar Musulunci a Nijeriya ta hanyar kashe Jagoranta Shaikh Ibraheem Zakzaky da tarwatsa dukkan dandazon mabiyansa.

Gidan Shaikh Ibraheem Zakzaky da sojoji suka rusa. 

A wancan lokacin, sun tsara cewa, za su saka bam ne a gidan Shaikh Zakzaky, sai ya zama cikin sauki shi da dukkan iyalansa sun rasu. A yayin da mabiya suka fito da nufin yin Allah wadai da wannan mummunan aikin, sai su bude wuta a kan su, kamar dai yadda suka yi ga wasu mutane da aka kira su da suna ’yan kungiyar Boko Haram a Jihohin Arewa-maso-gabashin Nijeriya a shekarar 2009.

Wannan yunkurin na gwamnatin ’Yar’aduwa ya bi ruwa ne bayan da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya samu cikakken rahoton zaman sirrin da suka tsara aiwatar da wannan danyen aikin, tare da kwafin takardar sirri (blueprint) din gwamnati kan yadda ta tsara za ta aiwatar da kisan-kiyashin.

Shaikh Zakzaky bai yi jinkiri ba wajen sanarwa da duniya halin da ake ciki, a wajen Tafsirin Alkur’ani na watan Ramadanan 1430 a FIC, Zariya.

Duk da fallasa cewa, jami’an tsaro na shirin yin kisan-kiyashi a kan ’yan’uwa Musulmi da Shaikh Zakzaky ya yi a wannan lokacin, bai hana jami’an tsaron bude wa masu Muzaharar nuna goyon bayan Palasdinawa wuta a Zariya ba a ranar Juma’ar karshen Ramadan din wannan shekarar, wacce ta dace da 18/9/2009, inda suka kashe mutum biyu, tare da jikkata gomomi a daidai kofar Doka, Zariya.

Bayan rasuwar Marigayi Umaru Musa ’Yar’aduwa a ranar 5/5/2010, da yake kamar yadda Shaikh Zakzaky ya sha fada karara cewa, wasu ayyanannun kasashe ne suke da nufin a kashe masu shi, a kuma kawo karshen Harkar Musulunci a Nijeriya, kasancewar suna kallon ta a matsayin barazana gare su daga nufinsu na sake mamaye kasar nan da dibar arzikin cikinta. Don haka sai kwangilar kashe shi ta komo hannun Shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Da farko kasashen da ke nufin ganin bayan Shaikh Zakzaky da da’awarsa, wanda suka hada da Amurka da Isra’ila, sun ba da kwangilar hakan ne ga wani Baturen Birtaniya, mazaunin kasar Amurka, mai suna Patrick William, wanda aka ce yana da kamfani na musamman don yin kisan mummuke ga duk wanda ake bukatar kashewa a duniya.

Patrick ya samu cikakken iko na amfani da wasu jami’an tsaron kasar nan a duk sad da yake bukata, inda suka rika shirin su harbe Shaikh Zakzaky, musamman a kan hanyarsa ta zuwa Husainiyyah Bakiyyatullah, inda yake bayar da karatu. Sai dai, hakan ya ci masu tura, a yayin da a ranar Mauludin Manzon Allah (S) na shekarar 1433 (19/2/2012), Shaikh Ibraheem Zakzaky ya fallasa wannan shirin, ya kuma yi wa Patrick da wadanda suka ba shi aikin albishir da rashin cikar burinsu.

Shaikh Zakzaky yake cewa; “Duk ranar da Allah ya kaddara min ajali, ya kuma zama shahada ya kaddara min, kuma ya zama kai Patrick kai ne makashina, zan yi wa kaina kyakkyawan albishir, in ce Alhamdulillah! Na gode wa Allah da ya zama kafiri tantiri irin ka ne aka ba shi kwangilar kashe ni. Albishirinka! Kai kuma ba za ka rayu bayana ba, ko shekara ma ba za ka yi ba. Wannan ma idan ka ga an kashe ni ajalina ne ya yi, kuma ko a kashe ni ko in mutu, wani abu guda shi ne, addinin yana nan, ruhin addinin kuma yana nan. Shi wannan ba ku isa ku kashe ba!”

Daga baya, kwangilar kashe Shaikh Zakzaky da murkushe Harkar Musulunci ta koma kai tsaye hannun Jonathan, tare da mataimakinsa Namadi Sambo. Kamar yadda a wani jawabinsa a shekarar 2013 Shaikh Zakzaky yake bayyanawa: “To, kuma yanzu sun sanar da shi Shugaban kasa da mataimakinsa, duk an sanar da su, kuma sun yarda sun saka hannu a kan sun amince za a kawar da al-Zakzaky.”

Don haka ya zama dare da rana, kowane lokaci, musamman a karshen mulkin Jonathan, Shaikh Zakzaky na faman tsallake yunkurin kisa ne daga jami’an tsaro. Har ma a ranar bikin Nisfu Sha’aban din shekarar 1435 (2014) yake cewa: “Kullum cikin tsallake hari muke daga wadannan miyagun mutanen. Yunkurinsu kullum shi ne ya za a yi su ga sun kashe mu… To, amma ranmu ba shi a hannunsu, yana hannun Allah ne. Allah (T) ne mai rayawa. Da a ce ranmu na hannunsu ne, ai da tuni sun zare. Tun da tuntuni suna ta faman bakin ciki, ga abu ba su so, ga shi yana ta habaka.”

A ranar Juma’ar karshen watan Ramadan, a kokarinsu na murkushe Harkar Musulunci, sojojin Nijeriya sun dira a kan almajiran Shaikh Zakzaky a daidai PZ da ke Zariya, a yayin da suke gudanar da Muzaharar nuna goyon bayan Palasdinawa, inda suka kashe mutane 34, cikin su har da ’ya’yan Shaikh Zakzaky su uku, wadanda sun kama su ne da ransu da lafiyarsu suka tafi da su barikin Basawa, suka kashe su ta hanyar azabtarwa.

Sojoji tun a wannan lokacin sun yi niyyar su samu dama ne da za su ci gaba da kashe-kashe, har su kai ga Shaikh Zakzaky. Shi ya sa ma bayan sun yi wannan kisan-kiyashin, sun ta zura ido su ga ko mabiya Shaikh Zakzaky za su fito Muzahara don yin Allah-wadai da harin, sai su yi amfani da wannan damar wajen ci gaba da kashe su, tare da bi gida-gida suna kisa da sunan suna neman ’yan’uwa Musulmin. A wannan lokacin, sai Shaikh Zakzaky ya hana ’yan’uwa fita don yin komai.

Duk da haka, sai sojojin suka rika yada farfaganda da labaran karya, cewa ’yan’uwa Musulmi suna shirin za su mai da martani ga sojoji a barikinsu. Karyar da ba ta samu wajen zama ba a kwakwalen wadanda suka san Harkar Musulunci a tsawon shekaru fiye da 30 a matsayin tafiyar addini marar tashin hankali ko neman fada da kowa.

A ranar 22 ga Muharram 1436 (14/11/2014), bayan kammala zaman juyayin Ashura, Shaikh Zakzaky ya ba da labari cewa: “Dazun abin da aka ce mana; an tara Sojoji a sansaninsu, an ce masu; Al-Zakzaky zai yi bore, saboda haka su zama cikin shiri komai na iya faruwa. To, me ya kawo sunan Al-Zakzaky kai da kake ‘training?’ Kuma in ya yi bore, ina ruwanka da boren? Na dauka idan ma wani abu ne, ba aikin ’yan sanda ba ne? Sai dai in Dan sanda ya gayyace ka, ka taimaka masa, amma Soja da bindiga an ce masa Al-Zakzaky zai yi bore ya zama cikin shiri, komai na iya faruwa.

“Wannan abin da aka gaya masu dazun ke nan. Kuma aka ce su rike bindigoginsu, yanzu haka bindigogin na hannunsu, kuma suna nan yanzu cikin shiri. Kuma sun shigo (Zariya) motoci ne ba kadan ba. Tun kwanaki suna ta shigowa, har da inda aka ga mota 10 da Turawa zalla, sun shigo sun je barikin Basawa shekaranjiya wancan. Kuma yanzu mota 10, mota 20 duk suna shiga. To, kuma duk ba za mu damu ba. Amma me ya kawo sunan Al-Zakzaky? Da yake shi soja ana masa tarbiyya ne da cewa; su mutanen gari sune abokanan gabansa. Za shi ya yi kisan kai ne kawai.”

Shaikh Zakzaky ya ci gaba da cewa: “To, wala Allah su zama cikin shirin, kila sun shirya suna da wani ‘unit’ wanda zai sa bakin kaya, ya je ya yi ta’addanci, su ce; ‘to, ka gani? Dama mun gaya muku.’ Daga nan kuma sai su shigo gari, su shiga kisan kai.”

Tun daga wannan lokacin, sojoji a karkashin mulkin Jonathan suka rika kai farmaki a kan Shaikh Zakzaky, a kowane lokaci suna da nufin su bude masa wuta, ko dai a kan hanyarsa ko kuma a gidansa. Haka ne ma ya sa wani lokacin sukan shigo cikin unguwar Gyallesu da tsakar dare, amma idan suka ga komai dare unguwar ba ta rabuwa da ’yan’uwa da suke ba da kariya, sai su juya a guje.

Shaikh Zakzaky ya tsallake yunkurin kisa daga gwamnatin Jonathan fiye da sau 30 a lokuta daban-daban. Ta kai ga yakan canza hanya idan aka gano sun yi kwanton-bauna a hanyar da aka saba bi zuwa wajen karatu. Haka aka rika fama har zuwa lokacin da aka samu canjin gwamnati. Ya zama Shugaba kasa Muhammadu Buhari ke mulki a karkashin jam’iyyar APC, a shekarar 2015.

A farko, kamar komai zai tafi lafiya kalau, bayan ’yan watanni da hawansa, musamman bayan da wata tashar ‘satilayit’ mallakar kasar Saudiyya, mai suna WISAL TV, ta fitar da wani rahoto, wanda a cikinsa ta gargadi hukumomin Nijeriya a kan bari da suka yi Shi’a na ya]uwa a kasar, ta kuma yi kira gare su da su dakile yaduwar Shi’ancin, kawai sai aka fara ganin hare-hare a kan ’yan’uwa Musulmi, harin kusa da kisan-kiyashin Zariya shi ne harin bom, da aka turo wasu yara cikin masu Tattakin Arba’in din Imam Husain (AS) daga yankin Kano, wanda ya yi sanadiyyar kashe mutum 23 da jikkata gomomi.

Duk da yake kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin harin, har ma ta yi barazanar murkushe Shi’a, amma Shaikh Zakzaky ya dora alhakin harin ne kan jami’an tsaro, bisa dalilan da ya bayyana a cikin jawabinsa na ranar Arba’in, wanda aka gudanar a ranar Alhamis, 3 ga Disambar 2015.

Ba a samu wata murya daga bangaren gwamnati, ko jami’an tsaro da ta musanta zargin da Shaikh Zakzaky ya yi a wannan lokacin ba, sai kawai martanin da sojoji suka bayar kwanaki tara bayan wannan jawabin, wanda shi ne ‘Kisan-Kiyashin Zariya’.


KISAN-KIYASHIN ZARIYA

A ranar Alhamis, 28 ga Safar 1437, daidai da 10/12/2015, bayan kammala zaman juyayin ranar wafatin Manzon Allah (S), Shaikh Zakzaky ya bayar da sanarwar taron saka tutar Maulud, wanda za a gudanar a yammacin ranar Asabar 1 ga watan Rabi’ul Awwal, 1437 (12/2/2015).

A shekarun da suke gabanin nan, sojoji sun saba gabatar da bikin yaye sabbin kuratan sojojin a Zariya a duk karshen shekara, a ranar Juma’a da safe. Sai dai a wannan shekarar, sai suka mai da shi ranar Asabar 12 ga Disambar 2015, kuma da yammaci, maimako Juma’a da safe kamar yadda suka saba gabatarwa a tsawon shekaru. Wannan ya ba su damar ya zama rana da lokacin bikin nasu ya yi daidai da na taron sauya tutar Mauludi da Harkar Musulunci ta ayyana za ta gabatar a Husainiyyah Bakiyyatullah a wannan ranar.

Harkar Musulunci ba ta yi tunanin dage taronta a wannan ranar ba, ganin cewa wuraren da za a gudanar da taruka biyun ba kusa suke ba, don haka babu wani abu da zai hada masu gudanar da taron sauya tuta da masu yayen sabbin kurata. Kuma su wadannan sun saba yi ne da safe, bikin sanya tuta kuwa ana yi ne wajen karfe 5:00 na yamma.

Sai dai wani abu da ba a yi zato, ko tsammani ba, da misalin karfe 12:15 na ranar Asabar din, wata babban motar Sojoji ta zo ta sauke wasu dandazon kuratan sojoji dauke da makamai, tare da akwatun harsashi, a daidai gaban Husainiyyah Bakiyyatullah. Abin da ya yi matukar ba ’yan’uwan da ke wajen mamaki.

An yi kokarin tuntubar su dalilin kawo su gaban Husainiyyah a daidai wannan lokacin, amma sai suka fara harbi a sama. Daga baya sai suka fara kewaye wajen suna harbi, yayin da ’yan’uwa suka bu}ace su, su matsa daga gaban Husainiyya.

Bayan kamar awa guda da faruwar haka, misalin karfe 1:00nr, sai ga tawagar Janar Tukur Yusuf Buratai ta biyo ta wajen Husainiyyar da sunan wucewa. Kai ka ce tawagar ta Shugaban rundunar sojojin Nijeriya ba ta san abin da ya faru a wannan wajen kimamin awa guda da ta gabata ba, wanda a ka’idar tsaro zai tilasta masu barin bin hanyar da samun wata da babu kowane irin barazana.

Zuwan su, tare da masu daukar hotuna cikin kakin sojoji, sai suka shirya wani abu kamar wasan kwaikwayo. Suka yi fuska, tare da nuna rashin sanin faruwar wani abu da wasu kuratan sojoji suka gabatar a wajen kafin zuwan su. A yayin da wasu ’yan’uwa suka tunkare su don su ji ko da me suka sake dawowa wajen? Sai wasu jami’an tsaro a cikin rigar ’yan’uwa Musulmi (kamar yadda Shugaban DSS na Zariya ya bayyana a gaban JCI cewa akwai mutanensu a cikin ’yan’uwa a wannan ranar a Husainiyyar) suka rima ihu, tare da daddaga sanduna. Nan take sojojin suka bude wuta kan mai uwa-da-wabi.

Bayan bude wutar, tawagar ta Buratai ta wuce, sai wadancan kuratan sojojin da aka kawo da farko suka ci gaba da kewaye Husainiyyah, aka rika maro masu karfi. A yayin da suka bi suka kwashe gawawwakin wadanda suka harba, suna goge jini da harsasan da ke kan hanya.

A shirin rana na BBC a wannan ranar, sai ga hirar Kakakin rundunar soja na wancan lokacin, S.U Kukasheka, inda yake bayyana cewa, an yi kwanton-bauna ga Shugaban rundunar sojoji ne, har ma ya tsallake rijiya da baya. Zargin da nan take Shugaban Jagoran Harkar Musulunci Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya musanta.

Kamar yadda aka gani cikin cikakken bidiyon wannan harin da Harka Musulunci ta saki daga baya, Soja sun ci gaba da kewaye Husainiyyah, tare da harbin duk wanda suka samu a kewayenta, har zuwa marfe 5:00ny, lokacin da Gwamnan Kaduna, Nasiru Ahmad El-Rufa’i ya zo wajen.

Bayan magana da ya yi da Jagororin Sojin, sai ya yi gaba. Wucewarsa ke da wuya suka kara tsananta harbe-harbe a Husainiyyar, tare da yunkurin shiganta ta kowane hali.

Ana cikin wannan halin har shigar dare, da misalin karfe 10:30 na dare, sai ga wasu sojojin sun kawo hari gidan Shaikh Ibraheem Zakzaky da ke unguwar Gyallesu, kilomita kusan biyar daga Husainiyyah Bakiyyatullah.

Zuwan su ke da wuya suka yi burki a daidai Banadeen da ke kan kwanar layin da zai kai mutum gidan Shaikh Zakzaky. Suka bude wuta a wani shagon mai shayi da ’yan’uwa suka taru suna shan shayi. Suka jefa wani abin fashewa a wani shagon, bayan wuta ta kama, sai suka rima amfani da hasken wutar wajen saitawa da harbe duk wanda suka gani a kan wannan layin.

Sojoji sun kwana suna harbi a wannan ranar Asabar 12 ga Disambar 2015 din, har zuwa wayewar garin Lahadi, inda suka kashe duk wani mutum da ke gidan Shaikh Zakzaky da suka hada maza, mata da kananan yara, tare da jikkata saura. Suka kuma watsa fetur a kan gawawwakin ’yan’uwa da kuma masu rauni da ake ajiye su a gidan Harisawa da ke kusa da gidan Shaikh Zakzaky, suka banka masu wuta suka kone murmus. Sannan suka tattaro gawawwakin wadanda suka kashe a kan layi, suka tara su waje guda, suka ba mutanen unguwa damar su caje aljihunsu su debi abin da suke so a jikinsu.

A asubahin ranar Lahadin, aka tura wasu sojojin makabartar Darur-Rahma, wanda ke tare da gine-ginen tarihi da aka yi su don yin fim din tarihin rayuwar Shehu Usman Fodiye, da kuma masallacin da aka gina na miliyoyin kudi a wajen.

Akwai ’yan’uwa da suka fito daga yankin Bauchi da nufin zuwa Gyallesu, amma da yake dare ya yi masu, sai suka yada zango a wajen da nufin safe su mara. Sun kashe duka da wadanda ke kula da wajen. Daga bisani suka banka wa wajen wuta, suka rusa shi.

Sun tsare duk hanyoyin shiga da fita Zariya, suna kamawa da hukunta wadanda suke zargi da zama almajiran Shaikh Zakzaky. A irin haka ne suka tsare motoci biyu a Unguwar Dogarawa da ke dauke ’yan’uwa da suka fito daga Tudun Wadar dankadai, Kano, suka bude masu wuta, suka kashe su duka, suka kwashe su suka kai Asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika, Zariya.

A daidai lokacin suke wannan ta’addancin a Gyallesu da Darur-Rahma, sun rima harba gurneti a kan ginin Husainiyyah, har suka samu dama suka shiga ciki, suka kashe da dama, suka harbi wasu, sannan suka kama su suka wurga a motoci suka tafi da su. Daga nan suka hau rusa ginin Husainiyyar.

Duk da wuta da suka saka wa gidan Shaikh Zakzaky bai fito ya mima masu wuya ba, gidan ya kwana yana ci da wuta, a yayin da ba su samu ganin sa ba sai a ranar Litini 14/12/2015, bayan sun rika saka sifika suna yekuwar cewa yau sun gama da Shi’a, Soja na cewa; “Al-Zakzaky ka fito ka yi saranda, ko mu maka kisan wulamanci.”

Ganin yadda gidan ya mone kurumus, sun dauka duk wanda ke ciki ya kone, don haka sai suka shiga gidan suna balle kofofi, har suka kai ga dakin da Shaikh Zakzaky, iyalansa da wasu almajiransa ke ciki, suka yi masu ruwan wuta.

A nan suka kashe ’ya’yansa guda uku, suka harbe shi a hannayensa da kafarsa da kuma idanunsa guda biyu. Suka kama shi tare da matarsa da ke tare da shi, ita ma cikin raunin harbi, suka fita da su.

Shaikh Zakzaky ya bayyana a wata hirar da ya yi da babban dansa, ta wayar tarho daga inda ake tsare da shi cewa; “Mu aka kawo wa hari, aka bu]e mana wuta, aka harbe mu da bindiga, aka kashe mutane sama da 1,000, ciki har da ’ya’yanmu. Ni da matata an harbe mu, ni an ja ni a kan gawar ’ya’yana ne. Sannan kuma aka kawo mu nan aka kulle duk cikar mu da harsasai a jikinmu. Yanzu haka muna fama da ciwo, duk jikinmu da harsasai.”

Kwanaki biyu bayan hakan, sai Gwamnan Kaduna, Nasiru El-Rufa’i ya umurci Hukumar KASUPDA tare da rakiyar jami’an tsaron Soji da ’yan sanda, suka rika bin duk wani gini da ke da alaka da Shaikh Zakzaky suka rusa shi. Bayan Husainiyyah da suka rusa, sun rusa gine-ginen Darur-Rahma da ke kauyen Dambo, Gidan Shaikh Zakzaky a Gyallesu, Fudiyyah Islamic Center a Dan Magaji da gidan da aka birne Mahaifiyar Shaikh Zakzaky a cikin Zariya.

Kisan-kiyashin Zariya ya yi sanadiyyar kashe ’yan’uwa Musulmi almajiran Shaikh Zakzaky fiye da mutum 1,000, tare da jikkata daruruwa, ciki har da wadanda sojoji suka kona su da ransu, fatar jikinsu ya salbe, Allah bai nufi kwanansu ya kare a sannan ba da kuma wadanda aka binne da ransu. Ya shafe iyalai da dama da suka hada uwa, uba da ’ya’yansu. Ya kuma ci rayukan tsofaffi, kananan yara, mata da samari daliban manyan Jami’o’i.

Tun daga ranar Asabar 14 ga Disambar 2015, wato 1 ga watan Rabi’ul Awwal, 1437, har zuwa yau 1 ga watan Rabi’ul Awwal, 1440, tsawon shekaru uku ke nan gwamnatin Nijeriya na ci gaba da tsare Shaikh Zakzaky da daruruwan almajiransa.

Ku biyo mu don karanta bitar abubuwan da suka biyo baya da abubuwan da suka faru daki-daki a tsawon wadannan shekaru ukun, tun bayan faruwar wannan harin.

No comments:

Post a Comment