January 06, 2019

Shekaru 3 Da Kisan Kiyashin Zariya (4)

Daga Saifullahi M. Kabir

BAYAN HUKUNCIN KOTU

Bayan hukuncin babbar kotun Tarayya da ke Abuja na umurnin sakin Shaikh Zakzaky da maidakinsa Malama Zeenah, da biyan su diyya da sauran sharudda kamar yadda suka gabata, an rika samun kungiyoyi da daidaikun mutane suna jaddada kira ga gwamnatin Nijeriya karkashin Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan ta mutunta umurnin na kotun kasa.

Bayan wannan hukuncin, wani tsohon Shugaban kungiyar Lauyoyin na kasa (NBA), Dakta Olisa Agbakoba, ya yi kira ga gwamnatin Buhari kan ta bi umurnin kotu wajen sakin Shaikh Zakzaky da maidakinsa.

Ya ce; “A matsayinsa na dan kasar nan, El-Zakzaky ya cancanci ’yanci. In kuwa akwai wani dalili na tsare shi, me ya sa ba za a bi umurnin kotu a sake shi ba, alabashi daga baya a kai shi kotu bisa wannan dalilin na daban?”

Shi ma tsohon Shugaban kungiyar Lauyoyin na Lagos, Mista Monday Ubani, ya jaddada cewa; “Wajibi ne gwamnatin Tarayya ta bi umurnin kotun Tarayya a cikin umurnin nata.”

A yayin da shi ma Festus Keyamo, wani fitaccen Lauya a garin Lagos din ya nanata cewa; “In har kotun kasa ta ba da matsaya a kan wani abu, to, wajibi ne gwamnati da al’ummar kasa su bi wannan matsayar.”

A ranar 10/12/2016, kimanin mako guda bayan hukuncin na kotun, kungiyar Lauyoyin ta kasa (NBA) a wajen wani taro da ta gudanar a garin Lagos, ta jaddada kira ga mutunta dokar ta kotu ga gwamnatin Shugaba Buhari.

Shugaban kungiyar, Abubakar Mahmod (SAN), ya bayyana matukar damuwarsu a kan rashin bin umurnin na kotun kasa, inda ya ce; “Ya sabawa duk wata doka a ce gwamnatin kasa ta ki bin umurnin kotu.”

Ya kuma jaddada kira a kan a gaggauta sakin Shaikh Zakzaky da matarsa kamar yadda kotun ta yi umurni. Tare kuma da kira ga mabiya Harkar Musulunci kan su rika mutunta dokoki da hakkokin sauran jama’a.

Wasu daga Lauyoyin Shaikh Ibraheem Zakzaky suna ganawa da manema labarai 

An kuma rika samun sakonnin taya murna ga Harkar Musulunci bisa nasarar da ta samu a yayin da ta kafawa masu zaluntar ta hujja da abin da suka yi imani da shi, kuma ta yi galaba a kansu. Kamar yadda wata kungiya mai suna ‘Mahdi Muslim Community’ da ke Nairobi a kasar Kenya ta fitar da takardar taya murna ga Harkar Musulunci a kan wannan nasarar, ta kuma jaddada kira ga gwamnatin Nijeriya kan ta gaggauta bin umurmin na kotun kasar, a ranar 7/12/2016.

Ganin yadda ake ta kiraye-kiraye ta ko’ina a kan gwamnati ta bi umurnin kotu, kwatsam sai ga wata kungiya da ake kira MURIC, wanda a farkon waki’ar Zariya sune farkon wadanda suka yi Allah-wadai da ta’addancin sojojin a kan ’yan kasa Musulmi, a wannan karon kuma bayan nasarar ’yan’uwa a kotu, sai kungiyar ta fito ta bakin Daraktanta, Farfesa Ishaka Akintola, wai ta bayyana Harkar Musulunci a matsayin kungiyar ’yan tashin hankali.

Sun bayyana hakan ne a ranar 5/12/2016, kwanaki uku bayan hukucin kotun Tarayyar ta Abuja, sai ga gwamnatin Kaduna ta fitar da abin da ta kira ‘White-Paper’, wadda take nuna matsayar gwamnatin Kaduna dangane da sakamakon rahoton JCI da ta kafa don binciken dalilin kisan kiyashin Zariya.

A cikin abin da ta kira ‘White-Paper’ din, gwamnatin Kadunan karkashin Gwamnan Jihar, Nasiru El-Rufa’i, ta bayyana matsayarta kan cewa za su bukaci gwamnatin Tarayya ta damka masu Shaikh Ibraheem Zakzaky don su gurfanar da shi a gaban kotu don su caje shi da laifuka daban-daban da ya aikata wa Jihar Kaduna a tsawon shekaru fiye da 30 na gudanar da Harkar Musulunci.

A nan, sai El-Rufa’i ya yi kunnen-uwar-shegu da kiran da kwamitin binciken na JCI ya yi a cikin rahoton da ya mika masa a ranar 15/7/2016, inda ya bukaci a hukunta Shugaban rundunar sojoji ta 1, ‘GOC 1-Division Army’ da ke Kaduna, Janar Oyebade, wanda shi ne ya jagoranci kashe mutum fiye da 347 da duk abin da ya faru a Zariya ranar 12-14/12/2015.

Kwatsam, ranar 1 ga Janairun 2017, sai ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yayin da yake jawabin sabuwar shekara, ya kira ’yan’uwa Musulmi almajiran Shaikh Zakzaky da sunan ’yan’uwansa. Buhari ya ambaci cewa: “’Yan’uwanmu maza da mata na al’ummar Shi’a”, ya yi kira gare su a kan su kasance masu bin dokokin kasa.

Wannan furucin ya sa al’ummar Nijeriya sun yi caa a kansa ta hanyar mai da masa da martanin cewa shi ya fi kamata ya bi dokar kotun kasa, tunda har yau ba a samu wani laifi kwara daya da wadanda ya kira ’yan Shi’a ko Jagoransu ya aikata, wanda ya sabawa dokar kasar ba, sabanin shi da ya ki bin umurnin kotun kasa tsawon lokaci.

Wannan ya tilasta Kakakinsa, Malam Garba Shehu yin magana a ranar 2/1/2017, a yayin da yake hira da BBC, ya bayyana cewa, al’amarin tsare Shaikh Zakzaky sha’anin Jihar Kaduna ne, ba abin da ya shafi Shugaban kasa da shi. Ya kuma kara da bayyana cewa, wasu mutane sun daukaka kara bisa hukuncin kotun da ta ce a saki Shaikh Zakzaky. Sai dai bai fadi ko su waye mutanen da suka daukaka karar ba.

Ranar 16/1/2017 ne wa’adin da kotun Tarayya ta ba gwamnati kan ta saki Shaikh Zakzaky da matarsa ya cika, a yayin da har zuwa wannan lokacin ba su bi umurnin kotun ba. Sai a ranar 21/1/2-17 jaridar DAILY TRUST ta kawo wani labari daga fadar Shugaban kasa, inda suka bayyana cewa, suna ci gaba da tsare Shaikh Zakzaky ne saboda matsalar tsaro da bukatar jama’a. Suka kuma ce ita matarsa Malama Zeenah ba suna tsare da ita ba ne, tana kula da mai gidan nata ne a inda ake tsare da shi.

Idan ba ku manta ba, a baya mun kawo cewa, a ranar 13/6/2016, Lauyan DSS, Bar. Tijjani ya bayyana a gaban kotu cewa, ba ana tsare da Shaikh Zakzaky ba ne bisa tilasci. Ya ce ana ba shi kariya ne a inda aka aje shi bisa yardarsa. Har ma ya ce DSS sun yi masa maganin raunin da sojoji suka masa na Naira Miliyan 5 da rabi.

A ranar Alhamis, 20/4/2017 kuma, sai ga mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osibanjo ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa, suna ci gaba da tsare Shaikh Zakzaky ne saboda matsalar tsaro. Ya kuma ce sun daukaka kara na hukuncin babban kotun Tarayyar da ta ce a saki Shaikh Zakzaky din.

In mai karatu yana lura, zai ga yadda maganganu suke sassabawa a tsakanin kwanaki daga jami’an gwamnatin, ta yadda suka kasa bayyana takamaiman dalili daya da ya sa suke tsare da Shaikh Zakzaky. Don haka a karshe suka ga ba mafita face kawai su mika Shaikh Zakzaky din zuwa ga gwamnatin Jihar Kaduna, don ta caje shi da kirkirarrun laifuffukan da ta ga dama.

WASU MATAKAN

Cikin matakan da Harkar Musulunci ta bi wajen bayyana zaluncin da aka mata da kuma kokarin samar da adalci daga dokoki da ka’ida na hukunta masu laifin yin wannan kisan kiyashin, kwamitin da ke fafutukar ganin an saki Shaikh Zakzaky da ke karkashin Harkar Musuluci, har ila yau, sun aika da koke zuwa ga Hukumar kare hakkin bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya (United Nations Human Rights Counsil) da ke Geneva, dangane da kisan kiyashin da aka yi a Zariya.

Bayan aikawa da wannan koken, UNHRC da ke Geneva din sun bai wa ‘FreeZakzaky Champaign Committee’ gayyata har sau uku a karo daban-daban, amma sai ofishin jakadancin Switzerland ta hana ‘Visa’ don amsa wannan gayyatar na zuwa ba da bayanai. Daga baya ma ofishin ya sanya takunkumi na tsawon shekaru uku ga Wakilan Kwamitin fafutukar ganin an saki Shaikh Zakzaky din.

Har ila yau, Harkar Musulunci ta shigar da karar duk masu hannu a kisan kiyashin Zariya a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, wato ‘International Criminal Court’ (ICC), wanda izuwa hada wannan rahoton Kotun na ICC ta kammala bincikenta a matakin farko dangane da kisan kiyashin, kuma har ma binciken nasu ya tabbatar da cewa sojojin Nijeriya sun aiwatar da wannan kisan kiyashin a Zariya. Ya zuwa yanzu ana jiran mataki na gaba ne, wanda shi ne kotun ICC din ta ayyana wadanda alhakin wannan kisan kiyashin na Zariya 2015 ya rataya a wuyansu. Daga nan sai matakin tuhumar su da ba da ‘waranti’ na a kama su a gurfanar da su a gabanta a mazauninta da ke Hague a Netherlands.

Harkar Musulunci ta kuma rika shirya Muzaharori a Abuja da sauran garuruwa da kuma gabatar da tarurrukan wayar da kan al’umma da fadakarwa, tare da bayyana zaluncin da aka yi a Zariya, musamman ga ’yan boko da masu rajin kare hakkin bil’adam, inda aka samu da dama suka rika fitowa suna Allah wadai, musamman a kan ci gaban gwamnatin Buhari na yunkurin kawar da Harkar, da auka wa ’yan uwa Musulmi a duk lokacin da suka fito don yin Muzahara ko wani taro da ya shafi addini da fahimtarsu.

Ita kuwa gwamnati a kowane lokaci ba ta da aikin da ya wuce ci gaba da fada da Harkar Musuluncin a matakin Jiha da matakin Tarayya. Tun bayan waki’ar ta Zariya, jami’an tsaro sun ci gaba da auka wa ’yan’uwa a garuruwa daban-daban a lokuta daban-daban, kamar yadda za mu kawo su daki-daki a ci gaban rubutunmu in Allah ya nufa.

No comments:

Post a Comment