BAYAN KISAN KIYASHIN ZARIYA:
Da yammacin ranar Litinin, 14 ga Disambar 2015 ne Shugaban rudunar soja ta 1 ke Kaduna, Manjo-Janar Adeniyi Oyebade ya kira taron manema labarai, inda ya bayyana cewa shi ne ya ba da umurnin a mamaye Husainiyyah Bakiyyatullah, gidan Shaikh Zakzaky da ke Gyallesu da Darur-Rahma. Ya kuma tabbatar da cewa, sun kama Shaikh Zakzaky, tare da matarsa da kuma wasu, kuma Shaikh din yana nan a raye cikin koshin lafiya. Ya yi wa ’yan jaridar alkawarin washegari su zo su gana da shi. Sai dai hakan bai yiwu ba.
’Yan’uwa Musulmi sun fito kan tituna a birane da kauyuka a washegarin wannan ranar don yin Muzaharar Allah-wadai da ta’addancin sojojin, tare da kira a kan su saki Shaikh Zakzaky. ’Yan sanda sun bu]e wa masu wannan Muzaharar wuta a garin Kaduna a ranar Talatar 15/12/2015, inda suka kashe ’yan uwa 13. Bakwai nan take, yayin da mutane shida sun kama su ne suka tafi da su da ransu, suka azabtar da su, sai a ranar Juma’a suka ba da gawawwakinsu aka yi musu jana’iza.
An samu Shahidi na 14, mai suna Shahid Idris Mando, wanda Allah ya karbi rayuwarsa a ranar 17/4/2016 bayan jinya da ya yi na tsawon watanni uku cur na harbin da jami’an ’yan sandan suka masa a yayin wannan Muzaharar ta ranar Talatar bayan waki’ar Zariya.
Ranar Alhamis, 17/12/2015 kafar watsa labarai ta ‘Fars News Agency’, ta ruwaito cewa Sarkin Saudiyyah, Salman Bin Abdul’azin ya kira Shugaban kasar Nijeriya, Muhammadu Buhari don ya yi masa jinjina, tare da bayyana harin kare-dangin da sojojin Nijeriya suka kaddamar a kan ’yan uwa Musulmi mabiya mazhabar Ahlul Baiti (AS) a matsayin daya daga hanyoyin yaki da ta’addanci.
Tsawon kwanaki biyu sojoji suka yi suna aikin kwasar gawawwakin da suka kashe a Gyallesu, inda suka kai wasu dakin ajiye gawa na asibitin Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, suka kuma tafi da wasu Depot dinsu da ke Zariya.
A tsakar daren wannan Alhamis din, 17/12/2015 ne sojoji suka kwashe duk gawawwakin na ’yan’uwa Musulmi suka je suka binne su a ramukan bai-]aya a kauyen Mando da ke bayan garin Kaduna da kuma wasu guraren da ba a iya tantance ina ne ba har yanzu.
Sakataren Gwamnatin jihar Kaduna, Alhaji Lawal Balarabe Abbas, ya bayyana a gaban kwamitin binciken abin da ya faru a Zariya (JCI) da Gwamna Nasiru El-Rufa’i ya kafa ranar Litinin 11/4/2016 cewa, shi da wasu daga jami’an gwamnatin Jihar Kaduna, da suka hada da shi Gwamnan kansa, wasu Sanatoci da kuma Babban Daraktan ofishin kula da harkokin addini na Kaduna, Injiniya Namadi Musa, sun yi zama, inda suka samo izini daga kotu, kuma suka je suka jagoranci Sojoji wajen bizne gawawwakin ’yan’uwa Musulmi da aka kashe a Zariya a ramin bai-daya a kauyen Mando da ke bayan garin Kaduna.
Alhaji Lawal Balarabe ya kuma bayyana a gaban JCI cewa, shi da kansa, tare da Manjo Odundare sun kirga gawawwakin ’yan’uwa Musulmi guda 156 a asibitin ABUTH da ke Zariya, sun kuma kirga wasu gawawwaki guda 191 a Depot din Soji na Zariya, inda suka kwaso su zuwa kauyen Mando, suka bizne su a ramukan bai-daya da aka haka bisa taimakon sojoji guda 40. Aikin wanda ya ce sun fara shi da tsakar dare ya dauke su tsawon awanni kafin su kammala. Nan suka bizne maza da mata, yara da manya a rami guda, ba tare da rarrabewa ba.
Kodayake ba a iya samun cikakken bayani a kan inda sojojin suka bizne gawawwakin da suka yi wa kisan-kiyashin ba, sai a ranar 6 ga Junairun 2016, wasu ’yan’uwa masu bincike suka gano. Jawabin Alhaji Lawal Balarabe a gaban kwamitin ta JCI ya kara tabbatar da gaskiyar abin da ake tsammani a baya.
Da yake kisan-kiyashin na Zariya an yi shi ne bisa kwangilar nufin shafe Harkar Musulunci a Nijeriya da Jagoranta, don haka bayan abin da sojoji suka yi na kashe mutane fiye da 1,000 a ranakun 12-14 ga Disambar, tare da rushe gine-ginen Husainiyyah, Gidan Shaikh Zakzaky da sakawa makabartar Darur-Rahma wuta, sai gwamnatin Jihar Kaduna ta shiga rushe duk wani gini da yake da alaka da Shaikh Zakzaky, ko kuma Harkar Musulunci baki daya a garin Zariya.
A ranar 17 ga Disambar 2015, Gwamnan Kaduna, Nasiru El-Rufa’i ya bayyana a kafafen ya]a labaran Jihar Kaduna, inda ya yi wasu kalamai da suke nuna goyon bayan abin da sojoji suka yi, da kuma tabbatar da cewa hakan an yi shi ne da masaniyar su, da kuma kokarin bata Harkar Musulunci.
Nasiru El-Rufa’i ya yi ikirarin cewa Harkar Musulunci tana takura wa al’umma a Jihar Kaduna a tsawon shekaru 30 ta hanyar rufe manyan hanyoyi a yayin tarukansu, amfani da makarantun gwamnati a yayin Tattakin Imam Husaini (AS), da kuma barazanar kwace wa wadanda suke makwabtaka da su filaye da gidaje. A nan ne ya bayyana cewa Husainiyyah Ba}iyyatullah ma ba bisa izini aka gina ta ba.
Sai dai Harkar Musulunci ta warware dukkan zarge-zargen nasa, a wani rubutu da Shugaban bangaren yada labarai na Harkar ya saka wa hannu. Ya nuna cewa ba su taba kashe hanya, ko hana wasu wucewa ba a yayin tarukansu, har ma suna da jami’an kula da ba da hannu a yayin taruka. Kuma duk inda ake amfani da shi a yayin Tattakin Arba’in, wanda aka fara yin sa a nan kasar shekaru uku da suka gabaci waki’ar, ana neman izinin jami’an kula da wajen. Sannan kuma ya bayyana cewa, Harkar Musulunci ba ta bata kwace wani waje, fili, gida, ko masallaci daga wani, ko wasu ba, kamar yadda ba ta taba yin gini a wani waje ba face ta cika sharuddan Hukumar tsara gine-gine.
Sai dai kamar El-Rufa’i ya yi wannan bayanan ne don ya samu damar ci gaba da rushe gine-ginen da ke da alaka da Shaikh Zakzaky, don haka a tsakanin ranar Lahadi zuwa Talata 20-22/12/2015, ya tura ma’aikatan KASUPDA bisa rakiyar jami’an tsaro suka je suka karasa rushe duk gine-ginen da ke Husainiyyah Bakiyyatullah, da ginin NTC, wanda ya shafe fiye da shekaru 50 (ba a dade da sayensa a hannun masu shi ba wannan abin ya auku). Tare da rushe shagunan da ake ginawa a tsallaken Husainiyyah, wanda su ma Shaikh Zakzaky ya sayi filin ne daga hannun masu shi ba jimawa.
KASUPDA bisa rakiyar jami’an tsaron sun kuma je unguwar dan Magaji da ke Zariya, inda suka rushe ginin Fudiyyah Islamic Center, wanda tsohon waje ne da Harkar Musulunci ta saye shi fiye da shekaru 20 da suka gabata a ginensa, kuma ba a yi komai a wajen ba a yayin harin sojojin. Suka je garzaya unguwar Jushi duk a cikin garin Zariya din, suka rushe wani gida da a cikinsa aka bizne Mahaifiyar Shaikh Ibraheem Zakzaky. Tare da rushe Darur-Rahma a kauyen Dembo, muhallin da ke dauke da makabartar Shahidai, masallaci, dakin taro da kuma gine-ginen tarihi don yin fima-fiman addini.
MUZAHARORIN ALLAH-WADAI
Al’ummar duniya ta kadu sosai da wannan harin ta’addancin da gwamnatin Nijeriya ta tura sojojinta suka yi a kan Shaikh Zakzaky da Harkar Musulunci, don haka aka ri}a samun zanga-zangar lumana (Muzaharori) tare da gangamin Allah-wadai a kusan dukkan manya biranen kasashen duniya.
Tun a daren Asabar, a yayin da sojoji suke gabatar da harin a gidan Shaikh Zakzaky, ’yan’uwa Musulmi a duk manya da kananan garuruwan kasar nan sun rika fitowa Muzaharar Allah-wadai da harin. Haka ma a kasar Birtaniya, yayin da wasu suka bayyana a ofishin jakadancin Nijeriya da ke birnin London, suna kira ga a dakatar da harin ta’addancin da sojojin Nijeriya suke gabatarwa a kan ’yan’uwa Musulmi a Nijeriya.
A ranar Juma’a, 18 ga Disamabar 2015, an gabatar da Muzaharori da gangamin Allah-wadai da aikin sojojin Nijeriya a kan ’yan kasa marasa makami a garuruwa kusan 50 a kasar Pakistan kawai, musamman a manyan biranensu da suka hada da Lahore, Karaci, Islamabad da sauransu.
Haka ma a Indiya, Muzaharorin Allah-wadai da kuma kiran a saki Shaikh Zakzaky ya gudana garuruwa fiye da 20. Haka kuma a Iran, Irak, Newyork, Istanbul, Canada da wasu kasashen Afirka da suka hada da Nijar da Kamaru.
Muzaharori da gangamin kira a saki Shaikh Zakzaky sun rika gudana a tsawon wadannan shekaru ukun, musamman a garuruwan Nijeriya, wanda a farkon wannan shekarar aka fara gabatar da Muzaharar kullum a babban birnin Tarayyar Nijeriya, Abuja.
'Yan uwa a wajen Muzaharar #FreeZakzaky a Abuja
ALLAH-WADAI DAGA KUNGIYOYI DA MUTANE
Kasashe daban-daban, ciki har da kasar Amurka da Iran, da kuma wasu cibiyoyi da manyan kungiyoyi a Nijeriya da suka hada da Majalisar koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Nijeriya (NSCIA), kungiyar Kiristoci ta kasa (CAN), Majalisar Dattijan Nijeriya, kungiyar kwadago ta kasa (NLC), kungiyar fafutukan kafa kasar Biafra (IPOB) da wasunsu, sun yi Allah-wadai da faruwar lamarin, tare da kira a gaggauta bincike a kuma hukunta wadanda suke da laifi a abin da ya faru a Zariya.
Wata kungiya mai suna ‘Socialist Party of Nijeriya’ a ranar 24/12/2015 ta yi kira ga Shugaban sojojin Nijeriya, Janaral Tukur Buratai da ya sauka daga mukaminsa har sai an kammala bincike a kan barnar da sojojin suka yi a karkashin ikonsa. Ta kuma yi Allah-wadai da takurawar da ake wa mabiya Harkar Musulunci, inda ta bayyana haramta zanga-zangar kiran a saki Shaikh Zakzaky da El-Rufa’i ya yi bayan abin da ya faru a matsayin goyon baya ga kisan-kiyashin da sojojin suka yi.
Haka ma kungiyar da ake kira a Turance, ‘Non-profit Making organisation’, sun bayyana takaicinsu a kan rayukan da sojojin suka kashe a Zariya ta hanyar cewa; “Ta kowane yanayi abin da sojojin suka yi ya saba wa ka’idar dokar kasa, ya kuma saba wa kundin tsarin mulkin Nijeriya.”
A yayin da kungiyar Inyamurai ta ‘Igbo Mandate Congress’ ya yi kira ga Shugaban kasa Buhari a kan ya samar da wani Kwamiti da zai ba Shaikh Zakzaky hakuri a kan abin da ya faru a madadin gwamnatinsa.
Daidaikun mutane ma sun rika tir da kisan-kiyashin Zariya, a yayin da tsohon Ministan sufurin jiragen sama na kasa, Femi Fani Kayode, ya bayyana abin da ya faru a Zariya a matsayin shiryayye kuma tsararren abu. Kuma ya yi Allah-wadai da kashe rayukan ’yan kasa marasa makami da kona gidaje da sojoji suka yi a Zariya, tare da tabbatarwa da Buhari da Buratai cewa za su bayyana a gaban kotun hukunta manyan laifuka na Duniya (ICC) ba da jimawa ba.
A wata hirarsa da tashar Talabijin din Channels TV a ranar 22/12/2015, mai rajin kare hamkin bil’adama, kuma Babban Lauya, Mista Femi Falana (SAN), ya nuna matukar takaicinsa a kan yadda jami’an sojoji suka take doka da kafafunsu, suka bude wuta a kan ’yan kasa marasa makami ba bisa ka’ida ba. Inda ya bayyana dole ne gwamnatin Nijeriya ta kama duk wanda ke da hannu a wannan harin ta hukunta shi, ta kuma biya diyyar duk barnar da aka yi na rayuka da dukiya. Sannan ta sanya darussan koyar da sanin hakki da ’yancin dan’adam a cikin kwasa-kwasan da ake koyarwa a makarantun sojoji.
Haka ma Babban Malamin adinin Musulunci, kuma Shehin Darikar Tijjaniya, Shaikh Dahiru Usman Bauchi, ya bayyana zubar da jinin da aka yi a Zariya a matsayin abin da zai jawo wa kasa fushin Allah. Ya kuma yi Allah-wadai da ayyukan sojoji, musamman da yake a daidai lokacin sun kama wasu daga Mahadattan Alkur’ani a Jihar Yobe, sun gana masu azaba, tare da yunwatar da su na tsawon kwanaki.
CI GABAN YUNKURIN GWAMNATI NA SHAFE HARKAR MUSULUNCI
Ganin irin tausayawar da ake ta samu daga kungiyoyi da mutane, tare da Allah-wadai da ake yi da wannan ta’addancin na Sojojin Nijeriya a kan ’yan’uwa Musulmi, sai gwamnatin Buhari ta fara fito da wasu shirye-shirye da tsare-tsare da zai bayyana abin da aka yi a matsayin abin da ya dace, tare da samar da muryoyin da za su nuna goyon baya da cire tausayin al’umma ga iyalai da dangin wadanda aka kashe a Zariya.
A ranar Asabar, 19/12/2015 wasu daga cikin Gwamnonin Arewa, karkashin Shugaban mungiyar Gwamnonin, Kasim Shettima, suka gabatar da zama a Kaduna, inda suka tattauna yadda za su bullowa su taka wa Harkar Musulunci burki a Jihohinsu.
Makonni biyu bayan wannan zaman, a ranar 28/12/2015 kungiyar Limamai da Malamai na Jihar Kaduna a karkashin jagorancin Marigayi Shaikh Usman Abubakar Babantine suka gana da Gwamnan Kaduna, Nasiru El-Rufa’i, inda suka bayyana goyon bayansu a kan fada da yake da wadanda suka kira su da ’yan Shi’a a Jihar Kaduna, suka kuma bayyana masa cewa hakan da yake wani aiki ne ma addinin Musulunci.
Kwanaki kadan bayan wannan zaman, a ranar 14 ga Junairun 2016, shi ma GOC I Division, Manjo-Janar Adeniyi, wanda shi ne ya jagoranci duk hare-haren da sojoji suka yi a Zariya, ya gana da wasu Malaman Wahabiyawa da Limamansu, inda ya yi musu bayani a kan dalilin da ya sa suka yi fada da Harka Islamiyya, da kuma sanar da su abin da sojoji suke bu}atar su sanar da almajirai da mabiyansu. A karshe ya ba su kyautar Naira dubu 500 suka raba a tsakanin su.
Wannan sai ya ba wasu daga Malaman kungiyar Izala, wadanda dama ba su iya boye gabarsu ga Shi’anci ba, damar ganin sun ri}a halatta ta’asar da sojoji, tare da gwamnati suka yi a kan ’yan’uwa Musulmi da bayyana kashe rayuka da barnata dukiyoyin da su Janaral Oyebade suka yi a Zariya a matsayin aikin da addinin Musulunci ke bukata.
A ranar 21/12/2015, Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi ya yi jawabi, inda yake yabawa da kashe rayukan da sojojin suka yi a Zariya, inda ya bayyana shi a matsayin fada da masu zagin Sahabbai. Sarki Sanusi ya ambata cewa, Nijeriya kasa ce da aka gina ta a kan koyarwar Sunnah, don haka ba za su zura ido wasu su rika zagin Sahabbai da matan Manzon Allah (S) suna kallo ba.
Kungiyar Izala, musamman ta bakin shugabanninta, Shaikh Sani Yahaya Jingir, Shaikh Abdullahi Bala Lau da Shaikh Kabiru Gombe sun yi ta wa’azozi suna masu murna da abin da aka yi a Zariya. A rayawarsu, gwamnati ta yi hakan ne don ta murkushe wadanda suka tare masu gaba, ta maishe su manyan Malamai.
Tun bayan kama Shaikh Ibraheem Zakzaky da sojoji suka yi a ranar Litinin 14/12/2015, a ranar Alhamis 17/12/2015 Shugaban rundunar sojojin Nijeriya, Janar Tukur Y. Buratai ya bayyana wa manema labarai cewa sun mika Shaikh din inda ya dace don a hukunta shi. Ba a sake samun labarin halin da Shaikh Zakzaky da matarsa, Malama Zeenah ke ciki ba, sai a ranar 13 ga Junairun 2016, kimanin wata guda cur, a yayin da wani Kwamiti a karkashin Majalisar koli ta Harkokin addinin Musulunci a Nijeriya (NSCIA), wacce ta hada da Farfesa Dahiru Yahya, suka gana da Shaikh din a inda ake tsare da shi a Abuja.
Baya ga matakin Muzahara da addu’a, wadanne matakai ne almajiran Shaikh Zakzaky suka rika bi a tsawon shekaru ukun nan don ganin an tabbatar masu da adalci an saki Jagoransu? Ku biyo mu don jin bitar su.

No comments:
Post a Comment