January 06, 2019

Shekaru 3 Da Kisan Kiyashin Zariya (3)

Daga Saifullahi M. Kabir

HARKA DA MATAKAN SHARI’A

A kokarinta na neman a yi mata adalci daga mummunan ta’addancin da sojojin Nijeriya suka yi na auka wa Jagoranta, rushe duk wani muhalli mallakinsa, kashe kimanin mutane 1,000 daga mabiyansa, da kuma kama shi a tsare ba tare da kwakkwaran dalili ba, Harkar Musulunci ta samar da Lauyoyi a karkashin jagorancin wani babban Lauya, Mr. Femi Falana (SAN), daya daga cikin lauyoyin da suka rika yin kira a kan a yi adalci ta hanyar hukunta masu hannu a rikicin Zariya tun a farkon Waki’ar.

Mr. Femi Falana SAN, na jawabi a wajen wani Muzaharar kira a saki Shaikh Zakzaky a Abuja 

Bayan shafe tsawon lokaci da aka yi Lauyoyin na Harkar Musulunci suna neman damar ganin Shaikh Zakzaky, sai a ranar Juma’a 1/4/2016, kimanin watanni biyar da tsare Shaikh din, sannan hukumomi suka bari Lauyoyin a karkashin Mr. Falana suka gana da shi a karon farko a inda ake tsare da shi a Abuja. Wannan ne ma ya ba Falana damar rubuta takarda a ranar 5/4/2016 ga Daraktan DSS na lokacin, Lawal Daura, a kan neman a bar iyalai da Likitocin wanda suke karewa su rika ganawa da shi.

Daya daga cikin lauyoyin Shaikh Ibraheem Zakzaky, Festus Okoye ya sanar da manema labarai a ranar 13/4/2016 cewa, sun shigar da kara a manyan kotuna guda biyu a Abuja da Kaduna a madadin Shaikh Ibraheem Zakzaky da matarsa, Malama Zeenah Ibrahim, bisa caji daban-daban.

Karan na kotun Babbar kotun Abuja (Federal High Court -6, Abuja), Shaikh Zakzaky da matarsa Malama Zeenah suna karar Antoni-Janar na kasa (AGF), Abubakar Malami, da Daraktan hukumar jami’an tsaron farin kaya (DG, DSS), Lawal Daura, da kuma shugaban hukumar ’yan sanda na kasa (IG).

Masu karan guda biyu, suna neman kotu ta tabbatar musu da hakkokinsu da suka hada da, hakkin rayuwa, hakkin walwala da zirga-zirga, hakkin kare daraja da mutunci, da kuma hakkin rayuwa cikin aminci tare da iyali.

Bisa take wadannan hakkokin da wadanda ake zargin suka yi ga Shaikh Zakzaky da Matarsa, ta hanyar tsare su na tsawon watanni biyar ba tare da likitocinsu, lauyoyinsu ko iyalinsu sun ziyarce su ba, sun bukaci kotun ta sa wadanda suke tsare da sun su biya su diyyar Naira biliyan biyu (2 Billion Naira).

Shi kuwa karar da aka shigar a Kaduna, Shaikh Zakzaky da matarsa Malama Zeenat ne suke karar Antoni-Janar na kasa (AGF), da Sojojin Nijeriya (NA), da Shugaban sojojin Nijeriya, Tukur Buratai, da Hukumar tsaron farin kaya (DSS), da kuma Antoni Janar kuma Kwamishinan shari’a na jihar Kaduna, bisa zargin kai hari a gidansu a ranar 12-14/12/2015, kashe musu ’ya’yansu da almajiransa a gabansu, rusa musu muhallansu da barnata dukiyarsu da kuma kama su a tsare, wanda ya tauye ’yancinsu a matsayinsu na ’yan kasa.

SHARI’AR KOTUN ABUJA

An fara shiga shari’ar da ke kotun Abuja ne a ranar 23/5/2016, a gaban mai shari’a Gabriel Kolawale, inda aka dage zuwa ranar 13/6/2016 sakamakon rashin zuwan wasu daga lauyoyin wadanda ake zargi. A ranar Talatar, 13/6/2016 aka ci gaba da shari’ar, inda lauyan DSS, Barr. Tijjani Gazali ya bayyana wa kotu cewa ba bisa tilasci ake tsare da Shaikh Zakzaky ba, yana tsare ne bisa zabin kansa, kuma su suna tsare shi ne bisa yardarsa don su ba shi kariya.

Gazali ya kuma bayyana wa kotun cewa, a tsawon watannin da ake tsare da Shaikh Zakzaky da Mai dakinsa a wajen DSS, an kashe masa abin da bai gaza Naira miliyan 5.1M ba na magani. A nan ne sai Lauyoyin Shaikh Zakzaky suka bukaci kotun ta ba su lokaci don mai da martani ga ikirarin na lauyan DSS, inda Alkalin ya daga ranar ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 13/7/2016.

Bayan dawowa kotun a ranar 13/7/2016, Lauyoyin Harka sun gabatar da amsa ga ikirarin na Lauyan DSS. Abin da ya tabbata shi ne hatta man injin da ke haska wajen da ake tsare da Shaikh Zakzaky a Abuja, Shaikh din ne ke saya da kudinsa tun sad da aka tsare su. Mai shari’a Kolawaye, ya sake dage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 20/9/2016. Ya bayyana zuwan Alkalai hutu a wannan tsakanin a matsayin dalilin dagewa da nisa.

Kodayake Lauyan Shaikh Zakzaky, Mr. Falana ya nemi kotun ta ci gaba da zaman a cikin hutun, amma Alkalin ya yi watsi da bukatar tasa. Sai dai a ranar 30/8/2016, Falana ya aika wa kotun da wasika, yana mai neman ta ba da dama a kai Shaikh Zakzaky asibiti a kasar waje, sakamakon rashin lafiyar idanunsa da yake kara tsananta.

Bukatar Falana ba ta amsu ba, a yayin da aka dawo kotu a ranar 20/9/2016, nan kuma zaman kotun bai yiwu ba, sakamakon taron da Alkalan manyan kotuna suke yi a wannan ranar a Abuja. Sai aka kuma saka ranar 5/10/2016 a matsayin ranar da za a dawo don ci gaban shari’ar.

A ranar 5/10/2016, Mai Shari’a Gabriel Kolawale, bayan sauraron abubuwan da suka rage, ya bayyana takaicinsa matuka a kan shari’ar, inda ya ce irin wannan take hakkin na dan kasa abin kunya ne ga Nijeriya. Ya nemi da a je a sulhunta tsakanin masu karar da wadanda ake kara kafin ranar 25/11/2016, inda ya ce zai yanke hukunci a wannan ranar ko da ba a sulhunta ba. Ko da ranar 25/11/2016 ta zagayo, ba a yi zaman kotun ba, nan ma Alkalin ya sake kara mako guda, inda ya saka ranar 2/12/2016 a matsayin ranar yanke hukunci.

Ranar 2/12/2016 ne kotun ta yi zamanta na karshe, inda mai shari’a Gabriel Kolawale ya karanta hukunci. Ya bayyana tsare Shaikh Zakzaky da mai dakinsa da ake yi a matsayin haramtacce, wanda ya saba doka. Ya kuma saba wa kundin tsarin mulkin Nijeriya. A madadin kotun, Kolawale ya ba da umurni ga gwamnatin Nijeriya ta gaggauta sakin Shaikh Zakzaky da mai dakinsa, Malama Zeenat a cikin kasa da kwanaki 45 daga ranar wannan hukuncin.

Har ila yau, kotun ta ba da umurnin gwamnatin Nijeriya ta gina wa Shaikh Ibraheem Zakzaky gida a duk jihar da yake bukatar zama a fadin jihohin arewacin Nijeriya, tare kuma da biyan kowannen su, (Shaikh din da Malama Zeenat) diyyar Naira miliyan 25 na haramtaccen tsarewar da aka yi musu, wanda ya kama Naira miliyan 50. Sannan kuma a yayin sakin, Hukumar DSS su mika Shaikh din da Matarsa ga wani babban Dan sanda, su kuma su raka shi zuwa gidan da aka tanadar masa a cikin kasa da awa 24.

SHARI’AR KOTUN KADUNA

Ita kuwa shari’ar Kaduna, wanda aka shigar a High Court, karkashin mai shari’a S.M Shu’aibu, bisa neman hakkokin barnar da aka yi a Zariya, an fara gudanar da zaman kotun ne a ranar 18/5/2016, inda aka dage ta zuwa ranar 7/6/2016 don ci gaba da sauraron karar.

A ranar Alhamis, 7/6/2016, aka koma don ci gaba da shari’ar, inda bayan kammala karanta kara, sai lauyan gwamnati, wato Antoni Janar na Tarayya ya nemi kotun da ta ba su lokaci don nazari da mai da martani ga Karan. Nan aka dage ci gaban sauraron karar zuwa ranar 15/6/2016.

A ranar Alhamis, 15/6/2016 an dawo kotun don ci gaba da shari’ar. Sai dai Babban Lauyan da ke wakiltan Shugaban sojojin Nijeriya bai zo ba, ya turo wani Lauya mai suna Husain Oyebani a matsayin wanda zai wakilce shi. Husaini ya bayyana wa kotu cewa ba zai iya kare shari’ar ba saboda bai yi nazarin ta ba. Sai ya nemi a ba su lokaci don yin nazarin shari’ar. Kotun ta karbi uzurinsa, kuma Alkalin ya dage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 30/6/2017, inda ya gargade su da shiryawa kare karar zuwa wannan ranar.

Ranar 30/6/2017, Lauyan na sojoji kuma mai tsayawa a madadin Tukur Buratai, wato, Mr. Biola Oyebanji ya bayyana a gaban kotun, inda ya bukaci kotun ta kori shari’ar, bisa hujjar cewa shari’ar na kotun Kaduna ta yi kama da ta Abuja da Alkali Kolawale ya yanke hukunci a ranar 2/12/2016.

Mai Shari’an, Sale Musa Shu’aibu, ya bayyana cewa kararrakin guda biyu da aka shigar a Kaduna da wanda aka shigar a Abuja abu ne mabambanta. Ya ce ya nazarci hukuncin da dan’uwansa Alkali Kolawale na babban kotun tarayya ya gabatar a kan neman hakkin tsarewa ba bisa ka’ida ba, da kuma neman ’yancin rayuwa. Kuma ya ga akwai bambanci da wanda yake gabansa. Don haka ya sanya ranar Alhamis, 6/7/2017 a matsayin ranar da zai yanke hukunci.

A ranar 6/7/2017, kwatsam sai Alkali S.M Shu’aibu ya bayyana da sabon al’amari. Inda ya karbi bukatar Lauyan sojoji, ya koma kan ra’ayin cewa kararrakin da aka shigar a kotun Abuja da wanda aka shigar a wannan kotun nasa abu guda ne. Don haka kai tsaye ya yanke hukuncin korar shari’ar gaba daya.

Da yake mai da martani a kan hukuncin na kotun, Shugaban kwamitin fafutukar ganin an saki Shaikh Zakzaky, Malam Abdurrahman Abubakar Yola, a wata takardar manema labarai da ya saka wa hannu a ranar 6/7/2017, ya bayyana bambancin da ke tsakanin karar da aka shigar a kotun Abuja da wanda aka shigar a Kaduna.

Ya ce, a Abuja an yi karar Antoni Janar na kasa, Shugaban DSS, da kuma Shugaban rundunar ’yan sanda na kasa a kan laifin da suka aikata a Abuja na tsare Shaikh Zakzaky da matarsa ba bisa ka’ida ba, da hana su ’yancin walwala. A Kaduna kuwa, an shigar da kara ne na Antoni Janar na kasa (AGF), da Sojojin Nijeriya (NA), da Shugaban sojojin Nijeriya, Tukur Buratai, da Hukumar tsaron farin kaya (DSS), da kuma Antoni Janar kuma Kwamishinan shari’a na jihar Kaduna, su kuma bisa laifin da suka aikata a jihar Kaduna na kai hari ga Shaikh Zakzaky da kama shi ba bisa ka’ida ba, kashe masa ’ya’ya da ’yan uwa da almajirai da kuma rusa masa muhallansa. “Don haka bambancin a bayyane yake,” in ji shi.

Malam Yola ya ce: “Wannan hukuncin ba zai taba karya mana kwarin guiwarmu na ci gaba da neman adalci ta hanyar bin matakan shari’a ba.”

Ya zuwa hada wannan rahoton, mun samu labarin cewa, Lauyoyin na Shaikh Zakzaky sun daukaka karar shari’o’in guda biyu zuwa kotun daukaka kara wato ‘Appeal court’; bisa rashin bin umurnin sakin Shaikh Zakzaky da kotun Abuja ta ba da, da kuma korar karar da kotun Kaduna ta yi bisa hujjar kamanceceniyar shari’un biyu. Sai dai alamu na nuna rashin jin dadin hakan daga hukumar Nijeriya, a yayin da ta kowane hali suke ta kokarin kawo cikas ga fara zaman na kotun daukaka kara a boye.

Ku biyo mu don jin abubuwan da suka biyo bayan yanke hukuncin kotun Tarayya da ke Abuja.

No comments:

Post a Comment