WAKI’O’IN DA SUKA BIYO BAYAN TA ZARIYA
Bayan waki’ar Zariya, wacce ta auku a tsakanin 12-14 ga Disamba, 2015, Gwamnatin Nijeriya ta rika daukar matakai na karfi, baya ga matakan karairayi don kawo karshen Harkar Musulunci da hana ta kowane irin motsi ko da na numfashi.
Yana daga makaman da Harkar Musulunci ke amfani da shi, shi ne su fito kan tituna a garuruwa su yi Muzaharori don bayyana wa Duniya halin da ake ciki, tare da kiran a saki Jagoransu daga haramtacciyar tsarewar da ake masa.
Wannan kuwa shi ne babban abin da Hukumar Nijeriya ta rika fada da shi. Duk sad da aka fito don yin Muzaharar, sai ta turo jami’anta su yi kokarin dakatarwa, a wasu lokutan ma har su bude wuta, su kashe wasu daga almajiran Shaikh Zakzaky.
An yi waki’o’i da dama bayan waki’ar Zariya, wasu a lokutan Muzaharar kiran a saki Shaikh Zakzaky, wasu kuma a wasu munasabobi kamar na Ashura da Tattakin Arba’in din Imam Husaini (AS).
Har ila yau, a wasu waki’o’in jami’an tsaron kan jikkata ’yan uwa ne, a wasu lokuta kuma har ma da kisan rayuka. Zan so in dan kawo wasu daga manya-manyan waki’o’in da suka auku a tsawon wadannan shekaru ukun da suka gabata.
WAKI’AR KADUNA
Waki'ar farko da aka yi a yayin Muzaharar kira a saki Shaikh Zakzaky (FreeZakzaky) a garin Kaduna ne, ranar Talata 15/12/2015, kwana guda bayan kama Malam Zakzaky (H). ’Yan sanda sun bude wuta suka kashe mutum bakwai nan take, suka kuma raunata wasu. Wasu ’yan’uwa shida kuwa, ’yan sanda sun kama, suka tafi da su da ransu ne, suka je suka kashe su. Ba su ba da gawarsu ba sai a ranar Litinin, bayan sun shafe kwanaki shida a hannunsu. Wannan ya sa Shahidan wannan waki’ar suka zama mutum 13. Akwai kuma mutane 10 da aka tsare su a wannan waki’ar, wadanda kotu ta wanke su daga tuhumar da ake yi masu bayan sun kwashe shekaru biyu a tsare.
An kuma samun Shahidi na 14, wato Shahid Idris Mando, wanda ya cika a ranar 17/4/2016, kimanin watanni 5 bayan waki'ar, bayan jinyar da ya sha na harbin da jami’an tsaron suka yi masa. An yi yi jana’izar Shahidai hudu a ranar Alhamis, Juma’a aka kuma yi ta mutum 3. Sauran mutum 6 din sai a ranar Litinin din da aka samu gawawwakinsu aka yi masu jana’iza.
Wannan ne farkon zaluncin da ya biyo bayan waki’ar Zariya. Duk da haka, bayan mako biyu da wannan ta’addancin, a ranar 2/1/2016 wasu matasa sun sake fitowa Muzaharar Free Zakzaky a Kaduna, inda suka faro daga Katsina Roundabout zuwa Leventis a cikin garin na Kaduna.
An ci gaba da gudanar da Muzaharori da tarukan da aka saba gudanarwa na Harkar Musulunci, duk da kuwa wasu ana yi lafiya, wasu kuma ana samun waki’o’i.
'Yan uwa a sahun Muzaharar #FreeZakzaky a Kaduna
TUNAWA DA SHAHIDAN KUDUS, 2016
Abin da ya biyo bayan wannan waki'ar shi ne taron tunawa Shahidan Kudus da aka yi Darur Rahma ranar 25/7/2016, inda Mopol suka zo da dukkan shirinsu na auka wa, suka nemi hana gudanar da taron.
’Yan’uwa ba su fasa ba sai da suka yi addu’o’i da jawabai suka tashi. Bayan an watse suka harba Tiyagas da kokarin kama wasu ’yan’uwa, amma sai Allah (T) ya takaita lamarin.
A shekarar 2017 ma ’yan sandan sun kuma zuwa wajen taron a Darur-Rahma, inda suka harbi mutane hudu bayan an tashi a taron.
Jami'an tsaro na fitowa daga Darur Rahma kafin su dirar ma Yan uwa
YUNKURIN DIRAR WA MASU TATTAKI ZUWA ABUJA
Sai kuma a ranar 6/8/2016, da wasu sojoji suka yi kokarin dira a kan wasu matasa da suka yi Tattaki daga Zariya suka nufi Abuja da nufin kiran a saki Shaikh Zakzaky. Sakamakon ido da aka saka masu a wannan lokacin da takardar manema labarai da Harka ta fitar dangane da mummunan nufin sojojin a kan matasan, sai Allah ya tunkude sharrinsu, sai bai zama waki'a ba, ba su harba ko kama kowa ba. Suka tilasta matasan su juya, amma duk da haka sai da matasan suka san yadda suka yi suka shiga garin Abuja a wannan lokacin a kokarinsu na bayyana wa duniya halin da Shaikh Zakzaky ke ciki.
'Yan uwa na tattaunawa da Sojojin a yayin Tattakin a hanyar Abuja
MUZAHARAR FREE ZAKZAKY A ZARIYA
Alhamis, 11/8/2016 ’yan sanda suka bude wa masu Muzaharar Free Zakzaky wuta da harbi da Tiyagas a daidai Kofar Doka Zariya, suka kama mutum 1, amma ba su harbi kowa da harsashi mai rai ba.
WAKI’AR FARKO A MUZAHARAR ABUJA
Mako biyu bayan hakan, aka kira gagarumar Muzaharar ‘Free Zakzaky’ a Abuja a ranar Alhamis 22/9/2018. A wannan ranar ’yan sanda sun yi ruwan Tiyagas da ma harsashi, sun raunata ’yan’uwa da dama. Sannan suka kama wasu mutum 12. Daga baya suka ba da belin yara biyar a ranar. Mutum bakwai din, wadanda Sistoci guda 3 ne da Burazu 4, sun kai su kurkukun Keffi suka tsare.
'Yan uwa mata da jami'an tsaron suka kama, bayan sun fito daga Kurkuku
Wannan ne karon farko da jami’an tsaro suka fara dira a kan masu Muzahara da harbi a Abuja. Amma Allah bai nufi an samu Shahidi ba.
SOME-SOMEN WAKI’AR ASHURA 2016
Bayan haka aka fara some-somen waki'ar Ashura ta shekarar 2016. Kafin zuwan ranar Ashura din a garin Jos, jami’an tsaron soji sun rika yin barazana ga duk mai tafiya da bakin kaya zuwa wajen zaman juyayin Ashura. Haka ma a Kaduna, jami’an ’yan sanda sun rika bi suna kokarin dakile masu Tattaki zuwa wajen zaman Ashura a tsawon ranekun zaman.
A ranar 9/10/2016, ’yan sanda a Kaduna, sun rika kama ’yan’uwa a hanyoyi daban-daban. Kamar akwai wasu da suka baro Hayin Danmani za su je Markaz, Malam Ahmad Rigasa da iyalansa kananan yara, ’yan sanda suka kama su. Haka ma cikin masu tahowa daga yankin Nasarawa/Barnawa, su Injiniya Mansur Karofi, ’yan sanda sun kama su, bayan sun harba masu Tiyagas a kan hanyar tasu ta zuwa wajen zaman Ashura, sannan suka kai su kotu. Daga nan aka yi gidan kurkuku da su.
Kananan yaran kuwa, sai daga baya aka ba da belin su. A yayin da wata Sista mai suna Malama Salamatu Abdullahi, sai da ta yi kusan wata uku cur a tsare a kurkukun Kaduna kafin kotu ta yarda ta ba da belinta. Sauran mazan kuwa, yanzu haka fiye da shekaru biyu ana tsare da su. Laifinsu kawai shi ne an kama su a kan hanya za su je zaman juyayin Imam Husaini (AS) a lokacin Ashura. An shiga kotu ya kai kusan sau 30 har yau ana dage-dagen shari’ar.
Wasu daga kananan yaran da yan Sandan suka kama
Wani zaluncin sarari dangane da wadannan bayin Allah din shi ne farkon kai su kotu a ranar 10/10/2016, kwana 1 bayan kama su, kotun ta nemi ’yan sanda su gabatar da shaida a kan wadanda suke zargin, amma Sifeton na ’yan sanda mai suna Dogara, wanda kuma shi ne ‘Prosecutor’ din, ya ce suna rokon kotu ta ba su nan da makonni biyu don gabatar da shaidun. Nan kuwa Alkali ya sa aka kai ’yan uwan kurkuku zuwa lokacin da za a koma Shari’ar. Tun daga ran nan suka fara ganin zalunci har yau!
WAKI’AR ASHURA 2016
A ranar Laraba, 12/10/2016 (Ranar Ashura) aka yi waki'o'in Ashura a garuruwan Funtuwa, Kano, Sakkwato, Kaduna da Jos.
A duk garuruwan da aka yi waki’ar, garin Jos ne kawai Allah ya takaita ba a samu Shahidi ba, amma an yi zaluncin da ya kai matuka, wanda ya yi sanadiyyar rushe Markaz din ’yan’uwa na garin da jikkata gomomin ’yan’uwa da kama ’yan’uwa maza da mata, yara da manya kusan mutum 45, aka tsare su a kurkuku na tsawon watanni biyu kafin kotu ta ba da belin su.
A garin Funtuwa ta Jihar Katsina, an samu Shahidai 10 nan take. A yayin da jami’an tsaron suka kama ’yan’uwa kusan 37 aka tsare su tsawon watanni.
Wani Dattijo, daya daga cikin Shahidan Ashura a Funtua
A Kano ma ’yan sandan da kansu suka debo ’yan iskan gari a cikin motocinsu, suka rika kokarin auka wa Muzaharar. Allah bai nufi za a yi waki’a mai tsanani a ran nan ba. Amma daga baya jami’an tsaron sun kashe wani Haris mai lura da zirga-zirgan ababen hawa (Traffic), Shahid Ja’afar Ali.
A garin Sakkwato ma ’yan iskan gari sun kashe wani dan uwa, Shahid Alhaji Farouk Gwadangwaji a wannan ranar ta Ashura, wanda suka kashe shi bayan kammala Muzaharar.
A garin Kaduna ma, sai da aka tashi Muzaharar lafiya, sannan da yamma jami’an tsaron tare da hadin gwiwar ’yan iskan gari suka auka wa ’yan’uwa a Markaz, inda a nan ma aka samu Shahidai 3, sannan kuma suka kona Markaz din. Bayan sun sace kayan cikin ta suka rushe ta, suka kuma je makarantar Fudiyya da ke Layin Kosai suka lalata ta.
Kwanaki uku bayan waki’ar Ashura a garin Kaduna, a ranar 15/10/2016 wasu ’yan’uwa suka je don su share Markaz din da aka rusa, nan take ’yan sanda suka zo da ’yan iskan gari, suka dira a kan ’yan uwan, suka kashe mutum daya nan take, suka jikkata da dama.
Daga nan jami’an tsaron suka kuma raka ’yan iskan gari zuwa unguwar Mu’azu, inda nan ma suka rushe makarantar Fudiyyar unguwar. Suka kuma shiga gidan wani dan’uwa, Sharif Awwal a Kinkanau suka samu karamar yarinya a ciki, suka hau ta da duka, suka ji mata rauni a ka, sannan suka je gidan wani dan’uwa Alhaji Usman shi ma suka lalata shi, suka kwashe kayayyakin da ke ciki.
WAKI’AR TATTAKI 2016
Waki’ar Tattakin Arba’in din Imam Husain (AS) a yankin Kano, ta auku ne a ranar Litinin 14/11/2016, inda ’yan sanda suka tare kan titi a daidai lokacin da masu Tattakin suka zo wani gari da ake kira karfi a Jihar Kano, suka bude wuta. Nan take suka kashe mutanen da har yanzu ba a tabbatar da adadinsu ba, sai dai akalla ana da tabbacin ba su gaza mutum 25 ba.
Jami’an tsaron sun sace gawawwakin wadanda suka kashe sun je sun bizne su a kabarin bai-daya, in ban da mutum 8 da suka ba da gawawwakinsu. Cikin wanda suka kashe har da jaririya ’yar kimanin watanni 8 da haihuwa mai suna Zainabul Kubra.
Jaririya Zainab, daya daga wadanda aka kashe a yayin Tattakin
A wannan waki’ar, ’yan sandan sun kama mutane kusan 90 a farko, suka ba da belin kananan yara daga baya, a yayin da kusan mutum 50 suka shafe tsawon watanni bakwai a kurkukun Kano, kafin kotu ta ba da belin su.
Yayin da yan sanda suke ruwan wuta a kan masu Tattakin Arba'een din
A ranar 5/3/2017 ne Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya furta da bakinsa cewa shi ya ba ’yan sanda umurnin bude wannan wutar da aka yi a kan masu Tattakin da ta jawo rasuwar mutane 25 a lokacin da yake ganawa da wasu Malamai da suka ziyarce shi a gidan gwamnati.
YUNKURIN AUKA WA ’YAN’UWA A SAKKWATO
Ranar Laraba 27/9/2017, Ashurar shekarar 1439 ta rage saura kwanaki kamar hudu, gwamnatin Jihar Sakkwato ta sanar da cewa ta haramta duk wani motsi ko muzahara da ’yan’uwa Musulmi almajiran Shaikh Zakzaky za su gudanar a duk fadin Jihar.
Washegari, Alhamis sai ga ’yan sanda dauke da muggan makamai a karkashin Kwamishinan ’yan sandan Jihar, Muhammad Abdulkadir sun zo Markaz, wadda ke kusa da gidan Shaikh Kasimu Umar. Lokacin da Shehin Malamin ya nufo Markaz din, sun tare shi sun yi magana da shi, ya tabbatar masu da cewa ba wani abu za a yi ba face abin da aka saba gudanarwa na zaman Ashura, sai suka tafi.
Yayin da Shaikh Qaseem ke magana da jami'an tsaron.
Ranar Juma’a sai suka kuma dawowa, suka daidaici lokacin fitowar Shaikh Kasim zuwa Markaz, sai suka bi ta hanyar, inda suka yi kokarin nuna an tare masu hanya ne, nan suka kama wasu ’yan’uwa guda 6, suka kai su State CID, sannan kuma suka girke jami’an tsaro a kowane lungun unguwar har zuwa wayewar gari.
Allah ya takaita lamarin, a yayin da ’yan’uwa suka samu sabati, kuma aka dauki matakan kaucewa duk wani mugun nufinsu, har ya zama ranar 1/10/2017, wanda ta yi daidai da 10/1/1439H, an gudanar da Muzaharar Ashura da asubahin ranar a Sakkwato, kuma an tashi lafiya. Sai dai an kama mutane 4 a garin Bodinga bayan kammala Muzaharar Ashura a garin, ciki har da Na’ibin Wakilin ’yan’uwa na garin, Malam Abubakar Modi. Sai da suka yi watanni hudu da kwana 10 aka sake su.
A ranar Lahadi, 22/10/2017 ’yan sandan sun kuma yunkurin auka wa ’yan’uwa a Sakkwato, inda suka je wajen da aka rufe Muzaharar Free Zakzaky. Da suka tarar an tashi sai suka harba Tiyagas. Daga nan suka nufi Markaz, inda suka tarar ba kowa, sai suka tafi.
A daidai wannan ranar, ’yan sanda sun bude wuta a kan masu Muzahara a Kaduna, inda suka jikkata ’yan uwa da dama, suka kuma kama mutane hudu.
WAKI’AR TATTAKI 2017
Shekara guda bayan wancan aukawar da ’yan sanda suka yi a kan masu Tattakin Arba’in din Imam Husaini (AS) daga yankin Kano, a ranar 5/11/2017 aka fara Tattakin wannan shekarar ta 1439H daga yankin Kano. An taso da misalin karfe 10:00ns daga Kofar Mazugal, aka yi Sallar Zuhuraini a kofar Nasarawa, sannan aka ci gaba da tafiya har inda aka rufe Tattakin a Dangi ‘Roundabout’ gab da wajen da ake ce wa Gadar Lado da nufin washegari za a tashi daga wannan wajen.
Kwatsam! Sai ga ’yan sanda nan sun taho cikin mota 10 a guje, suna zuwa kafin wasu su sauka a motocinsu ma suka fara bude wuta a kan ’yan’uwan da suke wajen ba su gama watsewa ba. Nan suka harbi ’yan uwa masu yawa, aka samu Shahidai guda uku; A’isha Muhammad Azare, Husaina Dauda Nalado Kano da kuma Shahid Umar Ahmad Gano, wanda shi sun tafi da gawarsa ne sai bayan kwanaki 28 suka ba da ita aka yi mata jana’iza.
Da yake an tsara bayan an kammala Tattakin kowane yanki, za a hadu ne a Abuja a yi taron Arba’in a ranar 20 ga Safar din shekarar. A wannan ranar wacce ta dace da 10/11/2017, jami’an tsaro sun kuma bude wuta a kan ’yan uwa masu taron Arba’in din, inda suka jikkata da dama da barkonun tsohuwa.
Za mu ci gaba insha Allah.






No comments:
Post a Comment