February 19, 2019

Shekaru 3 da Kisan-kiyashin Zariya (6)


Daga Saifullahi M. Kabir

WAKI’AR FREE ZAKZAKY A KADUNA DA ABUJA

A ranar 6/1/2018 labari ya iske ’yan’uwa daga dangi da makusantan Shaikh Zakzaky, cewa jikinsa ya tashi sosai har ma yana fuskantar barazanar shanyewar barin jiki! Wannan ya sa hankalin ’yan’uwa ya tashi. A cikin wannan daren na ranar 6/1/2018 aka rika gudanar da Muzaharori a wasu garuruwa, musamman a Bauchi da Kano.

An ci gaba da Muzaharar kira ga gwamnati ta saki Shaikh Zakzaky domin ya je ya nema ma kansa lafiya a safiyar Lahadi, 7/8/2018 a kusan dukkan birane da kauyukan kasar nan.

A wannan ranar ta Lahadi ’yan sanda sun bude wuta a kan masu Muzaharar a Kaduna, inda suka jikkata mutane biyar, har biyu daga cikin su suka samu Shahada; Shahid Muhammad Auwal Kakuri da Shahid Abdulmalik Sani. Shaikh Zango ya jagoranci yi masu janaza washe-gari Litinin a Kaduna.

Litinin 8/1/2018 ne ’yan’uwa suka fara cincirindon shiga Abuja don fara gudanar da Muzaharorin kira a saki Shaikh Zakzaky na sai baba-ta-gani. A wannan ranar ’yan sanda sun bude wa masu muzaharar wuta, inda suka kama wasu, kuma suka jikkata da dama, amma ba a samu Shahidi ba.

Ranar Talata 9/1/2018 ’yan’uwa almajiran Shaikh Zakzaky sun sake fitowa Muzaharar kira a sake shi a tsakiyar garin Abuja. A ran nan ma ’yan sandan sun kuma bude wuta a kan ’yan’uwa, inda suka jikkata da dama, suka kama ’yan’uwa masu yawa. A wannan ranar ne ’yan sanda suka harbi Shaikh Kasim Umar Sakkwato a cinyarsa, wanda bayan jinya da ya sha na tsawon kimanin kusan wata guda, ya yi shahada a ranar 5/2/2017.

Shaikh Saleh Lazare na jagorantar janazar Shaheed Qaseem Umar 

Washegari Laraba 10/1/2018 ’yan’uwa suka sake fitowa don Muzaharar Free Zakzaky a Abuja din. Ran nan ma jami’an tsaron sun bude wuta a kan masu Muzaharar, inda suka datse gaba da bayan Muzaharar, suka rika amfani da wasu mashina suna ratsa cikin ’yan’uwa suna watsa musu Tiyagas, bayan sun galabaitar da su, sai suka fara harbi da harsasai masu rai, inda nan take suka kashe mutum biyu; Shahid Aminu Ibrahim Gashua da kuma Shahid Usman Dunari, wanda shi sai bayan kwanaki 9 da shahadarsa sannan ’yan sanda suka ba da gawarsa aka yi mata janaza. Sun kuma jikkata gomomi a yayin da suka kama ’yan’uwa masu yawa.

Alhamis 11/1/2018 aka ci gaba da Muzaharar, sai dai an tashi lafiya a wannan ranar. Amma a ranar Juma’a 12/1/2018 an yi Muzaharar ne daga Babban masallacin Kasa na Abuja, inda ’yan sanda suka harba Tiyagas a kan masu Muzaharar.

A ci gaba da Muzaharar kullum a garin Abuja don fafutukar ganin an saki Jagoran Harkar Musulunci daga haramtaccen tsarewar da gwamnatin Buhari ke masa, yanzu haka Muzaharar ta kullum, wadda ake kira Fafutukar Abuja ko ‘Abuja Struggle’ a Turance, ta cika shekara guda cur ba tare da fashi ba.

Sai dai kuma, yana daga cikin natijojin wadannan waki’o’in na mako guda a jere, yadda ya zama ranar Asabar 13/1/2018 gwamnatin Nijeriya ta nuna Shaikh Ibraheem Zakzaky a Talabijin, inda ya yi bayani a kan yanayin halin da yake ciki, ya kuma yi godiya ga ’yan Nijeriya da ke yi masa addu’a.

Kodayake sun yayyanke video din (editing), amma dai ya faranta ran masoyansa, ko ba komai ran nan ne karon farko da aka gan shi a ‘Video’ aka ji maganarsa tun bayan kama shi da Sojoji suka yi a ranar 14/12/2015, kimanin shekaru biyu da wata daya tsakanin kamun nasa da nuna shi a farko.

WAKI’O’IN GABAN OFISHIN NHRC

A ranar Litinin 16/4/2018 ’yan sanda suka sake bude wa ’yan’uwa masu Muzaharar kira a saki Shaikh Ibraheem Zakzaky wuta a kusa da ofishin Hukumar Kare Hakkin Dan’adam (NHRC) da ke Abuja. Sun jikkata ’yan’uwa da dama a yayin harbi da Tiyagas, ruwan zafi da kuma harsashi mai rai.

Cikin wadanda suka raunata har da Ahmad Rufa’i Abubakar Dodo, wanda Allah ya kaddara shahadarsa bayan kwana biyu. A ranar 19/4/2018 ya yi Shahada a wani asibiti a garin Kano. A wannan ranar ’yan sanda sun kama ’yan’uwa kusan 100.

An sanya ranar 23/4/2018 ne a matsayin ranar da za a yi jana’izar Shahid Ahmad Rufa’i, inda aka yi Muzahara zuwa Ofishin Hukumar Kare Hakkin na Dan’adam (NHRC) a Abujan, bayan an kai masu koke cewa wannan gawar ’yan sanda sun harbe ta ne a gaban ofishinsu a makon da ya gabata, sun dauki hoton gawar sun yi bayanai, har ma an gudanar da Sallah ga Shahidin. A gaban ofishin Hukumar ’yan sanda suka sake bude wa ’yan uwa wuta, inda suka kama fiye da 100, tare da jikkata gomomi.

WAKI’O’IN KAI SHAIKH ZAKZAKY KOTU

Bayan dawo da Shaikh Zakzaky da matarsa garin Kaduna da kuma gurfanar da su a gaban wata kotu don yi masu haramtacciyar Shari’ar da El-Rufa’i ya shigar da su a madadin gwamnatin Jihar Kaduna, a ranar Laraba 20 ga Yuni, 2018, jajiberin ranar komawa kotu da Shaikh din, ’yan’uwa a Kaduna sun gudanar da gagarumar Muzaharar kira a saki Shaikh Zakzaky din da kuma yin Allah wadai da kai shi wannan kotun, alhali wata kotun ta yi umurni a sake shi tun fiye da shekara guda gwamnati ba ta bi umurnin ba. Nan ’yan sanda suka bude wuta a kan masu Muzaharar, inda suka raunata mutane uku, amma ba a samu Shahidi a wannan ranar ba.

Ranar Alhamis 21/6/2018 aka ayyana don dawowa kotu da ci gaba da shari’ar Shaikh Zakzaky (H), kodayake ba a yi zaman kotun ba, amma ’yan’uwa sun sake fitowa Muzaharar kira a saki Shaikh Zakzaky a garin na Kaduna, inda ’yan sanda suka sake bude wuta, sun shahadantar da mutum 3 masu suna; Shahid Imrana Ringim, Shahid Idris Alhasan Kaduna da kuma Shahid Sagir Adamu (Baba Bauchi), sun kuma jikkata da dama.

’Yan sandan sun tafi da gawar Shahid Sagir suka hada ta da ta wani dan sanda da suka kashe a wannan ranar, suka kai su dakin ajiye gawa a wani asibiti. Har zuwa yanzu (kimanin watanni hudu ke nan) ba su ba da gawarsa an masa jana’iza ba.

WAKI’O’IN RANAR ASHURA 1440/2018

Ranar 20/9/2018 ta dace da ranar Ashura ta shekarar 1440H, ’yan’uwa sun gudanar da Muzaharorin Ashura a dukkan birane da kauyukan kasar nan ciki har da birnin Tarayya Abuja.

Sai dai a Zariya ’yan sanda sun harba Tiyagas a kan masu Muzaharar bayan an tashi, inda suka raunata ’yan’uwa guda hudu. Wasu zauna-gari-banza sun dira a kan masu Muzaharar ta Ashura a garin Suleja, inda suka jikkata wasu mata da kananan yara. Sannan kuma wasu zauna-gari-banzan bisa rakiyar jami’an tsaro sun je da nufin kona Fudiyyar Anchau da Pambeguwa da ke Jihar Kaduna, sun wargaza ta suka tafi.

A Abuja kuwa, jami’an tsaron sun yi mummunan shiri, don kuwa har jami’an da ke kula da tsaron Shugaban kasa (Guards Brigade) sun fito sun rika bin Muzaharar, amma Allah ya nufi an kammala lafiya.

Sai a garin Potiskum da ke Jihar Yobe ne sojoji suka bude wuta bayan an kammala Muzaharar, suka raunata mutane hudu, daya mutumin gari ne, wanda a nan take Allah ya yi masa cikawa, mutum na biyu kuma da suka kashe shi ne Shahid Ali Zakariyya, wanda ya yi shahada bayan jinyar kwanaki 10 da harbin nasa.

WAKI’AR TATTAKI 2018 A ABUJA

Ranar Asabar 27/10/2018 aka fara waki’ar Tattakin Arba’in a garin Abuja. Sojoji sun bude wuta a kan masu Tattakin a daidai gadar Zuba, inda suka kashe mutum 6 a wannan ranar, tare da jikkata da dama.

Litinin 29/10/2018 sojojin suka sake bude wuta a kan masu Tattakin Arba’in ta yankin Maraba, inda suka kashe mutum akalla 40, tare da jikkata fiye da mutum 100.

Wanda ya jagoranci wannan kisan-kiyashin shi ne Kwamandan jami’an tsaro masu kula da fadar Shugaban kasa (Guards Brigade), Birgediya-Janar Musa Yusuf.

Washegari Talata, 30/10/2018, daidai da ranar Arba’in din Imam Husain (AS), gamayyar soja da ’yan sanda suka kuma bude wuta a kan ’yan’uwa a Abuja, suka kashe mutum biyar da jikkata da dama.

A jerin kwanaki uku din nan, an samu Shahidai akalla 49, yayin da fiye da mutum 110 suka jikkata. Sun kuma kama fiye da ’yan’uwa 200 har zuwa yanzu wasu suna tsare.

KARKAREWA

A takaice, wadannan wasu ne daga waki’o’in da na iya taskacewa sun auku a tsawon shekaru uku, tun bayan waki’ar Zariya ta Disambar 2015. Duk wannan yana daga cikin yunkurin gwamnatin Nijeriya karasa kwangilar da ta karbo daga Amurka da Isra’ila da Saudiyya na kokarin ganin bayan Shaikh Zakzaky da kawo karshen Harkar Musulunci a Nijeriya.

Insha Allah a rubutu na gaba za mu duba hannun Saudiyya da gudummawar Malaman Wahabiyawa a cikin wannan Waki’ar ta Zariya da abubuwan da suka biyo bayanta.

No comments:

Post a Comment