February 25, 2019

Shekaru 3 Da Kisan-kiyashin Zariya (7)


Daga Saifullahi M. Kabir

HANNUN WAHABIYAWA A KISAN-KIYASHIN ZARIYA

Waki’ar Zariya ta auku ne da nufin kawar da Shaikh Ibraheem Zakzaky da Da’awarsa baki-daya. Don haka ma tun kafin aukuwarta da kuma abubuwan da suka biyo baya, sun nuna balo-balo cewa akwai cikakkiyar gudummawar wadanda ake kira Wahabiyawa, wato akwai hannun tushen Wahabiyanci, gidan Sarautar Saudi-Arebiya a cikin duk abin da ya faru.

A nan, zan so mu dogara ga wasu abubuwa guda biyar da suka auku kafin, da kuma bayan kisan-kiyashin na Zariya, kamar haka:

1- Rahoton WISAL TV a kan yaduwar Shi’a a Nijeriya.

2- Kashedin Shekau ga Shaikh Zakzaky, da kuma kai mana hari da sunan Boko Haram.

3- Waki’ar Zariya da yabawar Sarkin Saudiyyah.

4- Rahoton AL’ARABIYYA a yayin zuwan Buhari Katar.

5- Rahoton DW na bayanin MBS a kan dakile tasirin Iran a Afirka.

6- Gudummawar Malaman Wahabiyawa/Izala a kan waki’ar.



RAHOTON TASHAR WISAL TV

Watanni kamar uku kafin aukuwar waki’ar Zariya, a cikin watan Satumbar 2015, wani gidan TV mai suna Wisal, mallakin kasar Saudi-Arebiya, sun yi wani ‘documentary’ inda a cikin sa suka nuna hadarin da ke fuskantar Nijeriya na yaduwar Shi’anci da tasirin Iran a tsakanin matasa, ta hannun Shaikh Ibraheem Zakzaky. Inda a marshe suka nuna takaici ga yadda aka kyale hakan na faruwa a masar da tafi ko’ina girma da tattalin arziki a nahiyar Afirka.

Rahoton ya bayyana cewa: “A duk duniya, a yanzu babu wata masa mafi ha]ari kamar Nijeriya, saboda yadda wata sabuwar fahimta ke ya]uwa har ta mamaye Jihohi hudu, wadda a cikin su akwai masu wannan a}idar kimanin mutane miliyan 25.”

Suka ce: “Wannan cutar da ta bulla a Nijeriya ita ce Shi’a, wacce take yaduwa a tsakanin matasa, wadanda suke makarantun boko suna karantar ilimin likitanci, Kanikanci da wasu fannonin na ilimin boko, wanda kuma ana daukar nauyinsu su je su kware a fannoni daban-daban. Wannan ya sa da yawan matasan ba su san ilimin addini ba. Don haka cutar Shi’anci ke yaduwa da gaggawa a tsakanin matasan Nijeriya.”

Suka ci gaba da cewa: “Wani matashi mai suna Ibraheem Yaqoub Zakzaky ne ya buya a bayan wasu abubuwa, kamar kokarin ’yanto Masallacin Qudus daga hannun Yahudawa da goyon bayan raunanan al’ummar da ake zalunta, yana yaudarar mutanen Nijeriya zuwa ga shiga wannan akidar ta Shi’anci.”

Suka ce: “Malamin, wanda aka san shi a matsayin dan tawaye, ana gayyatar sa ya je Iran don a kara masa ilimi a kan akidar Shi’a. Tsayuwarsa wajen yi wa Shi’anci aiki ya sa shi da mabiyansa sun kai ga suna shirya wasu Muzaharori kamar na Qudus da Ashura. Ya samu nasarar yada wannan cutar ne ta hanyar yin abin da ake kira TAQIYYA, wanda hakan ne ya sa jahilai suke bin sa. Da’awarsa ta fara shahara ne a shekarun tamaninoni (1980s), ta kuma ci gaba da yaduwa a 1990s. Abin da ya fi bata rai shi ne yadda Malamai suka kyale, suka yi shiru a yayin da wannan akidar mai hadari take ci gaba da yaduwa.”

Rahoton na Wisal ya ce: “Zakzaky din, ya yi fice a harkokin diflomasiyya, ta kai ga yana tura dalibai zuwa Jami’ar Tehran a Iran su yi karatu su mware a fannoni, har ma sun fara dawowa Nijeriya suna yada Shi’anci a tsakanin mutane.”

Suka ce: “Suna da wata Jarida da ake kira ALMIZAN, wacce ake buga ta da Hausa, wacce take yaduwa a cikin mutane sosai. Tana taimakawa wajen kara yaduwar Shi’anci. Kuma suna da Website na Hausa da Turanci, wanda suke yada manufofinsu. Kuma suna sayen lokaci a gidajen rediyo da talabijin da jaridu, don su yada manufofinsu ga al’umma. Wannan ne ya ba su damar samun alaka da kyakkyawar fahimta da masu bin Darikun Sufaye, suke haduwa don su fuskanci Ahlus Sunnah.”

Bayan kare rahoton, sai suka saka hira da wani mutum mai suna Dakta Muhammad al-Mubarak, inda yake sharhi a kan abin da aka fa]a. A ciki yake cewa: “A shekarar 1979, shekarar da Khumaini ya yi juyin-juya-hali, babu Shi’a ko daya a Afrika. Sam ba su san Shi’a ba kwata-kwata. Afirka nahiyar Musulmi ne. Eh, akwai wasu kasashe da mafiya yawan mutanen cikin su Musulmi ne, akwai kuma wasu da ka]an ne Musulmi din, amma Shi’a, sam ba a san Shi’a ba a nahiyar baki daya. Haka nan abin yake a da yawa daga kasashen Musulmi, kamar Indinosia.”

Al-Mubarak ya ce: “Amma bayan juyin Khumaini a 1979, sai aka fara aikin yada akidar Shi’anci zuwa kasashe daban-daban. Za mu iya gani yanzu, abin mamaki, Shi’a ta mamaye mafi girman kasashen Afirka a yawan mutane da tattalin arziki. Yanzu muna jin hauhawar farashin mabiya Shi’a a Nijeriya.”

Wannan rahoton, wanda muke da ‘video clip’ dinsa, in mutum ya nazarce shi, zai ga cewa Saudiyya tana jin takaicin yaduwar da’awar Shaikh Ibraheem Zakzaky na Harkar Musulunci da yake yi a tsakanin matasan Nijeriya, wanda kuma suna wa Da’awar kallon Shi’anci ne, saboda ganin cewa Jagoran Harkar da mafiya yawan mabiyansa suna bin tafarkin Ahlul Baiti (AS) ne.

Don haka sun nuna a cikin rahoton cewa, akwai bukatar taka wa yaduwar Shi’ancin birki ta kowane hali, a yayin da suke kokarin nuna cewa Harkar Musulunci din, ko abin da suke kira Shi’anci, na daga cikin tasirin juyin-juya-halin Musulunci ta Iran, wacce Amurka, Isra’ila da ita Saudi-Arebiya din suke tsananin gaba da shi.

KASHEDIN SHEKAU DA KAWO HARIN BOM A KAN ’YAN’UWA

Ba a jima da yin wannan rahoton na Saudiyya a kan takaicinsu na ya]uwar Shi’anci a Nijeriya ba, kamar wata guda bayan hakan, a karshen watan Oktoban 2015, sai ga Shugaban wata kungiyar Wahabiyawa da suke kai hare-haren ta’addanci a Arewacin Nijeriya da aka saka wa suna Boko Haram, mai suna Abubakar Shekau yana kashedi ga Shaikh Zakzaky da almajiransa a kan su gaggauta tuba daga Shi’anci.

A cikin garejeren bidiyon na Shekau, ya furta cewa: “’Yan Kaduna! Kai Zakzaky! ’Yan Shi’a, masu TAQIYYA! Ku tuba!”

Ku lura da wasu abubuwa a cikin wannan garejeriyar maganar ta Shekau, ta yadda yake kiran sunan Shaikh Zakzaky gatsai yana cewa ya tuba, alhali a baya Shekau bai taba kama sunan wani Malamin addini a kasar nan ya yi masa kashedi ba.

Kuma ku lura da yadda ya ambaci kalmar TAQIYYA, wannan kalmar da rahoton Wisal TV ya jaddada, cewa wai Shaikh Zakzaky yana yaudarar matasa ne ta hanyar yin TAQIYYA. Bai zama abin la’akari ba, a yayin da kalmomin Shekau suka dace da na Saudiyya?

To, bayan wannan kashedin kuma da wata guda, har ila yau, a karshen watan Nuwambar 2015, sai aka kawo wa ’yan’uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky harin bom a yayin da suke kan hanyarsu na Tattakin juyayin Arba’in din Imam Husaini (AS), daga Kano sun nufo Zariya.

Harin bom ]in da ya ci rayukan almajiran Shaikh Zakzaky kusan mutum 25, an yi nasarar dakile tashin na mutum daya, a yayin da na guda daya ne ya tashi ya kashe wannan adadin. Kwatam sai aka ji a kafafen yada labarai, wai kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin kawo wannan harin.

Sai ya zama kamar wannan ne ma’anar kashedin Shekau ga Shaikh Zakzaky da ’yan Shi’a, a yayin da yake cewa su tuba. Da ba su tuba ba, suka ci gaba da Shi’anci, ga shi ya kawo masu harin kunar bakin wake ma.

Sai dai Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky, a yayin da yake jawabi a wajen rufe taron Arba’in, kwana uku bayan aukuwar harin, ya bayyana cewa ba kowa ke da alhakin kawo harin ba face jami’an tsaron Nijeriya, wa]anda dama suke da alhakin duk abubuwan da ke faruwa a kasar nan da sunan rashin tsaro.

Bayan Shaikh Zakzaky ya dora alhakin harin a kan jami’an tsaron, bisa dalilan da ya bayyana a cikin jawabinsa na ranar Arba’in din, wanda aka gudanar a ranar Alhamis, 3 ga watan Disambar 2015, ba a samu wata murya daga bangaren gwamnati ko jami’an tsaro da ta musanta zargin da Shaikh Zakzaky ya yi a wannan lokacin ba. Sai kawai martanin da sojoji suka bayar kwanaki tara bayan wannan jawabin, wanda shi ne ‘Kisan-Kiyashin Zariya’.

WAKI’AR ZARIYA DA YABAWAR SARKIN SAUDIYYA

Mun riga mun yi bayani a kan waki’ar Zariya tun a babin farko na wannan rubutun, kuma mun kawo yadda wata kafar ya]a labarai ta ‘Pars News Agency’ ta ruwaito a ranar 16/12/2015, kwanaki biyu bayan gama waki’ar ta Zariya, cewa Sarkin Saudiyya, Salman Bin Abdul’azeez ya kira Shugaban kasar Nijeriya, Buhari ya taya shi murna a kan aikin da ya yi na murkushe Harkar Musulunci da sunan wai fada da ta’addanci.

Sarki Salman, ya bayyana kisan-kiyashin Zariya a matsayin yaki da ta’addanci da murkushe ’yan ta’adda. Wanda a rahoton Wisal TV da ya gabata za mu iya gane suna nufin tasirin Iran a Afirka da yaduwar Shi’anci ne suke nufi da Ta’addancin, kamar yadda kuma za mu gani a gaba.

Za mu cigaba insha Allah.

No comments:

Post a Comment