February 19, 2019
An Yi Walimar Cika Shekaru 40 Da Shelanta Harkar Musulunci
Daga Wakilinmu
A wani sabon salon amfani da kafafen sadarwa ta hanyar gudanar da ayyukan alkairi, ’yan’uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky, sun gudanar da walimar cika shekaru 40 da shelanta Harkar Musulunci a zauren Khairul Amal da ke shafin WhatsApps.
Walimar, wacce ta gudana a tsawon kwanaki uku a jere, an fara ta ne daga ranar Juma’a, 19 zuwa Lahadi 21 ga Jimadal Ulan a shekarar 1440BH, inda aka gudanar da abubuwa kala-kala da suka hada da kacici-kacici a kan Tarihin Harkar Musulunci, wanda ya gudana a ranar farko.
A rana ta biyu aka gabatar da jawabi a kan tarihin Harkar Musulunci a tsawon shekaru 40 a takaice. Sannan a ranar karshe aka saurari labarurruka daga dukkanin ’yan uwan da ke zauren a kan yadda suka fahimci Harka har suka tsinci kansu ana tafiyar tare da su.
Yayin jawabinsa dangane da maudu’in ‘Harkar Musulunci A Shekaru 40’, wanda ya gudanar a salon rubutu, Jagoran zauren na Khairul Amal, Saifullahi M. Kabir, ya bayyana tarihin Harkar Musulunci tun daga tushenta, inda ya faro da bayani a kan tarihin Jagoran Harkar, wato Shaikh Ibraheem Zakzaky.
Malam Saifullahi M. Kabir, ya yi bayani a kan tarihin haihuwar Shaikh Zakzaky, wanda ya faru a garin Zariya a shekarar 1953, wanda ya yi daidai da shekarar 1372 Hijiriyya. Da kuma yadda Shaikh din ya taso a gidan Malaman Alkur’ani, don haka ya zama tun yana karami ya shagaltu da karatun Alkur’ani ne da zuwa gona don taya Mahaifinsa aiki, har zuwa lokacin da ya sauke Alkur’ani yana da shekaru 14 da haihuwa. Inda daga nan ya fara karatun littattafai a gaban Malamai har ya karanta duk littattafan da ake karantawa a zaurukan ilimi a wancan lokacin.
Ya ci gaba da cewa, bayan da Shaikh Zakzaky ya karanta fannoni daban-daban na ilimin addini da Luggar Larabci, a shekarar 1969 (lokacin yana da shekaru 16) ne aka saka shi a makaranta Nizamiyya, inda ya fara da wata makaranta ta koyon Larabci a Zariya, wacce ake kira Zaria Provincial School. Bayan shekaru biyu, wato 1969 zuwa 1971, ya kammala ta.
Ya bayyana yadda Shaikh Zakzaky ya ci gaba da yin wata makaranta da ake kira Madarasatul Ulumul Arabiyya (School for Arabic Studies) a Kano, inda ya fara ta daga shekarar 1971 zuwa 1975. Ya ce, a wannan makarantar ne Shaikh din ya rika ware lokaci yana zuwa wasu azuzuwa na daban (Advance Level) yana karantar wasu fannoni na Boko da suka ha]a da English, Literature, Economics, Government, Hausa, Arabiyya da kuma Islamic Studies.
Ya ce, wannan ne ya sa Shaikh Zakzaky a yayin gama makarantar ya rubuta jarabawa kashi biyu; ta Grade II din da yake karatu a kansa da kuma na Advance Level ]in da ya karawa kansa. Kuma duk ya ci su. Don haka fitowar sakamakon a shekarar 1976 ya ba shi damar fara karatun Jami’a kai tsaye ba tare da share fage ba. Ya fara karanta Economic, Government da Sociology. Daga baya sai ya fi kwarewa a Economics, don haka sai ya dauke shi a matsayin ‘course’ dinsa. Ya yi Digiri a bangarensa, inda ya kammala a shekarar 1979.
Da ya shiga bayani a kan farkon Da’awar Harkar Musulunci kuwa, Malam Saifullahi M. Kabir, ya bayyana yadda Shaikh Zakzaky ya samu Jami’a a lokacinsa, akwai mutane wasu masu tunani dangane da makomar kasa kashi biyu; kashin farko sune kungiyar dalibai Kiristoci (FCS), wadanda suke da tunanin cewa tsarin da ke iko da kasar ya yi, don haka da bukatar a inganta shi ne kawai ba tare da sauyi ba.
Kashi na biyu kuma sune masu ra’ayin Kwaminisanci, wadanda suke sukar addini gaba daya, suke kuma sukar addinin Musulunci, musamman kan cewa addini kawai an samar da shi ne ma don a samu damar mulkar mutane.
Ya ce; “Kwaminisawa sun rika sukar addinin Musulunci ta hanyar ba da misali da mulkin wasu Sarakuna da Daulolin Gargajiya ko na Musulunci, irin su Mulkin Banu Umayya da Banul Abbas da irin ta’addancin da Sarakunansu suka yi. Haka ma irin mulkin Sarakunan Gargajiya a nan kasar. Sai suke nuna cewa wannan zaluncin da Sarakuna suka ri}a yi shi ne ma koyarwar addinin Musulunci. Don haka suna ganin ba zai taba yiwuwa addini ya zama tsarin adalci ga rayuwar mutane ba. Har ma suna cewa addinin Musulunci ya kafu, ya yi iko ne a duniya saboda lokacin duniya ba ta waye ba.”
Ya ce, da Shaikh Zakzaky ya riski wa]annan ra’ayoyin, sai ya samar da murya ta uku a karkashin inuwar Kungiyar Dalibai Musulmi (MSS), wanda yake a lokacin shi ne Sakataren kungiyar a Jami’ar Ahmadu Bello, kuma mataimakin Shugabanta na kasa kan harkokin kasashen waje. “Don haka sai ya fara kokarin mai da martani ga Kwaminisawa, ta hanyar wanke addinin Musulunci kan cewa, a kawo inda aka ga zalunci a gwamnatin da Manzon Allah (S) ya kafa. Ya kuma rika tabbatar wa da mutanen Jami’a cewa, komawa ga addinin Musulunci shi ne kadai mafita wajen samun adalci da wadatuwar arziki da samun aminci.
“Shaikh Zakzaky ya tsaya kyam a Jami’a wajen fa]akar da ]alibai da Malamai cewa, Musulunci kammalallen nizamin rayuwa ne ga mutum, addini ne, hanyar rayuwa ne, kuma ‘ideology’ ne a lokaci guda. Kuma a kan asasin adalci da ilimi da hujja aka kafa Musulunci. A yayin da shi Kirista yake ganin cewa Addini daban, rayuwa daban, Musulunci na ganin duk abu guda ne. Kwaminisanci na ganin ana danniya a kawo adalci. To, Shaikh Zakzaky ya tabbatar masu da cewa, ba inda za a samu adalci in ba a Musulunci ba.”
Malam Saifullah ya ce; “Da irin haka ne Shaikh Zakzaky ya fara kira ga komawa ga addinin Musulunci da yunkurin tabbatar da shi ya yi iko a doron kasa ma.”
Ya ce, tun daga wannan lokacin na Jami’a ne Hukuma ta fara daukar matakai a kan Shaikh Zakzaky da kiran da yake yi, wanda hakan ya yi sanadin kama shi a daure tun yana Jami’a a lokacin mulkin soja na Obasanjo, da hana shi takardar shaidar kammala Digirinsa.
Da yake magana a kan yadda Shaikh Zakzaky ya sha gwagwarmaya tun daga farkon al’amari, Saifullahi ya bayyana cewa tun da Shaikh Zakzaky ya shelanta da’awar kira a komawa Musulunci a ranar Asabar 5/4/1980 daidai da 20 ga Jimadal Ula, 1400H, daga nan Hukuma ta fara daukan matakan kama shi ta daure a kurkuku na tsawon shekaru.
Ya kawo jerin kame-kamen da aka wa Shaikh Zakzaky da adadin lokacin da ya yi, tun daga kamun gwamnatin Shagari, wanda aka kama Malam Zakzaky a garin Sakkwato a watan Mayun 1981 zuwa May 1984, sannan aka sake shi.
Ya ce; “Shaikh Zakzaky na kurkukun Shagari ne Buhari ya yi juyin mulki ya hambare Shagari. Don haka Shaikh ]in ya fito ne a lokacin Buhari na mulkin Soja. Wata shida bayan fitowarsa kuma, sai Buhari a lokacin yana yayin kame-kamen mutane ya daure, ya sake kama Shaikh Zakzaky ya daure shi tun a watan Disambar 1984, a lokacin Shaikh din bai jima da aure ba. Don haka ma har aka haifa wa Shaikh Zakzaky yaronsa na farko da aka saka wa suna Muhammad, Shaikh din na tsare a kurkukun Buhari soja. Sai a watan Agustan 1985, bayan an hambare Buhari daga mulki, Shaikh Zakzaky ya fito, bayan ya shafe watanni tara a tsare a kurkuku.”
Ya ci gaba da cewa; “Babangida kuwa ya kama Shaikh Zakzaky ne ya tsare tun a watan Maris din 1987 bayan shekaru biyu, a shekarar 1989, sannan aka sake shi. Daga nan ne kuma ba a sake kama Malam Zakzaky ba sai a lokacin Mulkin Janaral Sani Abacha, wanda ya kama shi a shekarar 1996. Bayan mutuwar Abacha, a shekarar 1999 Shaikh din ya fito a lokacin rikon kwaryar Abdussalami Abubakar.
Ya ce; “A yanzu haka Shaikh Zakzaky ya kasance a tsare tun kimanin shekaru uku da suka gabata, bayan da sojoji suka yi dirar mikiya a kansa, suka kashe iyalai, dangi da almajiransa fiye da 1,000 a Zariya bisa umurnin Shugaban kasa, Muhammadu Buhari.”
Ya bayyana babban darasin da ke cikin bitar tarihi, inda ya ce shi ne don a koyi abubuwan kirki. Ya ce; “Tabbas daga waiwayen tarihin Harkar Musulunci da Jagoranta ’yan’uwa za su koyi dakewa, kamar yadda Shaikh Zakzaky ya iya fuskantar wannan baranaza da jarabawowin a tsawon wa]annan shekarun, amma har yau bai sauya hadafi, ko manufarsa ba.”
A yayin taron, an raba kyaututtukan katin waya, ga wadanda suka lashe gasar kacici-kacici a kan Tarihin Harkar Musulunci, wanda Malam Adamun Adamawa ya jagoranta.
Daga jaridar ALMIZAN ta 26/5/1440
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment