February 26, 2019

Shekaru 3 Da Kisan-kiyashin Zariya (8)


Daga Saifullahi M. Kabir

RAHOTON AL’ARABIYYA TV A YAYIN ZUWAN BUHARI QATAR

Kwatsam sai ga tashar talabijin ta AL-ARABIYYA ta yi wani rahoto a kan ziyarar da Shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari ya kai Qatar, wanda suka dora ‘video’ din rahoton a shafin gidan talabijin din a ranar Talata 1/03/16. Suka yi masa take da “Sabon gargadi daga Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, game da masu yada busharar Shi’anci a Afrika.”

Suka ce: “Buhari ya hangi wani hatsari da ke tunkarowa na yaduwar wata akida mai hatsari, wacce manufarta ita ce, tayar da fitina, raba kan al’umma da kawo hatsaniya.”

Rahoton ya ci gaba da cewa: “Nijeriya wacce take Cibiyar Afrika; ta fi kowace kasa a Nahiyar ta Afirka yawan mutane, wacce ake kiyasta Musulmin cikin ta sun kai miliyan 85. Daga cikin su akwai kasa da miliyan 10 ’yan Shi'a, sauran kuma Musulmi ne mabiya Sunnah.”

Su ci gaba da cewa: “Shi’a ta yadu daga baya (a Nijeriya) ta hannun Ibraheem El-Zakzaky, wanda Iran ta nasabta shi a matsayin Wakilin Hizbullah a Nijeriya. Jami’an tsaro sun kama shi ne a watan Disambar shekarar da ta gabata; bayan sun tuhume shi da yunkurin kashe Shugaban Hafsan Sojojin Nigeria, a lokacin da yake kan hanyarsa ta wucewa Zariya; wacce ake ganin ta a matsayin wuri mafi muhimmanci ga mabiya Shi'a da suke zaune a Arewacin Nijeriya, kuma nan ne mazaunin Shugabanta da ke samun goyon bayan Iran.”

A nan sai suka sanya bidiyon Buhari yana cewa: “Arangamar (ta Zariya) faru ne a lokacin da ya yi kokarin dakatar da tawagar Hafsan-Hafsoshin sojojin Nijeriya. Daga baya Shi’a ta yi karfi. Kuma muna da masaniyar cewa tana samun karfafa da abin da ya yi kama da haka daga Iran”.

Sannan suka ci gaba da sharhi da cewa: “Shugabannin siyasa da sojojin Nijeriya ra’ayinsu ya zo daya a kan cewa Shi’a a Nijeriya - wacce take da goyon bayan Iran – ra’ayinsu daya da kungiyar Boko Haram, wacce ta yi wa Da’esh bai’a.”

Suka ce: “Dalilai da dama ne suka sabbaba yaduwar Shi’a a Nijeriya. Daga cikin su akwai talauci, jahilci, ba da tallafin karatu, (da Shi'a suke badawa) da kuma yaudarar mutane ta hanyar taken ’yanto Masallacin Al-Aqsa. Wadannan dalilan ne ke sa mutane tudadar shiga wannan Mazhabar da Iran ke karfafawa.”

Mai karatu, ka lura da yadda bayanan mutanen nan ke zuwa a tare; yaduwar Shi’anci, tasirin Iran, goyon bayan Iran, da batun TAQIYYA, ko taimakon raunana. Wadannan sune duk abin da suke kokarin su nuna cewa Harkar Musulunci na samu don habakar ta. Kuma shi ne abin da suke kokarin a dakile.

Kuma har ila yau, kalaman Buhari ya nuna maka kai tsaye mai suka yi a Zariya, sun auka wa Shaikh Zakzaky ne da almajiransa, don su dakile yaduwar tasirin Iran a Afirka, musamman a Nijeriya. Amma ba wani abu wai tare hanya ne ya sabbaba kashe mutum 1,000, da kama Shaikh Zakzaky a daure tsawon shekaru da rauni a jikinsa ba, kamar yadda za mu ji daga bakin Yariman Saudiyya a gaba.

Muhammadu Buhari da Malaman Wahabiyawa na Saudiyya da na Nijeriya

RAHOTON DW NA BAYANIN BIN SALMAN KAN DAKILE TASIRIN IRAN A AFIRKA

Sai aka zo, a ranar 24 ga watan Afrilun 2018, sashen Hausa na gidan rediyon DW da ke Jamus ya fitar da rahoton murya, inda Yariman Saudiyya, Muhammad Bin Salman ya furta a sarari cewa su ke da alhakin harin da aka kai wa Shaikh Zakzaky a kokarinsu na dakile karfi da tasirin Iran a Afirka!

Rahoton na DW, ya bayyana cewa: “A wata hira da jaridar TIMES ta Amurka ta yi da Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Muhammad Bin Salman ya ce kasarsa ta kai gouro-ta-kai-mari a Afirka don ganin ta rage tasirin Iran a nahiyar, yadda ya zuwa yanzu ta yi nasarar karya karfin kasar ta Iran a Afirka da kimanin kaso 95 cikin 100.”

A shafinsu na sakar sama, DW, sun rubuta a karkashin wani hoto da suka saka, cewa: “Muhammad Bin Salman ya ce kasarsa (Saudi-Arebiya) ce ta dakushe karfin Ibraheem al-Zakzaky a Nijeriya”

Sannan rahoton nasu ya ci gaba da cewa: “Dakta Zayeed Al-Amri, mamba a Cibiyar tsara dabarun mulki da tunkarar matsaloli na kasar ta Saudiyya, ya yi karin bayani kan manufar Yariman, inda yake cewa ‘abin da Yarima ke nufi a nan shi ne tun bayan da ya ayyana shirinsa na tunkarar makiya, Saudiya ta yi nasarar karya tanadin Iran a Yemen da Somaliya da Djibouti da Sudan, kamar yadda ta lalata yunkurinta na kafa makamanciyar kungiyar Hizbollah a Nijeriya da hana Ibraheem Zakzaky yin juyin mulki a kasar.”

Kafar ta DW, ta kuma ruwaito Dakta Amani al-Taweel ta Cibiyar bincike na Al-Ahram a Masar, inda take cewa: “A gaskiya Saudiyya ba abin da ya fi damunta tamkar yada akidar Wahabiyyanci a Afirka fiye da kulla huldar kasuwanci da alakar diflomasiyya ta ban gishiri, in ba ka manda.”

A wannan rahoton, Muhammad Bin Salman da sauran masu sharhi sun bayyana karara dalilin kisan kiyashin Zariya, cewa kwangila ce ta gidan Sarautar Saudiyya zuwa ga Shugaban Nijeriya da jami’an tsaronta a kan su dakile mata Shaikh Zakzaky da abin da suke kira Shi’anci, a kokarinsu na dakile tasirin Iran a Afirka da kuma karfafar yaduwar akidarsu ta Wahabiyyanci.

GUDUMMAWAR MALAMAN WAHABIYAWA A KAN WAKI’AR

Ya gabata tun a kashi na biyu na wannan jerin rubutun, na kawo yadda Malaman Wahabiyyawa suka rika zame-zame da gwamnati da kuma yin wasu kalamai na nuna farin cikinsu kafin da kuma musamman ma bayan abin da ya faru na kashe wadanda suke kira ’yan Shi’a fiye da 1,000 a Zariya.

Mun kawo yadda a ranar Asabar, 19/12/2015 wasu daga cikin Gwamnonin Arewa, karkashin Kashim Shettima, suka gabatar da zama a Kaduna, inda suka tattauna yadda za su bullowa taka wa Harkar Musulunci burki a Jihohinsu.

Da kuma zaman kungiyar Limamai da Malamai na Jihar Kaduna a ranar 28/12/2015 da suka gana da Nasiru El-Rufa’i, inda suka bayyana goyon bayansu a kan fadan da yake da ’yan Shi’a a Jihar tasa. Suka kuma bayyana masa cewa hakan da yake yi wani aiki ne da addinin Musulunci ke maraba da shi.

Mun kuwa kawo yadda a 14 ga Junairun 2016, shi ma GOC I Division, Manjo-Janar Adeniyi Oyebade, ya gana da wasu Malaman Wahabiyawa da Limamansu, ya yi masu bayani a kan shirin jami’an tsaro a kan Shi’a da kuma gudummawar da ake bu}ata daga Malaman, har ya ba su kyautar Naira dubu 500 su raba.

Mun kawo kuma inda a ranar 21/12/2015, Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi; daya daga cikin masu ra’ayin Wahabiyanci ya yi jawabi, inda yake yaba wa sojoji a kan abin da suka yi, da sunan hakan taimakon Sunnah ne da magance masu zagin Sahabbai.

Kungiyar Izala, musamman ta bakin shugabanninta, Shaikh Sani Yahaya Jingre, Shaikh Abdullahi Bala Lau da Shaikh Kabiru Gombe sun yi ta wa’azozi suna masu murna da abin da aka yi a Zariya.

Wani abu da ban kawo ba a baya shi ne bayanin daya daga cikin Malaman Izala, Shaikh Gero Argungun ya yi a fadar Sarkin Yawuri, Dakta Muhammad Zayyanu Abdullahi, kwanaki kadan bayan kisan kiyashin na Zariya, inda bayan ya gama yin karairayi ga Shi’a da Shi’anci a karshe ya shiga bayyana alakar su da Shugaban kasa, Muhammadu Buhari wajen kokarin magance Shi’anci a Nijeriya.

A cikin ‘audio’ din jawabin nasa, Shaikh Gero ya bayyana cewa: “Iran komai suna iya yi, shi ya sa da suka gayyaci Shugaban kasar Nijeriya, Muhammadu Buhari, muka yi ‘meeting’ tare da shi, muka fada masa ya yi hattara da wadannan mutane. Muka fada masa ka ji, ka ji ka ji (dangane da Shi’a). Ya ce to zai lura. Muka ce to in kuma ka je Iran kar ka sa bakaken kaya, don yana cikin hanyar yaudararsu, za su yi maka hoto su yada wa duniya cewa ai kai mamba ne daga cikin su.”

Gero ya ce: “Duk alkawuran da ya yi mana, da ya je Iran ya cika su, kun gan shi a ‘setilayit’ cikin fararen kaya.” Ya ci gaba da cewa: “Da (Buhari) ya dawo ya kira wasu daga cikin mu da muka yi ‘meeting’ da shi (kan ya tafi), ni ban samu zuwa ba. Ya ce duk abin da kuka fada mana kun rage, ni na je Iran na gani da idona, Wallahi babu Musulunci.”

Mai karatu, ba za mu tambayi kanmu cewa mene ne damuwar Shugaban kasar Nijeriya, kasar da ba ruwanta da Allah da addini, ba ruwanta da me kake bautawa a ka’idarta, da akidar Shi’anci ko Mazhabar Ahlul Baiti (AS)?

Kuma hatta taron da Buhari ya je Iran taro ne na wasu kasashe guda 8 masu arzikin man fetur a duniya ne. Ko da yake ya gana da Shugaban addini na kasar Iran, Sayyid Khamene’i, amma sam ganawarsu ba ta da alaka da Musulunci ko Shi’anci, face ya ba shi shawarwari ne a kan muhimmancin dogaro-da-kai da nisantar kasashe masu yin mulkin-mallaka.

KARKAREWA

Daga abin da ya bayyana ga mai karatu, zai fahimci cewa tabbas waki’ar Zariya da aka dira a kan Shaikh Zakzaky da almajiransa, wani yunkuri ne na kokarin kawar da Harkar Musulunci da abin da suka kira Shi’anci, ko tasirin Iran a Afirka. Ya fi karfin wani wasan kwaikwayo na cewa, wai an tare hanya ne kawai sai hakan ya auku, kuma har yau bai kawo karshe ba!

Don haka ne ma duk abin da suka yi na kokarin ganin bayan Harkar ta Musulunci abu ya ci tura, har yanzu ba su hakura ba. Suna ci gaba da tsare daruruwan almajiran Shaikh Zakzaky, da shi kansa Shaikh din da maidakinsa, duk da cewa babbar Kotun Tarayya a Abuja ta ba da umurnin a sake shi.

Amma sun take dokar, yanzu ma sun komar da shi Kaduna ne sun gurfanar da shi a gaban wata kotu suna masa haramtacciyar shari’a, wacce insha Allah a rubutu na gaba za mu tashi da bayanin yadda aka dawo da Shaikh Zakzaky Kaduna daga Abuja, zuwa yadda ake gudanar da haramtacciyar shari’arsa a wata babbar kotu da ke garin Kaduna din.

No comments:

Post a Comment