March 02, 2019

Shekaru 3 Da Kisan-kiyashin Zariya (9)


Daga Saifullahi M. Kabir

KAFIN DAWO DA SHAIKH ZAKZAKY KADUNA

Tun bayan da kotu ta yi umurnin a saki Shaikh Zakzaky a ranar 2 ga Disambar 2016, inda kotun ta ba da umurnin a saki Shaikh din da mai]akinsa, a cikin kasa da kwanaki 45, kuma a biya su diyyar Naira miliyan 50, tare da gina masu gida a duk Jihar da suka zaba a cikin Jihohin Arewacin Nijeriya, mako guda bayan wannan hukuncin na Kotu, a ranar Juma’a 9/12/2016, kwatsam sai DSS suka je gidan da suke tsare da Shaikh Zakzaky a cikin garin Abuja suna kokarin canza masa wajen da za su ci gaba da tsare shi.

A yayin wayarsa da wasu daga iyalansa a lokacin, Shaikh Zakzaky ya ba da labarin yadda wasu jami’an tsaron suka zo suna kokarin sai sun tashe su a gidan, kan cewa za su komar da su wani gida daban. Sai dai a yayin da suka zo, sam ba su nuna cewa za su canza wajen tsarewa ba ne, sun ce ne ana so ai ma wannan gidan kwaskwarima.

Shaikh Zakzaky ya ce masu; “Ku da kotu ta ce ku sake mu, me zai sa ku zo ku ce za ku canza mana wajen tsarewa? Kuma in ma da gaske za a yi gyara ne, ko fenti a nan gidan, ai ana iya yi muna cikin gidan, illa iyaka ai ma wani bangare, in ya bushe sai mu koma can a sake wa wani bangaren.” Amma dai sai suka dage a kan lallai suna so sai an kwashe kayan su Shaikh din, tare da su an mai da su wani waje saboda nan za a yi gyara.

A ranar Juma’a kwashe kaya da dauke Shaikh Zakzaky bai yiwu ba, sai a ranar Asabar suka kuma dawowa da Yamma a kan cewa lallai DSS DG Lawal Daura ne ya ce, a kwashe kayan a komar da su Malam Zakzaky wani wajen daban, don ci gaba da tsarewa.

Bayan Isha, a wannan daren Asabar 10/12/16 din kuwa, sai suka sake dawowa dauke da bindigogi suka kewaye gidan, sun zo da katuwar mota don kwashe kaya, suka rika hauka, har suka kwashi wasu karikitai suka yi gaba da su.

Dama a wannan lokacin akan ba Shaikh Zakzaky waya duk ranar Asabar da Talata da daddare don su yi waya da danginsu. Amma a wannan ranar, sai suka hana su waya din, sai daga baya aka ba da, inda su Malam suka labarta wa iyalansu, kuma ta sanadin hakan ne ma ’yan’uwa suka san halin da ake ciki, wanda aka rika Muzaharori tun a wannan daren, ba kawai a Nijeriya ba, har a birnin London.

Ranar Lahadi 11/12/16, sai DSS suka aminta Jagora ya tura ’ya’yansa da suke tare da shi su gyara wajen da za a mai da su din. Don haka suka je suka ga wajen suka tsaftace shi, sannan a ranar 12/12/16, shekara daya cif da waki’ar Zariya aka dauke su Shaikh Zakzaky daga inda ake tsare da su a cikin garin Abuja, aka komar da su unguwar jami’an tsaro don ci gaba da tsarewa.

Shaikh Zakzaky da mai]akinsa, Malama Zeenat sun ci gaba da zama a wannan sabon wajen tsarewar har tsawon watanni 17, wato tun daga 12/12/2016 har zuwa ranar 15/5/2018, inda aka dauke su daga Abuja, aka kai su kotu a Kaduna da bakin bindiga.



SHIRYE-SHIRYEN MAIDO DA SHAIKH ZAKZAKY KADUNA

Wani abu tabbatacce shi ne, duk lokacin da ’yan’uwa almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky suka yi wani gagarumin motsi (Muzahara), musamman a birnin Tarayya Abuja na kiran a saki Shaikh din daga haramtacciyar tsarewar da ake masa, jami’an tsaro sun auka musu, ko ba su auka ba, za ka ga wata natija ya biyo bayan hakan.

Wannan a fili yake, mun gani a can baya, yadda suka fito suka nuna Shaikh Zakzaky a TV, yana magana da ’yan jarida, bayan da ’yan’uwa suka kwashe mako guda suna Muzaharori, ana bu]e masu wuta, amma ba su takaita ba a farkon shekarar 2018.

Wasu muhimman abubuwa sun auku a watan Afrilun 2018, wanda ya fara da gagarumar Muzahara da ta gudana a ranar Laraba 11/4/16, inda aka yini a gaban kofar Majalisar Tarayyar Nijeriya, washegari Alhamis kuma aka gudanar da taron tunawa da Shahidan Gwagwarmayar Musulunci, wanda shi ne mafi girman taro da ya gudana a Abuja a lokacin, bayan kammala shi aka yi Muzahara wacce aka rufe ta a gaban ofishin Shari’a na Nijeriya.

Tun daga wannan ranar ne jami’an tsaro, da suka ha]a da ’yan sanda da kuma sojojin da ke tsaron fadar Shugaban kasa (Guards Brigade), suka mamaye filin ‘Unity Fountain’ dauke da muggan makamai, suka dakatar da zaman dirshan din da aka faro tsawon kusan watanni uku, tare da hana duk wani taro a wannan muhallin.

Makon da ya biyo baya, ranar Litinin 16/4/2018, ’yan’uwa suka sake cincirindo suka gudanar da Muzaharar kira a saki Shaikh Zakzaky, inda suka je ofishin Hukumar kare hakkin dan’adam da ke Abuja, sai dai a gaban Hukumar ’yan sanda suka bude wa ’yan’uwa wuta, suka raunata da dama, suka kama fiye da mutum 100, har aka samu Shahidi guda daya; Ahmad Rufa’i Bauchi.

Mutane da kungiyoyi sun ta Allah-wadai da wannan abin, don haka ga alama ita gwamnatin ba ta ji dadin hujumin da duniya ta yi mata na tofin-Allah-tsinen ba, sai kawai kwana biyu bayan nan, a ranar Laraba 18/4/18 gwamnatin Kaduna ta gaggauta shigar da kara a wata babbar kotu a Kaduna, inda take zargin Shaikh Zakzaky, Malama Zeenah da wasu mutum biyu; Malam Yakubu Yahya da Malam Sunusi Abdulkadir da laifuka guda takwas.

Sai dai kuma gwamnatin ba ta bayyana shigar da karar ba a wannan lokacin sai daga baya. A ranar 27/4/2018, Shaikh Zakzaky ya yi waya da babban dansa; Sayyid Muhammad, inda ya ba da labarin yadda Shugaban DSS na lokacin, Lawal Daura ya gana da shi, da kuma abubuwan da suka tattauna.

TATTAUNAWAR SHAIKH ZAKZAKY DA LAWAL DAURA

Shaikh Zakzaky ya labarta cewa a ranar Laraba 25/4/2018 an sanar da shi cewa washegari za su gana da Lawal Daura, don haka ranar Alhamis 26/4/18 tun da sassafe aka dauke su aka kai su muhallin da za su yi ganawar, amma shiru, har zuwa Magriban wannan yinin Lawal Daura bai zo ba. Sai bayan hakan ya zo, ya rika nuna masu isa. Daga karshe ya ce ba zai yiwu a yi ganin a wannan ranar ba, sai dai gobe a komo. Aka mai da su Shaikh inda suke tsare.

Washegari Juma’a aka dawo da su Malam, nan ma Lawal Daura ya kara bata lokaci, sai can da yamma ya zo. A nan ma ya so ya kara dage zaman, amma sai su Malam (H) suka ce ba za su sake zuwa wajen ba in har bai yi maganar da zai yi a lokacin ba. Don haka sai ya yi maganganunsa masu cike da izgili, nuna isa da rainin wayo.

Idan mai karatu ya nemi ‘audio’ din wayar da Shaikh Zakzaky ya yi da Sayyid Muhammad a lokacin, ko kuma ya nemi littafin da Cibiyar wallafa da yada ayyukan Shaikh Zakzaky ta wallafa mai suna ‘Yunkurin kashe Shaikh Zakzaky a tsawon shekaru 10’, zai ga cikakken labarin abin da ya gudana tsakanin Lawal Daura da Shaikh Zakzaky.

Dama kwana biyu kafin zuwan Lawal Daura, Yariman Saudiyya, MBS, ya yi magana, inda ya yi ikirarin da hannunsu a yi wa Shaikh Zakzaky abin da aka masa na yunkurin kawo karshensa da da’awarsa. Don haka a lokacin Shaikh Zakzaky ya fada wa Lawal Daura cewa: “Ka je ka gaya wa wanda ya ba ka ajiyarmu, ya kammala ladansa, in ya dauka kashe mu lada ne, tunda ya kashe mutum sama da dubu, to ya ha]a da mu. Ka ce masa ni da matata a shirye muke, mun shirya mutuwa, saboda haka Bismillah!”

Lawal Daura ya tambayi Shaikh Zakzaky, yanzu idan aka sake shi me zai yi? Ya ce wa Shaikh din. “Saboda akwai wasu masu wani ‘interest’ daban, in ya so sai a fasa wannan.” Sai dai bai fa]i mene ne wannan din da za a fasa din ba, kuma Shaikh Zakzaky bai tambaye shi ko mene ne ba.

Shaikh Zakzaky ya ce masa, zai ci gaba da abin da yake yi ne. “Da can me nake yi? Makamaina tun a da sune ilimi, da hankali da hikima. Kuna so na fita na sa jahilci ne da wauta da hauka? Me kake so na yi? Da can me nake yi wanda yanzu in na fita zan canza? Sai dai in kuna so in na fita zan yi hauka ke nan. Ko kuma ya zama ba ilimi zan sa ba, ko zan dauki makami. Na ce makami na shi ne ilimi da hankali. To sai dai in zan dauki kuma wani makamin ne daban,” in ji Malam Zakzaky.

A nan ne Lawal Daura ya ce wa Shaikh Zakzaky; “Malam na fa san ka tun kana yaro!” Malam ya ce masa; “Tun ina yaro? Ko tun muna yara? Ina ce a 1953 aka haife ka?” Lawal Daura ya ce; “Eh, a watan Agustan 1953.” Sai Malam Zakzaky ya ce masa; “Ni kuma an haife ni a watan Mayun 1953.” Nan Lawal Daura ya ce wa Shaikh Zakzaky; “Eh ka girme ni da watanni uku. To, shi ke nan tun muna yara.”

Nan Shaikh Zakzaky ya ce masa; “To, abin da ka san ni tuntuni dai ina yi, shi nake kai har yanzu. Shekarana 40 ina yi, shi ne kuma nake yi, a kansa kuma nake. Don haka in na fita abin da nake yi tun shekaru 40, shi zan ci gaba da yi.”

A nan Lawal Daura ya samu amsar daga alama ba ita ya so samu daga Shaikh Zakzaky ba. Ya ga cewa tunda Shaikh Zakzaky ya tabbatar masa da cewa zai ci gaba da abin da ya saba ne, bai da alamar fasawa, don haka yanzu ba za a fasa wannan din da yace in ya so sai a fasa shi ba. Wannan din kuwa shi ne kai Shaikh Zakzaky kotu, wanda suka riga suka shigar da kara tun kafin zuwan nasu.

Za mu cigaba.

No comments:

Post a Comment