Daga Saifullahi M Kabir
A cigaba da rubutunmu na wannan nazarin da muka fara, da yake yazo daidai da cewa yau 28 ga watan Safar ne, wanda rana mai kamar yau ne aka Shahadantar da Manzon Allah Muhammad (S), ta hanyar guba da aka dura a cikin tsimi da sunan wai magani aka bashi.
Jiya naje wajen buga irin takardar nan da ake rabawa ‘articles’ mai kunshe da sakon Wafatin Manzon Allah (S), a wajen da ake min aikin, wani ya dauki daya ya zauna ya karance shi tsaf, duk kuwa da yake rubutu ne kanana kuma mai yawa. Kasancewar ‘article’ din ya fi karkata ma bayani akan hana abin rubutu da Umar Dan Khaddabi tare da wasu daga sahabbai suka yi, da kuma bayani akan illar da rashin bada wannan abin rubutun ga Annabi (S) ya jawowa al’ummar Musulmi, kamar dai yadda in mutum yana bibiyan wannan nazarin zai ga mun kawo wasu daga ciki.
To, bayan ya karance tsaf. Sai yace min, Malam kai Dan Shi’a ne, ko kuwa sun kawo maka aikin ‘printing’ ne? Sai nace masa Ni Musulmi ne, me ya faru? Sai yace, takardar nan koda yake abubuwan da suka fada a cikinta gaskiya ne, amma gaskiyar magana akwai matsala a bayyana irin wadannan Hadisan. Sai nace masa, haba dai Malam. In dai Hadisi ne kuma ingantacce ai ban jin da wani matsala a cikin yada shi. Me yasa Malamanmu suka rubuta a littafinsu tun shekaru daruruwa ko ma dubbai in sun san akwai matsala a sanar da al’umma su. Ni ina ganin wannan yada Hadisan Annabi (S) ne, kuma duk mabiyin Sunnah zai yi farin ciki da hakan.
Sai Malamin yace min, baka ganin idan jahilai suka karanta wannan takardar za su iya dena ganin girman Sayyidina Umar? Sai nace masa, Radiyallahu Anh! Lallai dai mai sauki ne hakan, amma ni abin da nake gani shine, mu cire komai da komai tukunna, mu dauko zahirin abin, mu saka a faifai. Sayyadina Umar ya zama Sayyadina Umar ne saboda Manzon Allah (S). Kila da bai bi Annabi (S) da ba ma wanda zai san sunansa. Saboda haka tunda ya samu girman da ake ganinsa da shi saboda Manzon Allah (S), idan ya zama ya sabawa Annabi (S) a wani waje, kana ganin Musulmi mai Imani da Allah da Manzon da baya kuskure, zai goyi bayan Umar ya bar goyon bayan Annabi (S) akan sabawarsu? Yace A’a. Amma ai wannan abin a yi shiru ne da shi tunda ya riga ya faru, kuma su Sahabbai sun fi mu sanin dalilin da yasa suka hana Annabi (S) wannan abin rubutun. Ba gashi an ce ciwo ya masa tsanani ba, kaga ko don tausayawa ma za a iya ce masa ya hutar da kansa ba sai ya yi ba. Ni ina ga saboda wannan ne suka hana a bashi.
Nan nace, Malam kar ka warware imaninka mana. Baka ga sun ce hankalin Annabi (S) ya gushe bane? Wanda yana nufin suna so suce Manzon Allah ya zautu ne zai rubuta musu bata? Alhali yace zai rubuta shiriya ne da in aka rike ba za a taba bacewa ba a bayansa? To idan da gaske Sayyadina Umar da sahabban da suka taya shi hana a ba Annabi abin rubuta shiriya din nan sun yi Imani da Allah da Alkur’anin Allah, ashe ba a cikin Alkur’ani Allah ke cewa: “Abin da Manzo ya zo muku da shi ku rike shi ba, kuma abin da ya hane ku ku hanu ba?” Ashe Allah bai ce akan Annabinsa (S): “Kuma baya furuci bisa son ransa face wahayi da aka masa” ba? Ashe bai kuma ce: “Wanda ya bi Manzo hakika ya bi Allah” ba? Don haka in har sun yi Imani da Alkur’ani wallahi ba za su sabawa Annabi ba.
Nace, Malam idan kuma kace wai tausayawa ne yasa Umar yace ma Annabi zafin ciwo ya galabaitar da shi kar a bashi. Wai hakan yana tausayawa ne gare shi. Nan ma fadin Umar; “Hasbuna Kitabullah”, wato ‘Littafin Allah ya ishe mu’ ya karyata uzurin cewa suna tausayin Annabi ne. Domin kamar suna cewa ne bamu da bukatar Hadisin Annabi (S), ba su bukatar Sunnar Manzon Allah (S), Littafin Allah kawai ya ishe su, ba sai Annabi ya musu Hadisinsa ba. Wanda wannan kuma in muka ma Umar uzuri a kansa to wajibi ne mu ma duk wani Dan Qala-Qato, masu cewa basu yarda da Hadisai ba a yanzu sai Alkur’ani. Sai ya zama Sayyadina Umar ne farkon shugabansu.
Muna cikin maganar nan ne mutumin nan ya tubure aka cewa ni dan Shi’a ne, kuma gakiya da ma ya san ni dan Shi’a ne ba zai tsaya yin magana da ni yana bata lokacinsa ba. “Na zaci dan uwana Musulmi ne, ashe kai dan Shi’a ne. Allah ya shiryeku, ya ganar da ku hanya madaidaiciya.” Yace min. Ba wani jayayya sai nace masa, Amin.
To, labari ya cike mana rubutu yau. Sai nace gaskiyar magana akwai gayar rashin wayewa ga mutum, ya zama kiri-da-muzu ga hujja ana bashi yana bijirewa hujjar. Wani ya taba min magana, yace min, kaga ni ba dan Shi’a bane, amma ina rokonka ka sanar da ni gaskiyar magana, Manzon Allah (S) an kashe shi ne ya yi Shahada ko kuwa ya rasu ne kawai sakamakon rashin lafiya? Sai nace masa, ka nemi Sahihin Bukhari, ka je da shi wajen wani daga cikin Malaman garinku, idan kaje kace ya maka bayani akan Hadisi na 4458 da na 5712 da na 5714 da na 6886 da kuma na 6897. Ya bani labara cewa da yaje, ya budewa Malamin hadisan, sai Malamin ya karanta su kafin ya biya masa, ya koma ga wani ya karanta, ya kuma komawa ga wani ya karanta. Sai yace masa, ‘Yaro, kar ka biyewa wanda suka ce kazo ka karanci wadannan hadisan, ka tafi ka kyale su kawai.’ Karatun da bai masa ba kenan. A lokaci guda sai ya zama hakan da suka yi ne ya sa shi wannan ya fara zargin cewa lallai akwai damuwa kenan.
Idan ka duba Kilabul Magazi, Babin rashin lafiyar Annabi da Wafatinsa, Hadisi na 4458 a cikin Sahihul Bukhari, daya daga cikin matan Annabi (S), tana cewa; Mun yi masa dure a lokacin rashin lafiyarsa. Sai ya daga hannu yana mana nuni akan ‘Kar ku dura min.’ Sai muka ce, ai an sa mare lafiya dama da kin magani. Yayin da ya farka, sai yace; “Ashe ban hane ku a kan kar ku dura min ba?” Sai muka ce, ai kin magani ne kawai kake irin na mare lafiya. Sai yace da mu: “Kar wata a cikinku ta/ya bar wajen nan face ya sha ko ta sha (abin da kuka bani), kuma ina kallo, in banda Abbas, domin shi bai yi tarayya da ku ba.”
Me suka durawa Annabi (S)? Aka ce tsumi ne mai dauke da magani a ciki. Me yasa suka dura masa alhali yana cewa kar su dura masa? Sun sabawa Annabi (S) kenan ko? “Wanda ya bi Manzo hakika ya bi Allah.”, “Abin da Manzo ya zo muku da shi ku rike shi, abin da ya hane ku a kansa ku hau.” Inji Allah (T). Ina ce Manzon Allah (S) yace kar su dura masa!? Me yasa suka dura masa!?
Wata tambayar shine, da yaushe ya daga hannun ya musu nuni da kar su bashi tsimin? Kafin su bada ko? A ruwayar ance; ‘Yayin da ya farka.’ Ya farka daga mene? Kenan da suka bashi ya suma ne ko? Sai bayan da ya farfado sannan yace kar wani ko wata dake dakin su fita face Abbas, domin shi bai san abin da suka kulla ba. Ance Abbas ya shigo ne a lokacin, bashi suka durawa Annabi tsimin.
An kawo irin wannan hadisin har ila yau lamba ta 5712 a cikin Sahihul Bukhari, Kitabud Dibbu, Babul Ludud. Har ila yau, an kuma kawo irin Hadisin a Babin Diyya, Babin ‘Iza asaba kaumin…’ Hadisi na 6897. Kai, ka duba Babin Kisasi tsakanin mace da namiji a karkashin littafin Diyya, za ka ga irin wanna Hadisin na cewa wasu daga matan Manzon Allah (S) sun dura masa abin da suka kira magani alhali yana musu kashedi akan kar su dura masa. Yana nan a hadisi na 6889. Ko me yasa Imamu Bukhari ya kawo wannan Hadisin a babin Kisasin Oho?
To, duk ma ba wadannan ba. Wai me yasa Imamu Bukhari bai karishe mana hadisin ba mu ji yadda ta kaya. Da Manzon Allah (S) yace dole kowacce ta sha ko basu sha ba? Da ya kamata a karishe mana ace kowacce bata fita daga dakin ba sai da aka dura mata. Idan an yi hakan. Ko a nan din ma an saba umurnin Manzon Allah (S) ne?
Muna magana ne da gaskiya. Kuma muna cewa, gaskiyar magana mutane kar su bari a kunkume su a daji. Ya kamata su shigo gari. Mu gane cewa, gaskiyar magana fa wasu da ke kusa da Manzon Allah (S) sun cutar da shi. Kuma ba sau daya ko biyu ba kawai, so da dama suna saba umurninsa ne. Yasha yace ku bani, suce ba za su bada ba. Yace kar ku bani kuma su bashi din. Ya yi su kushe. Ya ki yi su ce don me bai yi ba. Ba kuma ta yadda zai yiwu wadannan da a zahiri suke wa Annabi (S) hakan, mun sani kuma ya zama wai a wajensu za mu karbi addini.
Za mu karbi addininmu ne a wajen wadannan shugabanni goma sha biyun da Manzon Allah (s) yace za su kasance a bayansa. Kamar yadda ya zo a cikin Sahihul Bukhari, Hadisi na 7222 da na 7223, daga Jabir Dan Samura, yace; Na ji Annabi (S) yana cewa: “Shugabanni goma sha biyu za su kasance.” Sai ya fadi wata kalma da ban ji me yace ba. Sai babana yace, Annabi (S) yace ne; “Dukkansu daga Quraishu suke.” Mun yi Imani da cewa wadannan 12 din sune halifofin Manzon Allah (S), kuma na farkonsu shine Imam Ali (AS) na karshensu Imam Mahdi (AS).
Ina kara jajantawa al’ummar Musulmi dangane da zagayowar ranar Shahadar Manzon Allah (S). Insha Allah za mu dora da rubutunmu gwargadon yadda hali ya bada.
No comments:
Post a Comment