Daga Saifullahi M Kabir
Rubutun tsage gaskiya da na faro tun kafin ranar Shahadar Annabi (S), sakamakon yanayoyi sai ya zama ya tsaya kusan wata biyu ban cigaba ba. In ba ku manta ba rubutun ya tsaya ne a kashi na 6, wanda na yi shi a farkon Rabi’ul Auwal, na fara da magana a kan hijirar Manzon Allah (S) da batun ‘Sahibin Annabi’ a kogo yayin hijirar, ko da yake mun yi magana ne sama-sama, sai kuma muka kawo batun yadda karfi da yaji aka kafirta iyayen Annabi (S) ake nuna su a matsayin kafirai kuma mushirikai alhali ba su kasance ba face muminai na gargaru kuma amintattu. To har nace za mu yi magana a kan haihuwar Manzon Allah (S) da yadda aka jirkita labarrurrukan haihuwar don a rage matsayin Annabin (s), sai kuma ya zama har lokacin ya wuce ba mu yi ba. Ina neman afuwan masu bibiyar nazarin.
Yau muna 1 ga Jimadal Ula ne, a cikin irin wannan watan ne ake tunawa tare da gudanar da juyayin shahadar tsokar jikin Manzon Allah (S), Sayyida Fatima (SA).
Da yake an samu ruwayoyi daban-daban a kan hakikanin kwanakin da ke tsakanin Shahadar Manzon Allah (S) wanda ya kasance a ranar 28 ga Safar 11bh, da Shahadar ‘Yarsa Sayyida Zahra (S). Mafi karancin kwanaki shine kwana 40, a yayin da akwai ruwayar da ta nuna cewa tsakaninsu watanni 6 ne (wannan shi ya fi shahara a wajen Ahlussunnah). Sai dai ruwayar da tafi inganci shine cewa Sayyida ta kara kwanaki 75 ko kuma kwanaki 95 bayan wafatin mahaifinta (S). Idan mun dauka kwanaki 75 din ne, shine zai kama ranar 13 ga watan Jimadal Ula. Ko da yake shima a kan yi kokari wajen raya munasabar ya zama an yi kwanaki uku ne a jere, 13, 14 da 15 ga Jimadal Ula din, kila don ya zama an dace da hakikanin kwanaki 75 din daga ranar 28 ga Safar din.
Ba tattauna ranar ne babban muhimmin abu ba a yanzu, tattauna abin da ranar ke kunshe da shi ne muhimmi. Ko da yake wasu suna da ra’ayin cewa ba su san amfanin tattauna abin da ya riga ya faru kuma ma ya wuce ba a yanzu. Har ma wasu kan bada wasu misalai da sam basu dacewa da inda ake aje su, dangane da cutarwar da sarakuna suka yi ma iyalan Manzon Allah (S) a bayan wafatin Annabi (S) din, wasu za ka ji suna cewa; Fada ne da ya faru tsakanin manya guda biyu, kai ina ruwanka!? Har ma su ce; Yanzu idan Babanka da Mamarka suna fada wa za ka tarewa? Wani ya taba fada min hakan, nace masa mai gaskiya zan tare wa mana.
Wai a cewarsu manya guda biyu sune Sahabban da suka yi sarautan Musulmi a bayan wafatin Annabi (S) bisa nadin kansu ga kansu, da kuma tsarkakakkun iyalan gidan Manzon Allah (S) wadannan da Allah (T) ya wajabtawa Sahabbai da duk masu Imani sonsu da bin su da girmama su, ya kuma tsarkake su tsarkakewa. Da wadannan Sahabban suka kwace mulkin al’ummar Annabi (S) daga gidan Annabi (S) suka dankarawa kansu, suka kuma cutar da iyalan Annabi (S) din, cutarwar da tarihi ya kasa boye birbishinsa ta kowane siga. Sai aka zo aka ce, eh an yarda an samu sabani tsakanin Sahabbai da Iyalan Annabi (S), amma ai to misalinsu kama misalin uwa da uba ne gare mu. Don haka tunda haka ne, kai naka kawai kallo, fadan mahaifa. Tambaya; Idan mahaifanka suka saba, kai ba za ka iya sanin wa ke da gaskiya wa ke da laifi ba? Ko ka gane sai ka rufe ido kawai kace su ta shafa? Ba wata hayar daza ka bi wajen gayawa mare gaskiya rashin gaskiyarsa ko ya gyara!?
Ballantana ba ma haka misalin yake ba. Tsakanin Sahabbai da Iyalan Annabi (S), kamar Uwa ne da ‘ya’yanta! Ahlulbait (AS) sune iyaye, sahabbai su ‘ya’yaye ne! Ai a cikin Alkur’ani ne Allah (T) yacewa Manzon Allah (S); “Kace musu bani bukatar wani lada daga gare ku, face soyayya ga makusanta na.” ko? Su wa Manzon Allah (S) zai fadawa hakan? Kace min Sahabbai. Su waye makusantan Manzon Allah (S)? Iyalan gidansa tsarkakan nan da Allah (T) yace ya tsarkake su tsarkakewa. Akwai makusanciyar da ta kai Sayyida Fatima (SA) kusanci da Manzon Allah (S)? Babu. Yauwa, to Sayyadina Abubakar ba Sahabi bane? Ba yana cikin wadanda Allah yasa Manzon Allah (s) ya fada musu cewa su so iyalan Annabin ba? Tambaya! Da ya inganta cewa Sayyida Zahra (S) ta koma ga Allah (T) tana mai fushi da shi, tana mai cewa sai ta kai karansa gaban Manzon Allah (S) a gaban zatin Allah (T) ranar Alkiyama, shin tsabar soyayyar da yake mata ne yasa ta fadi hakan?
Kar kace min ba a yi hakan ba, ai na yi magana a kan hakan a kashi na 3 na wannan nazarin (Tsage Gaskiya 3) ko? Har da bayanin yadda Sayyida Zahra (S) ta ma mijinta wasicci a kan ya bizne ta da daddare, kar ya bari Abubakar ko Umar su sallaci gawanta. Kuma haka aka yi ba su sallatan ba. Malam, soyayyarsu ga Sayyida Zahra (S) yasa ta yi wasicci a kan hakan? Ita wajibi ne su so ta. Shin a ina Allah (T) ya wajabta ita ta so su? Kai ma ba inda aka ce ka bi su balle ita tsokar jikin Manzon Allah (S).
Misalin Sayyida Zahra (SA) a kan dukkan sahabbai kamar uwa ce da ‘ya’yanta. Wanda duk ya bi ta ya yi zaman lafiya da ita, ya rabauta da bin mahaifiyarsa, wanda kuwa duk ya saba da ita har ta yi fushi da shi to yana cikin fushin Allah. Kai wallahi gumma uwar da ta haife ka ta yi fushi da kai a kan Sayyida Zahra (S) ta je wajen Allah (T) tana fushi da kai. Ko ba komai, uwarka na iya fushi da kai a kan son ranta. Amma ita Sayyida Fatima (S) ta samu sheda daga Allah (T) a kan cewa ba za ta taba yin fushi ba face da fushin Allah (T). Kamar dai yadda Mahaifinta yake, fusata shi fusata Allah (T) ne. A baya mun kawo hadisi na 3714 a cikin Sahihul Bukhari, inda aka ruwaito Manzon Allah (S) yana cewa: “Fatima tsokar jikina ce, duk wanda ya fusata ta, ni ya fusata.”
Ga duk wanda bai sani ba ma, idan har ya karanta rubutun nan kashi na 3, ya kuma koma cikin Sahihul Bukhari ya ga hadisan nan da na kawo, sam ba zai min musu a kan cewa sarakuna sun fusata Sayyida Fatima (SA) ba, har ta musu kaura, ta bar kula su har ta koma ga Allah. Ko da yake a kan ce wai saboda sun hana ta gado ne, wanda yake gaskiya ba kawai wannan bane. Shi Fadak dama ba gado bane mallakin Sayyida Zahra (S) ne. Manzon Allah (s) ya bata shi tun yana raye. Sai dai gadon ma sun rike, don haka sai suka yi amfani da hakan suka mai da Fadak ma gado, suka ce kuma ba a cin gadon Annabawa, wai abin da suka bari sadaka ne. Kun ga tunda kuma an haramta cin sadaka ga Annabi da Ahlulbait (AS), shikenan su Sayyida Zahra (S) su zauna a talauce kenan. Wannan ne babban burin masu rike hakkin Ahlulbait (AS).
Amma gaskiyar magana shine cutarwar da tasa Sayyida Zahra (S) ta yi fushi kuma ta furta bara’arta ga sarakunan nan ba kawai saboda sun hana ta Fadak ko wani gadonta bane. A’a cutarwa ce da ta yi sanadiyyar rasa rayuwarta gaba daya ma sakamakon aikinsu.
Da sannu za mu nazarci irin cutarwar da sarakunan Musulmi suka yi ga Sayyida Zahra (S) da mijinta Ali (AS) da ‘ya’yanta (AS) a bayan wafatin Manzon Allah (S) daga littafan Sunnah ba tare da waiwayan na Shi’a ba! Nan za mu ga shin sun nuna soyayya ne ga makusantan Annabi (S) a bayan Annabin ko kuwa kiyayya da gaba da hujumi suka rika zuwa musu da shi.
Daga cikin amfanin tuna irin wadannan har da cewa mutum ya san su wa yake bi a matsayin shugabanninsa. Kar a je Lahira ya ga an yi wuta da wasu kuma shi ya dauke su a matsayin jagororin shiriya ne, ya zo yana tuhuma a kan me yasa suka jagorance shi suna cewa ba su ce ya bi su ba ai. Domin gaskiyar magana shine tunda ya inganta cewa fushin Sayyida Fatima (S) fushin Annabi ne, kuma fushin Allah ne. kuma ya inganta cewa akwai wasu mutane da Sayyida ta koma ga Allah tana fushi da su, tana mai wasiyya a kan kar ma a bari su ga gawarta, kuma sai ta kai su kara wajen Allah, to wallahil azeem mutanen nan ba zai yiwu Allah ya musu makoma daya da Sayyida Zahra (S) ba! Kuma dai a Lahira in ba wuta ba Aljanna ko? Kuma Allah ba zai saka tsokar Annabi, wacce take fushi da fushinsa take yarda da yarsar sa a inda ba Aljanna ba. Ba kuma zai saka wadanda suka cutar da ita har ta yi shelar cewa ta yi fushi da su a Aljanna ba.
A ranar Lahira, wadannan sahabban da za a kada su wuta kamar yadda na kawo ruwayoyin a kashi na 5 na wanna rubutun daga Annabi (S), na gaba a cikinsu su ne wadanda suka cutar da Sayyida Zahra (S) har ta koma ga Allah tana fushi da su. Wallahi babu wani da ya canza wasiccin Annabi (addininsa) fiye da su. Tabbas Mu’awiyya da Yazidu sun bi tafarkinsu ne a aiki! Da ace su ne suka zo a zamanin su Mu’awiyya abin da za su yi kenan, domin wanda ya kashe Hasan da wanda ya kashe Husain (AS) ba zai fi zunubi a kan wanda ya fusata Fatima har ma ya kashe ta ba.
Za mu cigaba insha Allah.
No comments:
Post a Comment