February 11, 2018

Tsage Gaskiya (6)

Daga Saifullahi M Kabir 

Cigaban wannan nazarin zai sauya fasali kadan, kasancewar mun shigo watan da aka haifi fiyayyen halitta, Masoyinmu abin kaunarmu, Muhammad Dan Aminatu da Abdullahi (S). Ko da yake a watan akwai abubuwan da ya kamata ace mun waiwaye su mu ga abubuwa a hakikarsu, musamman abin da ya shafi batun Hijirar Annabi (S) daga Makkah zuwa Madina, wanda ya kasance fitan Annabi (S) daga Makka ya faru ne a ranar 1 ga Rabi’ul Auwal, shekara ta 13 bayan aike.

 Wannan hijirar ce ta kasance silan kafa daular addinin Musulunci a garin Madina, daular da ta fadada har sai da ta mamaye duniya baki daya.

 To, darussan da ke kunshe a cikin wannan Hijirar abubuwa ne da ya kamata ya zama mun yi nazarinsu, tun kama daga dalilin yin hijirar, da kwanciyar Shugaban Muminai a shimfidar Manzon Allah (S) a daren Hijira, da fitan Annabi (S) inda har ya samu dan rakiya masanin hanya, wanda ya amince zai raka Annabi (S) har garin Madina, amma da suka shiga cikin kogo suka ji alamun Kafirai za su gano inda suka buya, sai shi wannan dan rakiyan ya fara damuwa yana bakin ciki, akan me yasa ya yarda ya raka Annabi (S) alhali ana kama su kashe su za a yi?

 Shine kamar yadda Allah (T) yake bamu labari a Alkur’ani, sai Manzon Allah (S) yace ma wannan dan rakiyar nasa; “Kar ka yi bakin ciki, Allah yana tare da mu.” Wato ka bar damuwa ba wani abu da zai same mu, Allah zai kiyaye mu. Wani yana iya cewa, ai Allah (T) yace masa ‘Sahibihi’, wato ‘Sahibinsa’ ne, wanda yake nufin yabo ne na musamman ga wannan dan rakiyar. Sai muce masa ai Allah (T) yace ma Annabi (S) Sahibin Mushirikai ma. Baka ji ba, a yayin da suka cewa Annabi (S) mahaukaci, sai Allah (T) yace musu: “Sahibinku (yana nufin Annabi) ba mahaukaci bane.” Ko a wani wajen yace; “Sahibinku ba batacce bane”? Don haka koma wane ne wannan dan rakiyar, wanda mai bai inganta cewa wanda ake cewa bane, ba ana nufin an yabe shi bane.

 Wannan wani bahasi ne da zai zo nan gaba musamman da ruwayoyi insha Allah, ta yadda za mu fahimci karfi da yaji an yi kokarin kange matsayin Imam Ali (AS) ne na fansar rayuwar Manzon Allah (S) yana me neman yardar Allah da ya yi a daren hijira, a yayin da ya kwanta a shimfidar Annabin da Mushirikai sukai gangamin kashewa.

 Kun san jarumtar Ali (AS) irin na Annabi (S), irin kuma na ‘ya’yan Hashim ne. Kila bamu sani ba, ko mun manta cewa Allah (T) bai halicci wasu mutane da suka kai Banu Hashim jarumta ba. Ya zo a cikin littafin Al-Irshad cewa; A yakin Hunaini, bayan da Sahabbai suka gudu suka bar Annabi (S), sai ya kasance daga shi sai mutum goma. To, mutum tara daga cikin goman nan dukkansu Banu Hashim ne. mutum na goma shine Aiman (dan gidan Ummu Aiman (RA)). Da aka kashe Aiman sai ya kasance saura mutum tara dukkansu Hashimawa ne tare da Manzon Allah (S).

 Hashim shine kakan Manzon Allah (S) na biyu. Kamar yadda muka sani, mahaifin Annabinmu Tsarkakakke dan Tsarkaka shine Shugabanmu Abdullahi Dan Abdulmudallib dan Hashim (AS). Wadannan tsarkakan bayin da suka kasance masu sujuda a tsawon kasancewarsu. Allah (T) ya zabe su, ya fifita su a kan dukkan talikai, kuma ya sanya su masu Imani, masu sujuda, ya rika jujjuyawa da tsatson Annabinsa Muhammad (S) ta cikinsu tun daga Adamu (AS) har zuwa kan na karshensu Abdulmudallib (AS).

 A cikin Khisal, daga Manzon Allah (S) yake cewa: “Allah Mai girma da daukaka ya kasa mutanen kasa zuwa gida biyu; sai ya sanya ni a kashin da ya fi alkairi. Sannan sai ya kasa wannan rabin (mafi alkairin) gida uku, sai na kasance fiyayyen kaso ukun. Sai Allah (T) ya zabi Larabawa daga cikin dukkan mutane, ya kuma zabi Kuraishawa daga dukkan Larabawa, sannan ya zabi Banu Hashim daga dukkan Kuraishawa, sannan ya kuma zaban Banu Abdulmudallib daga cikin Banu Hashim, sai Allah (T) ya zabe ni daga cikin dukkan Banu Abdulmudallib.”

 A wajenmu, dangin Manzon Allah (S) sune mafiya kyawu da tsarkakan dangi. Mu mabiya Annabi Muhammad (S) mun yi Imani da cewa iyayensa tun daga kan Abdullahi har zuwa kan Annabi Isma’il zuwa Annabi Adam (AS) dukkansu Musulmai ne, masu Imani da Allah (T). Ba’a taba samun Mushiriki a tsatson Annabi (S). Wasu ruwayoyi da wasu suka kawo a cikin littafansu cewa wai wani ya tambayi Annabi cewa ina babansa yake? Sai Annabi wai yace wai da babanka da babana duk suna wuta (Wal iyazu billah) duk karyar banza da hofi ce. Kirkirarrun labarai ne don a kushe darajar Manzon Allah (S).

 Yaushe Allah zai shaida mana cewa ya jujjuya Annabi a tsatson masu sujjada kuma ya zama an samu Mushiriki a cikin iyayensa? Ballantana kuma babu wani da ya isa ya kawo maka cewa an taba samun wani daga iyayen Manzon Allah (S) da a tarihi aka ganshi ya ma gunki sujada. Larabawa suna bautar gumaka ne kafin Musulunci, amma ko a lokacin su gidan iyaye da kakannin Annabinmu (S) ba su taba bautawa gunkin ba. Don haka ne ma Annabi (S) ya iya tasowa a hannunsu tsawon shekaru 40 kafin ai masa wahayi bai taba bautar gunki ba.

 Abin da ya inganta shine iyayen Manzon Allah (S) sun kasance ne mabiya addinin Annabi Ibrahim (AS), wanda su ne suka kasance halifofi kuma wasiyan karshe na Annabi Ibraheem (AS) kafin bayyanar Annabi Muhammad (S).

 Malam, ka kaddara cewa dukkansu Mushirikai ne, saboda a lokacin da suka rasu ba a aiko musu da Manzo ba, ba su samu mai kira ba, balle ya kira su su bi Allah. Sai suka mutu a yadda suke, ashe Allah (T) bai cewa: “Bamu kasance masu azabtarwa ba har sai mun tada dan sakonmu (Manzo)”? Ta ya Allah zai saka wadanda bai ake musu da Manzo ba a wuta? Ai sai Allah (T) ya aiko da Manzo ne, sakonsa ya riske ka kaki ka bi shi hark a mutu, sai ya azabtaka akan cewa an yanke maka hujja ka ki karba.

 Ko da yake, mutanen nan ba su tsaya a kan cewa iyayen Annabi (S) ne kawai a wuta ba, sai dai suka rufe idonsu suka kirkiri karyar cewa wai wanda ya raini Annabi (S) ya bashi kulawa ma, wato Abudalib (AS) wai ya mutu yana Mushiriki ne. Wani da ya Musulunta ‘yan watanni kafin wafatin Annabi (S), bai ma san Abudalib ba, bai taba ganinsa ba, ya yi musu ruwaya cewa wai da Abudalib (AS) ya zo mutuwa, bayan ya shekara 13 yana taimakon Annabi (S) a wajen isar da sakon addinin nan, wai amma duk bai Musulunta ba, wai sai Annabi (S) yace masa; Ya baba, ka Musulunta, sai Abudalib (AS) wai ya ji nauyin hakan, ya duba yaga Mushirikai a gewaye da shi, sai yace ma Manzon Allah (S); Ya Dana. ‘Ni ina kan addinin iyayena.’

 Don haka wai sai ya mutu yana Mushiriki. Saboda su sun dauka cewa iyayen Annabi (S) din Mushirikai ne. In da gaske ne Abudalib (AS) yace yana kan addinin iyayensa ne, ai iyayensa, wato kakannin Manzon Allah (S) dukkansu Musulmi ne masu bin Musuluncin da Allah (T) ya aiko Annabi Ibrahim (AS) da shi. Idan za ka taimaki kanka, sai ka yarda da ruwayoyin da aka samu daga ‘ya’ya da jikokin Annabi (S), da ke tabbatar da cewa Abudalib (AS) Musulmi ne, na farko-farko ma, sai dai ya boye imaninsa ne saboda ya samu damar taimakon Annabi (S). Wannan kuma bai buya ma kowa ba cewa an samu Mumini a cikin fadan Fir’auna da yake bin Musa (AS) amma ya boye imaninsa saboda ta hakan ne kawai zai iya taimakon Annabi Musa (AS).

 Wato abin da ya faru shine, wasu tunda ya zama ba iyayensu kawai ba, har su kansu sun girma suna bautawa gumaka ne, iyayensu sun mutu suna Mushirikai, don haka suka gummace suce ai ba iyayensu ne kawai za su shiga wuta ba har da iyayen Manzon Allah (S) da iyayen Ali (AS) ma. Don haka kun ga sai ya zama in aka ce musu Allah (T) ya yi alkawarin wanzar da Shugabanci a tsatson Annabi Ibraheem (AS) wadanda ba su kasance azzalumai (kafirai ba), sai suce ai a tsatson Ibrahim din, da aka gangaro, su iyayen Annabi (S) sun kasance daga cikin azzalumai (Kafirai) ne. Don su kare maslahar sarautarsu suka dankara kafirci a kan iyayen Manzon Allah (S).

 Gaskiyar Magana shine, Allah ya sanya iyayen Manzon Allah (S) su kasance akan addinin Annabi Ibrahim (AS) ne. Kuma ba kawai addini ba, sai da Allah (T) ya gadar musu da ilimi da kyawun sura da haibar Annabi Ibrahim (AS). Har ma yazo cewa; a yayin da Sarki Abrahata ya ga Abdulmudallib (kakan Annabi (S), sai ya tsaya yana ta kallon fuskarsa, ya yaba da kyawunta da haibar da ke tattare da ita, bai taba ganin kyakkyawa kamarsa ba. Sai yace masa; Shin a cikin iyayenka akwai mai irin kyawun nan da hasken da na gani a cikin fuskarka? Sai Abdulmudalib (AS) yace masa; ‘Kwarai kuwa ya kai wannan sarki! Dukkan iyayena sun kasance kyawawa, ma’abota haske da haiba.’ Malam, wannan haibar da hasken da kyawun, ajiyar Allah ne na ManzonSa (S) a cikin wannan tsarkakakken tsatson.

 Yaushe zan aminta maka da wani tatsuniyar jingina kafirci ga mahaifan Fiyayyen halitta baki daya? A in azan yarda da kai a yayin da kake kokarin jefa Mahaifan Ma’abocin ceto a ranar Alkiyama a wuta? Iyayen Annabi na, Muminai ne, Fiyayyu akan dukkan al’ummar Annabi (S) ba kawai Sahabbansa ba. Ban gushe ba ina fatan Allah (T) ya yi mana makoma da makomar Abdullahi da Amina da Abudalib da Fatima bint Asad (AHS).


 Insha Allah a cigaba za mu ji labarin haihuwar wannan Annabi (S) da irin karairaki da aka lafta a ciki don a rage kima da darajarsa ga al’ummarsa (S). Allah ya kara mana soyayyar Manzon Allah (S).

No comments:

Post a Comment