Daga Saifullahi M Kabir
Cikin masu yin comment akan rubutun da nake yi, wani bawan Allah ya min nasiha, yana mai cewa: “Bawan Allah ka ji tsoron Allah. Dukkan Sahabban Annabi ‘yan Aljanna ne, ba wanda zai shiga wuta a cikinsu. Kuma mu muna tare da su, muna son su kome suka yi. Ka dena zagin Sahabbai. Annabi yace mu kame bakinmu daga abin da duk suka aikata, har ma yace musu ku aikata duk abin da kuka ga dama Allah ya ya gafarta muku.”
Da farko sai nace, na gode sosai, kuma na ji dadi da wannan nasiha, domin kamar yadda Manzon Allah (S) ya fada cewa: “Addini nasiha ne.” don haka ne ma na dage wajen yi ma mutane nasiha akan wajibcin nisantar wadanda suka bijirewa Manzon Allah (S), da kira zuwa ga bin wadanda aka ce mu bi su. Nagoda da nasiharka. Ko ba komai hakan ya nuna ana biye da abin da nake cewa. In da kuskure a ciki a sanar da ni kuskuren ne bisa hujja ba da kame-kame ba. Allah ya kara mana tsoronSa.
Mu fara da fadinka cewa: Dukkan Sahabban Annabi ‘yan Aljanna ne, ba wanda zai shiga wuta a cikinsu.” Sai nace maka, har da mutum 12 din nan da Manzon Allah (S) ya kira su da Sahabbansa! Kuma yace amma su Munafukai ne, kuma yace ba za su shiga Aljanna ba? Suma kana tare da su ko? Ka amince Allah ya maka makoma daya da su?
Hadisi na 7212 a cikin Sahihu Muslim, Huzaifa (Ma’abocin sirrin Manzon Allah) ya ba da labari cewa, Manzon Allah (S) yace: “A cikin SAHABBAINA akwai wasu munafukai guda goma sha biyu (12). Daga cikinsu akwai mutum takwas da ba zai yiwu su shiga Aljanna ba sai idan har rakumi zai iya wucewa ta hujin allura….”
A cikin ruwayar, Manzon Allah (S) cewa yayi fa; ‘Fi ashabiy….’ Wato, a cikin Sahabbaina. Kai kuma yanzu kace min duk Sahabban Annabi (S) ‘yan Aljanna ne. Manzon Allah (S) yace; Ba za su shiga Aljanna ba! Kai kace ba wanda zai shiga wuta a cikin Sahabban. Maganar wa za mu kama tsakanin taka da ta Annabinmu Muhammad (S)?
Ballantana ma, wannan kana iya kace, ai su Munafukai ne. Ah! To ka san adadin Munafukai a cikin Sahabban Manzon Allah (S) ne? Ka san suwaye Munafukai su waye ba su ba? Baka ji a cikin Alkur’ani Allah (T) yana fadawa Annabi (S) cewa daga cikin Sahabbansa akwai wadanda suka kware da Munafunci har ta kai ga cewa Annabin ma ba zai iya saninsu ba, Allah ne kawai ya san su?
Ba mamaki sune wadannan masu canza addinin Annabi (S) din a bayan wafatinsa. Wadanda Imamu Bukhari ya kawo mana hadisai a cikin Sahihinsa, Annabi (S) yana bada labarinsu cewa ranar Lahira za a kawo su wajensa ya gansu, sun san shi ya sansu, sai ya ga za a kada su, yace zuwa ina? Ace zuwa wuta! Yace Ya Rabbi Sahabbaina ne. Sai ace ma Annabi (S) baka san abin da suka aikata a bayan wafatinka ba. Sun canza addininka sun gayyara sunnarka!
Mu duba ruwayoyin mana kawai a yadda suke a cikin Sahihul Bukhari? Mu fara da Hadisi na 6576 da hadisi na 7049 a cikin Sahihul Bukhari, Mugira yace, ya ji Abu Wa’il daga Abdullahi yace: Manzon Allah (S) yace: “Ni ina tare da ku a bakin Tafki (a ranar Alkiyama), kuma na san wasu mutane daga cikinku, za a zo ana kore su, a raba su da ni. Zan ce; Ya Ubangijina, Sahabbaina ne. Sai ace min; ‘Hakika baka san abin da suka aikata a bayanka ba.”
A hadisi na 6583 a cikin Bukharin, Manzon Allah (S) yace ne, a yayin da yake shayar da mutane a tafki da ruwan da duk wanda ya sha ba zai kuma jin kishi ba har abada. Sai azo a kore wasu jama’a daga inda yake. Yace Jama’an ya sansu sun san shi (wato sun yi rayuwa ne tare da shi), amma sai a raba tsakaninsa da su.
A hadisin dake gaban wannan, na 6583 kenan, Abu Sa’idul Kudri yace; Manzon Allah (S) yace, a yayin da aka kore sahabban nashi daga gare ni, zan ce; “Ya Ubangijina su fa daga gareni suke. Sai ace min; Kai baka san abin da suka yi a bayanka ba.” A nan Manzon Allah (S) zai yi musu bara’a. Yace a nisanta shi da duk wanda ya haddasa wani abu a bayana daga gareni. Wato ai wuta da su.
Eh mana. Idan mutum na tare da Manzon Allah (S) a Lahira sai aka zo aka raba shi da Annabi wane makoma za a kais hi? Wuta! Kamar yadda idan muka koma Hadisi na 6587 a cikin Bukhari din, za mu ga ruwayar Abu Huraira daga Annabi (S) yana cewa: A yayin da yake tsaye a cikin mutanen, wadanda ya san su sun kuma san shi (Sahabbai kenan), sai WANI MUTUM ya fito ya shiga tsakanina da su. Sai yace musu; “Muje!!!” Manzon Allah (S) yace, sai nace, “Ina za su je?” Sai wannan Mutumin da yake kada su, yacewa Annabi (S), “Wuta za su je wallahi.” Sai Annabi (S) yace, “Me ya faru da su?” Sai mutumin yace ma Annabi (S): “Sun juya baya ma addini, sun yi ridda ne a bayan baka” (wato, sun canza addininka, sun komo da jahiliyyar da suka baro). Manzon Allah (s) yace; “Wadanda za su yi saura a cikinsu ba za su wuce misalin ‘hamalin ni’am’ ba.”
Ance; ‘hakan na nufin’, misali, idan makiyaya na tafe da garken shanu masu yawa, akan samu ‘yan kwarori da sukan mutu a hanya ko a yanka su sakamakon wahala ko ciwo ko su bace. To misalin wadanda za a bari tare da Manzon Allah (S) a wannan wajen a cikin sahabbansa basu wuce irin ‘yan kwarorin nan da kan salwanta a cikin garke ba. Sauran duk wuta za a tura su.
Wa zai tura su watan to? Ai kun ji a hadisi na 6587, Manzon Allah (S) yace mana, wani mutum ne zai zo ya shiga tsakaninsa da Sahabban nasa, ya kada su zuwa Jahannama. Yace masa baka san abin da suka aikata bayan wafatinka ba. Sun canza addininka sun bar koyarwarka, sun shimfida sarautansu, sun mai da addinin kamar tafiyar jahiliyyar da suka baro. Me yasa Mutum ne zai yi ba Mala’iki ba? Kun san mutumin? Shine wannan da Manzon Allah (S) yace mana shi zai raba wuta da Aljanna a ranar Alkiyama. Amirulmuminin Ali Dan Abudalib (AS), kamar yadda nan gaba za mu zo da ruwayoyi a kan hakan.
To, kai mai cewa dukkan Sahabban Annabi ‘yan Aljanna ne bad an wuta a cikinsu kuma kana tare da su ko me suka aikata. Har yanzu kana nan a bakanka? In ka kafe akan hakan, kana karyata Manzon Allah (S) ne? Ko masu ruwayar wadanda su Sahabban ne da kansu? Ko Imamu Bukhari din duk da amincin da ka bashi? Malam! Ka amince Allah ya maka makoma daya da wadannan mutanen da Imam Ali (AS) zai kora su wuta da umurnin Allah (T) da amincewar Manzon Allah (S)?
Kaga dai a nan Manzon Allah (S) bai ce munafukai bane. A’a, Sahabbansa ne, kila sun boye munafuncin ne, sai bayan da suka shayar da shi guba da sunan magani kamar yadda Mukai bayai a baya, Wafatinsa ke da wuya suka canza duk koyarwarsa. Suka bi ta kan iyalan gidansa. Suka canza duk wata sunnarsa, kamar yadda a baya muka kawo cewa hatta Sallah sai da suka canza. Bayan sun kwace hakkin shugabancin al’ummar Musulmi daga hannun masu hakkin. Sun kuma kwace dukiya da gadon masu gadon Annabi sun shirga masa karya cewa wai yace ba a gadonsa.
Malam, ba muna cewa a Sahabbai babu mutanen kirki da suka tsayu a kan addinin Annabi bane. A’a muna cewa ne akwai na kirki da suka wanzu a kan Addinin, akwai kuma masu juya baya, masu butulci, masu kangarewa koyarwar Annabi yana raye da bayan ransa. Don haka mu ba mu yi Imani da cewa wai dukkan Sahabban Annabi ababen riko bane. Face ma an ce ne su Sahabban da mu masu zuwa a bayansu mu yi riko da Ahlulbait (AS), wanda Imam Ali (AS) ne samansu.
Ba wanda muke zagi a cikinsu. Muna fadan gaskiya ne. Kuma ba Shi’a suka ruwaito ba, Sunnah ne. Amma gaskiyar magana ba wani waje da Annabi (S) yace mu kame baki daga abin da Sahabbai suka aikata. In kuma ka san wajen ka kawo min. Abin da na sani kawai shine tunda ya zama kun dauke su a matsayin masu koya muku Musulunci, to wajibi a sanar da ku cewa akwai abin da suka kirkira a bayan Annabi (S) wanda ba shine Musuluncin da Annabi ya koyar ba. Kuma mu da muka san hakan, hakki ne a kanmu mu sanar da ku gaskiya. Iyalan Manzon Allah (S) da Alkur’ani, su ne ababen riko ba waninsu ba ko waye!
Shin zai yiwu Manzon Allah (S) yace wa wani ya aikata duk abin da yaso, tun kafin ya aikata ma an yafe masa. Wannan a hankalce ma ya saba ga duk wanda kwakwalwarsa ba irin na dabba bane! Duk wanda ya aikata mummuna misalign kwayar zarra zai gani a ranar Alkiyama, haka ma duk wanda ya aikata mai kyau komai kankantarsa zai gani a ma’auninsa ranar Alkiyama. Koda wannan mutumin Annabi ne, ba sahabi kawai ba. In har Annabi zai ce su aikata abin da suka so an yafe musu, me zai sa kuma a kada su wuta ace sun canza a bayansa?
Za mu cigaba insha Allah.
No comments:
Post a Comment