February 11, 2018

Tsage Gaskiya (9)

Daga Saifullahi M Kabir 

Manzon Allah (S) wata rana ya kira Sayyida Zahara (S), sai yake ce mata: “Ya ke ‘ya ta, hakika za a zalunce ki a bayana. Kuma za a raunata ki a bayana. Duk wanda ya cutar da key a cutar da ni, wanda duk ya miki hujumi ya min hujumi ne, wanda kuwa ya sadar gareki, to ya sadar gareni ne, kuma wanda ya yanke miki ya yanke mini ne. Domin ke daga gareni kike, kuma ni ma daga ke nake, ku ma ke tsoka ce daga jikina, kuma kece ruhina.” Sannan Manzon Allah (S) yace mata: “Ga Allah kadai nake gama duk wanda ya zalunceki daga cikin al’ummata.”

Wata rana Manzon Allah (S) ya kira Imam Ali, Hasan, Husain da Sayyida Fatima (SA), sannan sai yace ma duk wadanda suke dakin su fita masa. Sanna yace ma Ummu Salma, ke ki tsaya a kofar dakin kar ki bar kowa ya shigo. Sannan sai yace ma Imam Ali (AS): “Ka matso kusa da ni.” Sai Imam ya matsa. Sannan sai ya kama hannun Sayyida Fatima ya daura shi akan kirjinsa na lokaci mai tsawo. Ya kuma rike hannun Imam Ali da dayan hannunsa. Yayin da Manzon Allah ya so ya musu Magana, sai ya kasa, sai kawai ya kama hawaye kawai. Ya yi kuka mai tsanani, sannan suma duka suka fashe da kuka tare da shi.

Sai Sayyida tace masa: “Ya Ma’aikin Allah zuciyata ta raunana saboda kukanka. Ya kai shugaban Manzonni daga farko har karshe, Ya kai amintaccen Ubangijinsa kuma ManzonSa, Ya Masoyinsa kuma Annabinsa. Wane ne zai kasance ga ‘Yayan nan (Hasan da Husaini) bayanka? Kuma musiba za ta sauka min a bayanka? Wane ne ga Ali dan’uwanka kuma mai taimakon addininka? Wane ne da Wahayin Allah da al’amarinsa? ”

Sai Manzon Allah (S) ya cigaba da hawaye har ya rufe fuskarsa saboda wannan kukan. Sannan Ali, Hasan da Husain (AS) suma duk kuka suke yi. Har zuwa lokacin da ya daga kansa, yana kallonsu. Hannun Fatima (SA) yana rike a hannunsa. Sai ya hada hannun da na Imam Ali (AS) sannan yace masa: “Ya kai Baban Hasan. Amanar Allah da na Annabinsa yana hannunka, Ka kiyaye ma Allah da ni a cikinsu, na san za ka aikata hakan.”

Manzon Allah (S) ya cigaba da cewa: “Ya Aliy. Ka kiyaye abin da duk Fatima ta umurceka da su, hakika na umurceta da abubuwan da Jabara’ilu ya mata umurni da su. Ka sani ya kai Ali, cewa ni mai yarda ne ga duk wanda Fatima ta yarda da shi, haka ma Ubangijina da Mala’ikunsa. Ya Ali, azaba ta tabbata ga duk wanda ya zalunceta, azaba ta tabbata ga duk wanda ya kwace mata hakkinta.  Azaba ta tabbata ga duk wanda ya ya keta alfarmarta.” Aka ce a sanna sai Sayyida ta mika kanta ga Annabi (S), sai ya shafa kanta, yace mata: “Babanki fansarki ya ke Fatima.”

To, wannan kamar na kawo muku karishen wasu ruwayoyi ne kamar yadda na faro a darasin da ya gabata. Don ya zama bai buya mana ba cewa dama tun farko Manzon Allah (S) ya sanar da Sayyida Zahra (S) da iyalanta cewa za a zalunce su, za a kwace hakkinta da na mijinta kuma ma za a doke ta har a yi mata barin cikinta. Amma Manzon Allah ya musu wasiyya da su yi hakuri.

Allah mai cika alkawari kuwa, sai ya zama ba wani abu da basu gani ba a bayan Manzon Allah (S) cikin abubuwan da ya fada musu za su riske su.

Manzon Allah (s) yana komawa ga Allah (T), a yayin da Amirulmuminin (AS) yake ta sabgogin kokarin ganin ya yi masa sutura ya bizne shi, sai ya zamana su kuma Muhajirun da Ansar daga Sahabbai sun watsar da wannan sha’anin na jana’izar Annabi, suka dankara ma kansu hada-hadar kokarin sun fitar ma da kansu Khalifan da ya dace da son ransu. Nan suka nufi wani zuren taro da ake cema ‘Sakifar Banu Sa’ida, inda kowace Kabila daga Kabilun Madina kowannensu yake raya cewa lazim su ne za su samu matsayi na su halifci Annabi (S).

Abin mamaki sosai, ta yadda za mu ga cewa kwata-kwata, bai wuce watanni biyu ba Manzon Allah (S) ya tara su a Ghadeer Khum ya halifantar da Imam Ali (AS) a matsayin halifansa a cikinsu a bayansa. Labarin Ghadeer abu ne da yake kamar hasken rana, sam bai buya ma mutanen wannan lokacin ba bare na wancan zamanin. Amma kuma yau ga Manzon nan ya koma ga Allah (T), ko bizne shi ba a yi ba, amma har sun juya ma umurninsa baya.

Dama a cikin Alkur’ani, Allah (T) yace: “Muhammadu ba kowa bane face Manzo, kuma Manzonni sun gabace shi. Shin idan ya mutu, ko kuma aka kashe shi, za ku (yi ridda) ne ku koma ga abin da diga-diginku ke kai (Jahiliyya)?” Sai kuwa mutanen nan suka ba Allah amsa a aikace da cewa Eh! Mun zabi mu watsar da abin da ya zo da shi, mu yi son ranmu. Wanda hakan shine Jahiliyya din.

Ba za ku yi mamakin juya bayansu da kin karban wasiccin Manzon Allah (S) ba a yayin da ya yi wafati, tunda a halin da yake da ransa ma, ya musu umurni da abubuwa da dama sun ki yi. Ai bai buya ma mai bibiyan nazarin nan ba inda ya zama ya inganta cewa Manzon Allah (S) ya nemi su bashi abin rubutu sun hana, har ma Umar ya fadawa Annabi bakar magana ko? Da kuma inda yace kar su bashi abu suka dura masa, har ma wata tace sai suka dura masa alhali yana hana su, suka ki.


To, wani abu da ba mu yi magana a kansa da zurfi ba a baya shine batun tura su yaki da Annabi (S) ya yi a karkashin Usamatu Dan Zaidu, da suka ki su je, suka dawo suka tsaya a kansa, ya daga kai ya gansu yace Allah ya la’anci duk wanda bai kama hanya ya tafi ba. Kuma basu je din ba.

Yana raye kenan. Ina kuma ga ace ga shi sun ga baya numfashi? Bai da halin yi musu magana? Sai su bi umurninsa a wannan lokacin? Eh haka ya kamata. Amma ba su yi hakan ba.


Insha Allah, mu tsaya a nan sai mu cigaba da labarin Saqifa kamar yadda Imam Abu Muhammad, Ibn Qutaiba al-Dinawari, wannan malamin Ahlussunah da ya rasu a shekara ta 276 bayan hijira (yau kimanin shekara 1193 da rasuwarsa) ya kawo a littafinsa Al’imama was-Siyasa.

No comments:

Post a Comment