Daga Saifullahi M Kabir
A rubutun da ya gabata, idan mutum yana biye, zai ga cewa mun kawo sabani mai ban takaici da Umar dan Khaddabi ya haifar ga Sahabbai a gaban Manzon Allah (S) a ranar Alhamis din 24 ga Safar, shekara ta 11bh. Wanda wannan sabanin, wanda ya biyo bayan hana Manzon Allah (S), abin rubutu, shi ya jefa al’ummar nan cikin rudu da bin bata, da kauracewa hakikar shiriya. Domin Manzon Allah (S) yace ne; “Zan rubuta muku abin da in kuka yi riko da shi ba za ku taba bata ba har abada.” Kenan idan ba a yi riko da shi ba za a bace. To ina kuma ga ma ba a bari an rubuta din ba? To kun ga sai Umar yace ba za a bayar ba. A kyale Annabi zafin ciwo ke cinsa, ko ma kamar yadda ya zo a wata ruwayar, yace ne Annabi ya fita daga hayyacinsa, littafin Allah ya wadatar da su
Don haka nake cewa, wannan hana Annabi (S) ya rubuta Hadisi mai muhimmanci wanda yake dauke da wasiyar shiriya ta dindindin, ta tabbatar maka da cewa wanda ya hana din da wanda ya goyi bayan hanawan, dukkansu wasu mutane ne masu boyayyun al’amari a zukatansu. Wato ina cewa ne, ya kamata ka yi tunani, me yasa Umar zai tsaya tsayin-daka yace ba a isa a ba Annabi abin rubutu a wanan lokacin da ya nema ba? Anya zai zama haka kawai ne ba wani abin shi da wadanda suka goyi bayansa a wajen suke gudu ba? Mene ne wannan abin? Muna da bukatar mu ji shi ko?
Kar a manta, hadisan da muka kawo a rubutun da ya gabata dangane da jayayyar Umar ga Annabi (S) gaba daya daga littafin Sahihin Bukhari ne, mun kawo Hadisi na 114 da na 3053 da 4431 da 4432 da 5669 da na 7366. Allah ya so ya zama wannan batun bai buya ga al’ummar Muhammad (S) ba, cewa Umar dan Khaddabi ne ya shiga tsakanin shiriyarsu da Mai shiryarwa. Kamar yadda Ibn Abbas (RA) ke cewa: “Mafi munin abin bakin ciki shine abin da ya shiga tsakanin Manzon Allah (S) da rubutunsa na shiriya.” Kuma ba komai bane wannan abin da ya shiga tsakanin face Umar din da ya hana Annabi (S) da wadanda suka goyi bayansa.
Kar kace ina ta cewa Umar, Umar, Umar bance Sayyadina ko abin da ya kamaci haka ba. Ina magana ne akan shi a gaban Manzon da babu wani Sayyid a gabansa a duk talikai. Ina magana ne akan Umar a yayin da ya sabawa Shugaba (S) da gangan, saboda abin da suka boye a zukatansu na cewa ba su so ya zama shiriya ta tabbata a cikin wannan al’ummar ba, sun ma kansu alkawarin ba makawa sai sun canza duk wani abu da yake daidai da yadda Annabi (S) ya zo da shi. Kamar yadda kuma sun yi iyakar kokarinsu wajen ganin sun canza addinin nan a bayan Manzon Allah (S).
Inda za ka san cewa hana Annabi yin rubutun nan ya jawo halakar da yawa daga ‘yan wannan al’ummar, ka shiga cikin Sahihul Bukhari ka binciko hadisi mai lamba ta 530, daga Abu Rawwada, dan uwan Abdul’azeez, yace; Na ji Zuhri yana cewa: Wata rana na shiga wajen Anas Dan Malik (hadimin Manzon Allah (S) a garin Dimashk, sai na tarar da shi yana kuka. Sai nace da shi me yasa kake kuka? Sai yace min; ‘Ban san wani abu daga abubuwan da na riska a lokacin Manzon Allah (S) da yanzu yake nan (a yadda yake) ba in banda wannan Sallar, kuma ita ma sallar an canza ta!’
Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Ku duba ku gani, Sahabi ke kuka, shekara kasa da 30 daga wafatin Manzon Allah (S), amma yana ba da tabbacin cewa duk wani abu da Manzon Allah (S) ya koyar na ibada, hatta sallah da ake yinta kullum sai da aka canza ta daga irin wacce Manzon Allah (S) yake yi kuma ya koyar. Malam, ina kuma ga kai yanzu da kake cikin shekara ta kusan 1330 bayan wafatin Manzon Allah (S)?
Hadisi na 529 a cikin Buharin dai, daga Anas din, yace; “Ban san wani abu da yake a zamanin Manzon Allah (S) wanda yake a yanzu (a yadda yake a da din) ba.” Sai aka ce da shi, ga Sallah. Sai yace; “Ashe ba ku canza abin da kuka canza a cikinta ba!?”
Masu tambayar nashi fa Sahabbai ne suma, sun ga Annabi (S), sun yi Sallah tare da Annabi (S), amma an wayi gari a kasa da shekaru 30 da wafatin Annabi (S) halifofin da suka mulki al’ummar Annabi sun tilasta canza wasu abubuwa daga yadda suke a hakika. Muna iya cewa sun canza koyarwar Manzon Allah (S) zuwa abin da suka ga dama. Sai aka wayi gari Sahabbai ma sun dena yin irin ibadar Manzon Allah (S). Ina kuma ga tabi’ai da mabiyansu har zuwa yau da muke?
Kun ga shiriyar da Annabi ya so ya rubuta din nan wacce da Umar da wasu daga Sahabbai sun bari ya rubuta mana, kuma suka bar al’umma suka bi, da ba a kai ga wannan baganniyar ba. Amma da suka hana, sai ya zama Manzon Allah (S) ya fadi wasiyyar da baki, nan ma kamar yadda suka kawo a cikin Hadisi na 4431 a cikin Bukhari, sai aka ce wai Annabi (S) ya yi wasiyya da abubuwa guda uku ne, aka fadi guda biyu aka ce wai an mance wasiyya ta uku da ya yi.
Har mukan ce, don Allah kar a mai da mu wawaye mana. Ace Manzon Allah (S) da kansa ya yi wasiyya da abubuwa kwara uku kacal, amma duk wadanda suke wajen ace guda biyu suka iya tunawa sun mance na karshen? Ashe da ace Annabi (S) ya yi wasiyya da abubuwa 313 ne bai zama wajibi a kiyaye su ba? Ballantana guda uku kacal!? Da sannu za mu zo da bayanin wasiyyar da Annabi (S) ya yi ta ukun da aka ce an mance ta. Wacce ita ce ya so ya rubuta ta ma don tabbatarwa. Wannan wasiyyar kuwa itace riko da Imam Ali (AS) a bayansa, domin shi ba zai taba canza addininsa ba har abada! Don haka riko da shi da koyi da shi a bayan Manzon Allah (S) ne kawai shiriyar da za ta wanzar ma da mutum imaninsa har abada.
Ba ku ji ba? Har a lokacin da aka canza komai din, Sahabban Annabi (S) suka koma yin ibada irin wanda sarakuna suka amince da su yi. Imam Ali (AS) ne da kadan din da suke bi shi suka cigaba da yin duk wata ibada irin yadda Annabi (S) ya yi.
Hadisi na 784 a cikin Bukhari, daga Imrana bin Husyn, yace: Mun yi salla tare da Aliyu dan Abudalib (RA) a garin Basra. Sai muka ce: Wannan mutumin (wato Imam Ali) ya tuna mana da irin sallar da muke yi tare da Manzon Allah (S). A nan muka tuna cewa Manzon Allah (S) fa idan yana sallah, yana yin kabbara a duk lokacin da ya dago ko ya duka.”
Hadisi na 786 da na 826 duk a Sahihul Bukhari din, daga Mudarrif dan Abdullahi, yace; Mun yi salla a bayan Aliyu Dan Abudalib (RA) ni da Imrana Dan Husyn. (Ali) ya kasance idan zai yi sujada yana yin kabbara, idan ya dago daga sujada yana yin kabbara, idan zai tashi daga raka’a ta biyu yana kabbara. A yayin da muka idar da sallar. Sai Imran Dan Husyn ya kama hannuna yace; Hakika wannan (suna nufin Imam Ali) ya tuna min da sallar Manzon Allah (S). Ko kuma yace ne; “Hakika ya yi mana irin sallar Manzon Allah (S).”
Ya kai ma’abocin neman shiriya, don Allah ka yi nazari a karan kanka akan wannan al’amarin. Nan fa dukkansu da mai sallar da masu bin sallar Sahabban Manzon Allah (S) ne, sun yi sallah a bayansa, amma kalli yadda mafiya yawansu suka mance ma da yadda Annabi (S) yake Sallah sai da suka gani Imam Ali (AS) yana yi, sannan suka tuna cewa ashe fa ga yadda Annabi (S) yake yin Sallarsa. To, don Allah, da sallar wa suke yi kenan?
Malam, wadannan sune fa wadanda suka ruwaitowa al’ummar Annabi addinin Annabi. Dubi yadda har sallah ma su kansu ba suna yin irin na Annabin (S) bane, ina kuma ga kai yanzu? Amma kun ga sun ba da shaidar Imam Ali (AS) na yin salla ne irin yadda Annabi (S) ke yi ko? To kuma don me za ka bi wadanda suka dena yin irin ibadar Manzon Allah (S) ka bar wanda yake yin irin na Annabi (S)?
Ashe za mu zama ababen zargi a wajen mai hankali, idan muka ce ba za mu bi wadanda suka hana Annabi ya rubuta mana tabbatacciyar shiriya ba? Idan muka ce mun ki mu koyi addini daga wadanda suka dena yin irin ibadar Manzon Allah (S)? Abin mamaki yanzu idan wanda ake kira Shi’a, mabiyin Imam Ali (AS) ya zo yana Sallah, tun daga alwala za ka ga mutane suna nuna shi, suna cewa dubi yadda yake alwala. Malam! An canza addininka ne daga koyarwar Annabi (S), mu kuma muna yin addini da ibada ne irin wanda kofar ilimin Manzon Allah (S) ya ruwaito mana, ‘ya’yansa suka koyar da mu.
Na tsaya wani misali har rubutun nawa ya yi tsawo yau ma. Sai nace gaskiyar magana ni dai bani ba wanda ya yi jayayya da Manzon Allah (S) akan rubuta mana shiriya, wallahi ina fada maka GASKIYA ne cewa ban sonsa, ban kuma goyon bayansa, ina son Annabi (S) ne, kuma ina goyon bayan Annabi (S) ne! Allah ya riga ya tsare; amma wallahi idan da Annabi Adamu, ko Ibraheem ko Isa (AS) waninsu zai sabawa Annabi Muhammad (S) akan wata magana bare umurni, da ba zan bi su ba, b azan so su ba, kuma b azan musu uzuri ba. (Sun kubuta daga aikata hakan), to, ballantana wani da ba ma waliyi bane, bisa shaidar ruwayoyi ma yana cikin Jahilan cikin sahabban Mazon Allah (S) kamar yadda za mu ji a can gaba.
Kuma da sannu za mu ji cewa ba a ranar Alhamis din nan ne kawai ya fara jayayya da Annabi (S) ba, ingantattun ruwayoyi a cikin Sahihul Bukhari sun tabbatar da cewa har cin-kwala (shake) Manzon Allah (S) ya taba yi. Muhammad (S) ne Annabina kuma shine abin riko na.
Za mu cigaba insha Allah.
No comments:
Post a Comment