Daga Saifullahi M Kabir
A rubutun da ya gabata na yi kokarin tunatar da mu yadda suka canza koyarwar Manzon Allah (S) da gangan, sakamakon kin bari ya rubuta mana wannan shiriyar. Ko da yake duk da sun hana rubutun, Manzon Allah (S) ya fada mana abin da zai rubuta, cewa: Bayansa mu yi riko da Iyalan gidansa tsarkaka ne.
Wani abu da ya kamata mu waiwaya a nan shine, shin sun bi iyalan gidan nasa a bayansa? Shin sun yi riko da iyalan gidan nashi a bayan wafatinsa ne?
Babba a cikin iyalan gidan Manzon Allah (S) it ace Maulatana Sayyida Zahra (SA). Wannan da a hadisi na 3714 a cikin Sahihul Bukhari, aka ruwaito daga Abu Walid, da isnadinsa zuwa ga Miswari Dan Makhrama yace: Manzon Allah (S) yace: “Fatima tsokar jikina ce, duk wanda ya fusata ta, ni ya fusata.” To, sun fusata Fatima (S) din ne, tare da cewa sun san cewa fusata ta fusata Annabi (S) ne. Suna sane da cewa kuma duk wanda Fatima (S) ta yi fushi da shi Manzon Allah (S) na fushi da shi. Kuma fushin Manzon Allah (S) fushin Allah (T) ne.
Malam, bance ka dauko littafin Alkafiy ba, ballantana k ace ai Shi’a ne. Ban kuma ce ka dauko Imama Was- Siyasa ba, bare kace ai bai ingata ba. Wannan Sahihul Bukhari din da ke hannunka nake so ka sake budewa ka je kan Hadisi na 4240 da na 4241, za ka ga ruwaya daga A’isha matar Annabi (S), tace: Fatima ‘yar Annabi (SA) ta aikawa Abubakar da sako tana mai tambayarsa a kan abin da ta gada daga Manzon Allah (S) na daga abin da Allah ya bashi a Madina da Fadak, da kuma abin da ya yi saura daga Kumusin Khaibar. Sai Abubakar yace mata; Ai Manzon Allah (S) yace: ‘Ba a gadonmu! Abin da muka bari sadaka ne…’
Ta cigaba da cewa: Sai Abubakar yaki yaba Fatima komai. Sai Fatima ta yi sabani da Abubakar a kan wannan, (cewa babanta yace ba a gadonsu), sai ta kaurace masa, har ta yi wafati bata sake masa magana ba. Kuma ta rayu ne bayan wafatin babanta da watanni shida. A yayin da ta yi wafati, mijinta Ali ne ya birne ta a cikin dare. Ba a gabatar da Abubakar gareta ba kuma bai sallaci gawarta ba.”
Wannan kunga Nana A’isha ke tabbatar da cewa Fatima ‘yar Annabi (S), wacce Allah ke fushi da fushinta, yake yarda da yardarta ta yi kauracewa Abubakar har ta koma ga Allah bata masa magana. Wato tsawon rabin shekara tana mai kaurace masa. Ba ma kawai hakan ba, har ta yi wafati ta bar wasicci ga mijinta akan ya bizne ta ne da daddare kar ya bari Abubakar ko Umar su sallaci gawarta. Don haka Imam Ali (AS) ya ma tsokar Annabi (S) janaza ya bizne ta a cikin duhun dare ba tare da sun sani din ba.
Wannan ke tabbatar maka da cewa, Sayyida Zahra (S) har ta koma ga Allah tana mai fushi da Abubakar ne, ba kawai da ta yi wafati shikenan ba. A’a, har yau din nan da muke ciki bata bar fushi da shi ba. Kuma kamar yadda aka ruwaito ta fada a wani waje, cewa sai ta kai karansa gaban Manzon Allah (S) a gaban zatin Allah (T) akan cewa sun fusata ta, kuma sun danne hakkinta.
Haka ma a Hadisi na 6726 a Bukharin, aka ce bayan da ta nema yace mata Manzon Allah (S) yace ba a gadonsu… Sai Sayyida Fatima (S) ta kauracewa Abubakar, ba ta sake masa magana ba har ta koma ga Allah (T).
Duk wadannan kila kace gaba daya hadisan guda uku da na kawo ba a ce ta yi fushi da shi ba, an ce ta kaurace masa ne. Sai nace idan ka kasa bambance ma’anar kauracewa mutum da kuma yin fushi da mutum, ka koma baya zuwa ga Hadisi na 3093, an kawo cewa, da Abubakar yace wa Fatima (SA), ai Manzon Allah (S) yace; “Ba a gadonmu, duk abin da muka bari sadaka ne.” Sai Fatima ‘yar Manzon Allah (S) ta yi fushi, ta kaurace ma Abubakar. Bata gushe ba tana mai kaurace masa har ta yi wafati. Kuma ta rayu ne bayan wafatin mahaifinta da watanni shida.
Wasu sukan ce to ai Abubakar ya ba Sayyida Zahra (SA) uzurinsa na hana ta gonarta ta Fadak da gadonta na Mahaifinta, da cewa wai Annabi (S) yace ba a gadon Annabawa. Sai nace maka ka tausawa zuciyarka mana, ka zamar da ita mai ‘yantacciyar tunani da nazari. Amfanin hankalin da Allah yam aka ya bambanta ka da dabba shine ka iya gane hankali da rashin hankali ko da rainin hankali.
Manzon Allah (S) da ya san cewa zai koma ga Allah, kuma ‘yarsa kwara daya da zai bari a Duniya ita ce Fatima (SA), kuma tana da hakkin ya sanar da ita duk wani abu da ya shafeta daga gare shi, don Allah zai yiwu Manzon nan ya tafi ya san ba za a gaje shi ba amma ba zai fadawa wannan ‘yar tasa kwara daya ba? Zai yiwu ya zama ya san cewa ba makawa za ta nemi ta gaje shi, amma sai ya kasa sanar da ita cewa kar ta nemi gadonsa abin da ya bari sadaka ne?
Ka budo Hadisi na 3715 da na 3716 a cikin Sahihin Bukharin da ke hannunka; A’isha matar Manzon Allah (S) tace, Annabi (S) ya kira ‘yarsa Fatima (SA) a lokacin rashin lafiyar da ya yi wafati a cikinta. Sai ya yi magana (cikin sirri) da ita, sai ta yi kuka. Sai ya kuma kiranta ya yi sirri da ita, sai ta yi dariya.’
A’isha ta cigaba da cewa: Sai na tambaye ta akan wannan sirrikan da ya mata (Bayan wafatin Annabi (S). Sai tace min, “Annabi (S) ya sirranta min cewa zai yi wafati a cikin wannan rashin lafiyar da ya yi wafati a cikinsa. Sai na yi kuka. Sai ya kara sirranta min cewa ni ce farkon wacce zan bi shi a cikin iyalan gidansa. Sai na yi dariya.”
Ashe in har Manzon Allah (S) zai yi wannan sirrin da ‘yarsa, zai mance ya fada mata cewa kuma ba za ki gajeni ba, har sai ta ji a wajen Abubakar, wanda dama kuma kaf cikin sahabbai shi kadai ne kawai ya san da wannan maganar cewa ba a gadon? Ko kana so kace min wannan da Allah (T) ya sanya yardarta da fushinta su zama nashi za ta nemi hakkinta ne bisa karya da zalunci? Kana so kace Sayyida Zahra ta san bata da gadon Manzon Allah (S) amma ta nema a bata? Har ta yi fushi akan hanata da aka yi?
Na sani, nan wajen ma muhalli ne na rabuwar ra’ayi tsakanin Musulmi, akwai masu ra’ayin cewa Abubakar ke da gaskiya kila kai kana cikinsu, amma ni da masu irin ra’ayina shine tsokar jikin Manzon Allah (S) ce mai gaskiya, kuma ita ke kan daidai, kuma fushin da ta yi da Abubakar ya tabbata a gare shi har abada. Domin da shaidar ‘yarsa A’isha ta ce har Sayyida Zahra (SA) ta koma ga Allah bata dena fushi da shi ba. Kuma fushinta fushin babanta ne, fushin babanta fushin Allah (T) ne. Don haka duk mumini wajibinsa ne ya yi fushi da wanda Allah ke fushi da shi!
Da sannu za mu zo da bayani a kan yadda kiri da muzu suka shure Imam Ali (AS) daga Khalifancin Manzon Allah (S), suka dauki sarauta, alhali Manzon Allah da kansa a bisa ingantattun ruwayoyi ya tabbatar musu da cewa Imam Ali (AS) ne halifansa a bayansa. Har ma nake cewa, wai ko son zama shugabanni da kuma bukatuwarsu ga cinye dukiyar Annabi (S) da sunan sadaka ne yasa aka kosa Manzon Allah (S) ya bar duniya, har ma aka ruwaito a cikin Sahihin Bukhari wasu na bada labarin cewa sun durawa Annabi magani alhali yana hana su? Suka ki hanuwa, suka dura masa, har ya suma, yayin da ya farka yace ashe ban hana ku akan kar ku dura min ba? Kar dayarku ta bar wajen nan face ta durawa kanta, in banda Abbas, domin shi bai san abin da kuka kulla ba!
Hadisai ne a cikin Sahihul Bukhari, insha Allah za mu biyo ta wajen a cigaban nasarinmu. Amma ina cewa ne, mutum ya sani, idan zai ma Manzon Allah (S) tawaye da gangan, to ya bi wadanda suka yi hannun riga da koyarwar Manzon Allah (S). Kuma abin da nake fada bai taba zama zagi ba, ina fadan zahiri ne, kuma gaskiya. Kuma dai Allah ya nufa ya zama yanzu mutane sun san gaskiya din ne, in suka ga dama su bi, in suka ga hagu kuma su cigaba da bin son zukatansu.
A wannan ‘issue’ din, muna bayan Sayyida Fatima (S) ‘Yar Annabi (S), kamar yadda a ‘issue’ din hana abin rubutu muke bayan Manzon Allah (S). Kai a ‘yar wanne kake?
Zan cigaba insha Allah.
No comments:
Post a Comment