Daga Saifullahi M Kabir
Kun karanta a baya cewa akwai hadisi na 3714 a cikin Sahihul Bukhari, daga Abu Walid, da sanadinsa zuwa ga Miswari Dan Makhrama yace: Manzon Allah (S) yace: “Fatima tsokar jikina ce, duk wanda ya fusata ta, ni ya fusata.” Haka ne ko? Shi fusata mutum na daga nau’in cutar da mutum din ne. To, mun ji cewa fusatawa ko cutar da Sayyida Zahra (S) cutar da Manzon Allah (S) ne. To, mene ne sakamakon masu cutar da Manzon Allah (S)?
A aya ta 56 na Suratul Ahzab, Allah (T) yana cewa: “Wadannan wadanda suke cutar da Allah da ManzonSa Allah (T) ya la’ance su a duniya da Lahira, kuma ya tanada musu azaba mai kunyatarwa.” A aya ta 61 na cikin suratul Tauba, Allah (T) yace mana: “Kuma wadanda suke cutar da Manzon Allah suna da azaba mai radadi.”
Idan haka ne, to mene ne matsayin wadannan da suka cutar da Sayyida Zahra (S) kamar yadda aka ruwaito a cikin Sahihul Bukhari hadisi na 4240 da na 4241 da na 6726, cewa har ta yi fushi da su, kuma ta kaurace masa, har ta yi wafati bata sake masa magana ba. Kuma ta rayu ne bayan wafatin babanta da watanni shida (tsawon wata shidan nan tana fushi da shi har ta koma ga Allah). Tambayar da nake yi shine mene ne hukuncinsu, duba da yadda suka cutar da tsokar Manzon Allah (S), wanda yace cutar da ita cutar da shi (S) ne, kuma Allah yace mana masu cutar da Annabi suna da azaba mai radadi. Shin mai Imani da Allah zai aminta da wanda ke da tabbacin fuskantar azabar Allah a Duniya da Lahira ya zama shine abin kallonsa a addini!? Wallahil Azeem ni ban son su. Ra’ayina a kansu shine ra’ayin Sayyida Zahra a kansu. Ina fatan ya zama har na koma ga Allah ina fushi da su nima.
Shi cutarwar da sarakunan nan sukaiwa Sayyida Zahra (S) ba wani abu ne da yake boyayye ko kuma abin da ba a tsammace shi ba. Wato ina cewa ne dama su Sayyida Zahra da mijinta da ‘ya’yanta sun san cewa za a cutar da su bayan wafatin Manzon Allah (S) kamar yadda shi Annabi (S) din ya sanar da su tun kafin ya rabu da su, har kuma ya yi musu wasicci da hakuri. Don haka dama sun san za a cutar da su, kuma sun san ko su waye za su cutar da su din. Ba kowa bane face wadannan da suka cutar da Manzon Allah (S).
Wadanda suka tsaya a gaban Annabi (S) yace su aikata suka ki aikatawa, yace kar su aikata wani abin suka aikata, suka saba masa, karshe ma suka dura masa guba suka yi sanadin Shahadarsa, yaushe kake tsammanin za su saurarawa iyalan gidansa a bayansa!? Sai aka wayi gari ba kawai Fadak suka kwacewa Sayyida Zahra (S) ba, sun kwace mulki da shugabancin zahiri na Amirulmuminin (AS) duk kuwa da sun dauki alkawarin za su bi shi a bayan Manzon Allah (S) tun a Ghadeer.
A cikin wasiyar da Manzon Allah (S) ya ma Shugaba Ali (AS), kamar yadda aka ruwaito a cikin ‘Kitabu Sulaim Bin Kais, Jildi 2, shafi 917 (Wanda al-Ansari ya yi tahkikinsa). Manzon Allah (S) ya fada ma Imam Ali (AS) cewa: “Lallai Kuraishawa za su dira a kanku, za su yi muku taron dangi su zalunceku kuma su yi maka fin karfi” (Ma’ana, za su hadu su kwace hakkokinku, su yi maka fin karfi akan mulkinka na halifancinsu na zahiri da barka a kai).
Annabi (S) yace: “ (a wannan lokacin) Idan har ka samu mataimaka, to ka yake su (Su Quraishun da za su kwace hakkin naka). Idan kuwa ba ka samu mataimaka ba to ka rike hannayenka daga gare su, ka kiyaye jininka (a wannan lokacin), amma lallai shahada na jiranka, Allah ya la’anci makashinka.”
Allah Sarki Imam Ali (AS). Sai kuwa bayan wafatin Manzon Allah (S) ya kasance abin da Manzo ya fada masa ya auku din, ta yadda suka je suka hadu a Sakifar Banu Sa’ida suka nada Halifa daban ba shi ba, suka kuma dawo suka ce tilas Ali ya yi bai’a ga wannan halifan kwacen. Har kuma suka masa barazanar za su kashe shi idan har ya ja da su. Wanda hakan ya jefa Imam a cikin matsanancin yanayi, ta yadda ya tilasta ma kansa killacewa na tsawon lokaci. Kasancewar Manzon Allah ya bashi wasiccin cewa, idan ya samu mataimaka, to ya yaki wadannan masu masa kwacen mulkin ya karbi mulkinsa. Idan kuwa bai samu ba, to ya kame hannayensa daga yakin, sannan kuma ya tsare jininsa.
Hakan tasa Imam Amirulmuminin (AS) ya nemi taimakon mutane, daga Muhajirun da Ansar a kan su zo su fada masa don ya ga yadda abin za ta kasa. Tare da cewa Sayyida Zahara (S) ta kasance tana mai taya shi wannan neman, an ruwaito cewa suna fita ita da shi da daddare su je majalisun Sahabbai daidaikunsu da sukan zauna su yi hira da daddare, sai Sayyida Zahara ta musu jawabi, tana mai tuna musu abin da Manzon Allah (S) ya yi a Ghadir Khum a gabansu, ta kuma tambaye su akan me yasa suka sauya da yi ma wanda ba shi Annabi ya halifantar ba mubayi’a? Sai su ce mata, ya ‘Yar Manzon Allah. Hakika duk abin da kika fadi gaskiya ne, amma kuma wannan mutumin ya riga dan Amminki (wato Imam Ali) fuskantomu da al’amarin mubayi’a.
Dan haka sai ya zama Imam Ali (AS) ya rasa mataimaka kwarara. An ce da kyar da wannan zagayen ya iya samun mutum 40 da suka biyo shi zuwa kofar gidansa a kan sun amsa masa kiran neman taimakonsa. To, kun san Manzon Allah (S) yace idan ya samu mataimaka ya kwaci hakkinsa, kuma adadin mataimakan nan daga 40 ne zuwa sama kawai, kamar yadda Sulaim bin Qais ya kawo cewa, Imam Ali (AS) yace: “Da ace na samu mutum 40 nagartattu kuma masu min biyayya ta gaskiya da suka goya min baya, wadanda sukai tawaye ga mai kwacen, da na kaddamar da jihadi akansu.”
Kana iya cewa ai Imam (AS) ya samu mutum 40 din yanzu. Eh, ya samu mutum 40 a ranar, amma sai yace da su yanzu duk su tafi, gobe da safe kowa ya zo cikin shiri. Wayewan gari, sai ba wanda ya zo sai kasa da mutum 5 a cikin mutum 40 din nan. Wanda ya nuna lallai dama ba a shirye suke da goya masa baya da yi masa biyayya ba.
Ta wata fuska kuma Imam ya samu mutane fiye da hakan, amma tunda ba a nagartar da yake bukata bane sai ya kore samuwar. An ce Abusufyan ya zo ma da Imam Ali (S) wata magana, inda yake ce masa: “Ya kai dan Ammin Muhammad! (Yana nufin Imam Ali (AS), ina kake? Ina Abbas!? Kuka bar wannan abin (Mulkin Muhammad) a hannun kaskantattun kabilun ‘Taim’ da ‘Addiy’? Me ya faru ne? In ka shirya ka zo zan baka mayaka mutum dubu ka yake su ka kwace hakkinka.”
Sai Imam Ali (AS) ya yi dariya, sannan yace masa, Abu Sufyan na san waye kai. Na kuma san abin da ka ke nufi. Ni ina neman ‘Mulklisai’ ne masu takawa. Kai kuwa na san me ke zuciyarka a kan wannan addinin. Don haka sai Imam (AS) ya kore tayin Abu Sufyan, domin ya fahimci shi Abu Sufyan na da burin ya yi amfani da shi ne kawai ya zama al’ummar Musulmi sun fara yake-yake har a wayi gari addinin ya rushe, tunda abin da yake da buri kenan a tsawon rayuwarsa yasa ya yi ta yakar Manzon Allah (S) a Makkah da Madina.
To mutum na iya cewa, Ah! Shi Imam Ali (AS) shi kadai ba zai iya yakarsu bane, bayan ba wanda ya ke iya yin galaba a kansa a wajen yaki? Sai muce, Manzon Allah ne ya san hikimar cewa sai ya samu mutanen da suka kai 40 da za su dafa masa. Kila mu iya cewa babu mamaki hakan na nufin saboda in abin ya karbi mulkin ne bayan ya yake su, to su waye kuma Mulkisan da za su taimaka masa wajen gudanarwa? Idan ya zama masu gudanarwar lalatattu ne masu cuta a zukatansu kun ga ai ba kanta ko?
Cikin wasiyyoyin, Manzon Allah (S) ya cigaba da fada ma Amirulmuminin (AS) dangane da abubuwan da zai same su a bayan wafatinsa, kamar yadda Sheikh Saduk ya kawo a Amalinsa, da Fara’idus Simdain na Alhamiyuni cewa: “Amma ita ‘Ya ta Fatima, wacce ta kasance itace shugaban matan talikai, a yayin da na kalle ta sai na tuna da abubuwan da za su faru da ita bayan bani nan.”
Manzon Allah (S) yaci gaba da cewa: “Kamar ina ganinta a yayin da kaskantacce zai kusa dakinta, ya keta alfarmarta, a kwace mata hakkinta, a kuma hanata gadonta, a kassara mata tayin da ke cikinta, a barar da cikinta. A wannan halin za ta kasance tana kira tana cewa; ‘Ya Muhammadaa!’ Amma ba za ta ji amsa ba. Za ta nemi dauki, amma ba za ta samu mai taimako ba. Za ta wanzu a bayana tana cikin bakin ciki da damuwa, kuma tana mai yawan kuka. Za ta kasance kamar kaskantacciya (a wajen masu cutar da ita) bayan kuwa a lokacin rayuwar mahaifinta ta kasance mai daukaka.”
Manzon Allah (S) ya ci gaba da cewa: “Za ta kasance farkon wanda za ta sadu da ni a cikin Ahlulbaiti na bayan na tafi. Za ta riske ni a cikin damuwarta kuma tana raunatacciya wacce aka bakantawa rai, wacce akawa kwacen hakkinta, kuma wacce aka kashe ta. Allah ka la’anci wanda ya zalunceta, kuma ka yi wa wanda ya fusata ta azaba, ka kaskantar da wanda ya kaskantata, kuma ka dauwamar da wanda ya barar da tayin cikinta a wutarKa.”
A ruwayar aka ce, a daidai wannan lokacin sai Mala’iku suka amsa addu’ar Manzon Allah (S) da ‘Ameen’. Ba mu gushe ba muma muna cewa Allah ka la’ance su da duk wanda ya goyi bayansu bisa sani.
Insha Allah za mu cigaba.
Allah yasaka da alkairi
ReplyDelete